A+ R A-
18 September 2020

Siffofin Aboki Na Imani Kuma Na Kwarai

Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Imam Ja'afar al-Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij' da ya gabatar a ranar 11, Janairu 2011 (5, Safar 1432):


"قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ (ع) اخْتَبِرُوا إِخْوَانَكُمْ بِخَصْلَتَيْنِ فَإِنْ كَانَتَا فِيهِمْ وَ إِلَّا فَاعْزُبْ ثُمَّ اعْزُبْ ثُمَّ اعْزُبْ مُحَافَظَةٍ عَلَى الصَّلَوَاتِ فِی مَوَاقِيتِهَا وَ الْبِرِّ بِالْإِخْوَانِ فِی الْعُسْرِ وَ الْيُسْر"


شافی، صفحه‌ى 652


"Abu Abdillah, Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Ku gwada 'yan'uwanku da siffofi biyu, idan har sun kasance tare da su, (shi kenan) idan kuwa ba haka ba, ku nesance su, ku nesance su sannan ku nesance su, (su ne kuwa): kiyaye salla a kan lokacinta da kuma kasantuwa tare da 'yan'uwa cikin tsanani ne ko kuma cikin jin dadi".

(Al-Shafi, shafi na 652)


Ya zo cikin Al-Kafi, daga wajen Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Ku jarraba 'yan'uwanku da siffofi biyu". A nan 'yan'uwan da aka ce ba wai kawai ana nufi wadanda kuke tare da kuma rayuwa tare da su ba ne. Hatta mutanen da ku ke son ku dauka a matsayin 'yan'uwanku da abokanku, na kurkusa da ku, to wajibi ne su zamanto suna da wadannan siffofi guda biyu. "Idan har suna da wadannan siffofi guda biyu", wato idan har suna da wadannan siffofi guda biyu to lamarin ya fi kyau. "Idan kuwa ba haka ba, to a nesance su, kuma a nesance su, kuma a nesance su". Kamar yadda ya zo ne cikin Alkur'ani "Gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare Shi" (Suratus Saba 34:3). Ku nesance su.

Mene ne wadannan siffofi guda biyun:

(1): "Kiyaye salla a kan lokacinta". Siffar farko ita ce su kasance masu kiyaye salla a kan lokacinta. Ko shakka babu ana nufin lokacinta na fadhila ne. In kuwa ba haka ba, idan har aka ce sakakken lokacinta kawai, to har karshen lokacinta ma ai lokaci ne. Idan har mutum bai yi haka ba (wato bai yi salla ba har sai da lokacinta ya fita), a wannan lokacin kan ya zamanto fasiki. Yana so ne ya ce masu salla cikin lokacinta na fadhila. Marigayi Ayatullah Bahjat (yardar Allah ta tabbata a gare shi) wanda a lokuta da dama mun sha jin wannan lamari daga bakinsa. Ni kai na na sha ji sannan kuma wadansu ma sun nakalto min - ya kan ce malaminsu - daga dukkan alamu yana nufin marigayi Aghaye Qadhi ne a matsayin misali - ya gaya masa cewa idan har mutum ya kiyaye salla cikin lokacinta, to lalle zan zamanto lamuni wajen ceto shi ko kuma a matsayin lamuni dangane da samun madaukakin matsayi; wata magana dai makamanciyar hakan. Ni din nan a wani lokaci na taba tambayarsa cewa wajibi ne sallar ta zamanto da kyau kan ko? sai ya ce: Na'am, e haka ne, salla wacce ta dace tare kuma da kula da Ubangiji, sannan kuma a farkon lokacinta. Idan har mutum ya kiyaye hakan, to hakan wani lamari ne da ke daukaka mutum da kuma kai shi zuwa ga matsayi na koli na tauhidi. Wannan ita ce siffa ta farko.

(2): "Kasantuwa tare da 'yan'uwa cikin tsanani ne ko kuma cikin jin dadi ". Siffa ta biyu wata siffa ce ta zamantakewa. Siffa ta farko siffa ce ta daidaiku, tsakanin mutum ne da Ubangijinsa; amma wannan ta biyun tsakaninsa ne da sauran mutane. Mutumin da siffarsa za ta kasance mai taimakon 'yan'uwansa, shin cikin tsanani ne ko kuma cikin yalwa. To wannan tsanani da kuma yalwa (dai tana iya daukan yanayi biyu), shin shi kansa wanda za a taimaka masa din ne ya ke cikin tsanani da yalwan. A matsayin misali yana cikin talauci, ba shi da kudi, to zai taimaka masa. Wato ya saukaka masa, ya taimaka masa da harshensa, ya taimaka masa ta hanyar kare mutumcinsa. Sannan kuma mai yiyuwa ne abin nufi da tsanani da yalwa din shi ne na mai taimakawan ne, wato shin shi ma mai taimakon yana cikin yalwa ne ko kuma kumci.

Don kuwa akwai wadansu mutane da suke a shirye su taimaka wa mutum, a lokacin da yake cikin yanayi mai kyau; a lokacin da idanuwa suka koma kan mutum, a shirye suke su taimaka masa. Amma daga lokacin da dukkanin idanuwa suka janye daga gare shi, to su ma sai su juya masa baya. Wadansu daga lokacin da duniya ta juya wa mutum baya su ma sai su juya masa bayan.

A'a, ba haka lamarin ya kamata ya kasance ba. Cikin kowane irin hali da yanayi a taimaka wa mutum.