A+ R A-
18 September 2020

Rabon Kwado Ba Ya Hawa Sama

Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi da Alayensa) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij'

 Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:-

الدنيا دُوَل فما كان لك أتاك على ضعفك وما كـان منها عليك لم تدفعه بقوّتك ومن انقطع رجاؤه مما فات استراح بدنه ومن رضي بما قََََسَمه الله قرّت عينه

 

"Duniya wata aba ce mai jujjuyawa, don haka abin da ya kasance naka ne zai same ka komai rauninka kuwa. Abin da kuma ya kasance daga gare ta a kanka ba za ka iya kare kanka daga gare shi da karfinka ba. Wanda kuma ya fitar da ransa daga kan abin da ya kubuce masa, ya hutar da jikinsa (ya huta), wanda kuma ya amince da rabon da Allah Ya ba shi, yana cikin farin ciki da kwanciyar hankali".

(Tuhaful-Ukul shafi na 40).

*****

A wannan hadisi za mu fahimci cewa ababan kawa na duniya abubuwa ne da suke sassauyawa, ba dole ba ne mu zaci abubuwa irin su dukiya, matsayi, sukuni, lafiya da kwanciyar hankali da muke da su, za su ci gaba da kasancewa tare damu har karshen rayuwarmu. Koda wasa, akwai yiyuwar a kwace su daga gare mu.

Duniyar da ake nufin cewa idan mutum ya kaurace mata ya hutar da kansa ita ce duniya abar zargi. Wato wacce mutum yake nemanta ruwa a jallo don biyan soyace-soyacen ransa, ba wai madaukakan abubuwa da za su kai mutum zuwa ga alherorin lahira da sauran abubuwan rufin asiri na rayuwa ba ne.

(Sharhin Hadisi Na Imam Khamenei)