A+ R A-
17 October 2021

Gabatarwar Mai Shafi

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Ubangijin talikai gaba ɗaya, Wanda Ya halicce mu daga laka kana Ya tsara mu cikakken tsari kana kuma Ya fifita mu sama da dukkan halittu, sannan kuma Ya arzurta mu da hankali don mu yi amfani da shi wajen banbance gaskiya da ƙarya, sannan kuma don ɗaɗa shiryar da mu Ya aiko mana Annabawa da Manzanni don su nuna mana hanya madaidaiciya da kuma kare mu daga sharrin Shaiɗan la'ananne, kamar yadda kuma suka shiryar da mu kan cewa mu bauta wa Allah Shi kaɗai da kuma riƙo da madaidaicin tafarki ta hanyar fahimta da kuma yarda, da kuma nesantar da mu da zama " 'yan amshin shatan" iyaye da kakanni waɗanda suka ka riƙi wani tafarki ba tare da wata cikakkiyar hujja ba. Sannan tsira da amincinSa su tabbata ga Annabin rahama, cikamakin annabawa kana kuma Shugaban Manzanni, wanda ya zo mana da shiriya da kuma rahama, mataimakin waɗanda aka zalunta da kuma raunana, Shugabanmu Annabi Muhammadu ɗan Abdullahi (s) tare da tsarkakan Mutanen gidansa, waɗanda Allah Ta'ala Ya zaɓe su su zama taurari masu shiryarwa da kuma haskaka hanya ga dukkan muminai kana kuma Ya wajabta soyayya da kuma ƙaunarsu ga dukkan muminai, da zaɓaɓɓun sahabbansa waɗanda suka kasance tare da shi kana kuma suka taimaka masa tun daga farko har ƙarshe ba tare da sun juya da baya ba, da kuma dukkan mabiyansu waɗanda suke farin ciki da farin cikinsu kana kuma suke baƙin ciki da baƙin cikinsu, suke abokantaka da abokansu kana kuma suke gaba da maƙiyansu.

Bayan haka...., haƙiƙa haƙƙin Manzon Allah akan mabiyansa haƙƙi ne mai girman gaske, koda yake saninsa da kuma kula da shi yana bambanta tsakanin mutane. Lalle babu shakka kan cewa sonsa shi ne a kan gaban waɗannan haƙƙoƙi, don kuwa shi ne matakin farko na riƙo da abubuwan da ya bari, koyi da sunnansa, raya al'amurransa da kuma haƙiƙanin binsa. Domin kuwa matuƙar ba'a samu ƙauna ta haƙiƙa ba, to babu yadda bi da kuma sadaukarwa za su tabbata. A don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke cewa:"Ɗayanku ba ya kasancewa mumini har sai na kasance abin soyuwa gare shi sama da kansa, mahaifinsa, ɗansa da kuma dukkan mutane".

Haƙiƙa sonsa (s.a.w.a.) reshe ne na son Ubangiji, Maɗaukakin Sarki, kuma dukkansu biyun sun kasance matakan farko ne na imani. Bugu da kari kuma wannan so nasa (s.a.w.a.) yana wajabta so da ƙauna ga makusantansa masu riko da amanarsa da kuma isar da sakonsa, don kuwa da haka ne wannan silsilar ƙaunar ta kan cika, a duk lokacin da aka rasa ta kuwa, to babu wata ma'ana ga son Allah da kuma son ManzonSa, don haka aka ruwaito shi (s.a.w.a.) yana cewa:"Ku so Allah saboda abin da ya ciyar da ku na daga ni'imominSa, ku so ni saboda son Allah, kana kuma ku so Ahlubaitina saboda so na".

A saboda haka ne wannan nau'i na ƙauna ga Allah, ga ManzonSa da kuma mutanen gidan AnnabinSa ya kasance wani al'amari mai girman gaske cikin rayuwar ɗaiɗaiku da kuma ta jama'ance, kuma ya kasance wani mabuɗi ga alaƙar ɗaiɗaiku da kuma al'ummance da koyarwar Ubangiji, kamar yadda Allah da ManzonSa suka shiryar da mu kuma suka umurce mu da hakan, don kuwa su ne taskokin ilminSa, masu kiyaye amanoninSa, mafifita akan sauran al'umma ta ko ta wani dangare.

To don haka ne na tsara wannan shafi don amfanin dukkan al'umma gaba ɗaya, musamman ma masu magana da harshen Hausa, don sanin wani abu daga cikin koyarwar Ahlulbaitin Manzon Allah (a.s), wadanda su ne "Jirgin Annabi Nuhu" wanda ya rike su ya tsira wanda kuwa ya yi watsi da su ya halaka.

Koda yake dai abin da muka rubuta a ciki bai kai ko cikin cokali na koyarwa Ahlulbaiti (a.s.) ba, to amma dai duk da haka, watakila masu neman sani iri na za su iya amfana da ɗan abin da ya sawwaƙa daga cikin abin dake cikin shafin.

Saboda la'akari da ƙoƙari da kuma taimaka min da wasu 'yan uwa na suka yi wajen tsara wannan shafi, ta hanyar ba da shawarwari da dai makamantansu, don haka ba zan rufe wannan gabatarwa ba har sai na gode musu da kuma roƙon Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala da Ya saka musu da alherinSa.

Daga karshe, ina rokon duk wanda ya bude wannan shafi don dubawa, da yayi salatin Annabi ga iyayena da Allah Yayi musu rasuwa da niyyar ladar ta je gare su.

 

TUNASARWA

Duk wani wanda yake da wata tambaya (dangane da abin da muka rubuta), ko kuma neman karin bayani, ko kuma shawara da dai sauransu, yana iya rubuto min ta adireshi na na email da ke can kasan shafin farko da sauran hanyoyin tuntubar mu ta nan Game Da Mu

 

Mai karatu, a sha karatu lafiya.

Muhammad Awwal Bauchi