A+ R A-
13 July 2020

Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Shahid Abu Mahdi al-Muhandis

An haifi Jamal Jafaar Mohammed Ali Āl Ebrahim wanda aka fi sani da alkunyarsa ta Abu Mahdi al-Muhandis a ranar 1 ga watan Yulin 1954 a gundumar Abu Al-Khaseeb na lardin Basra na ƙasar Iraƙi. Mahaifinsa dai ɗan asalin ƙasar Iraƙi ne, ita kuwa mahaifiyarsa an ce asalinta Ba’iraniya ce ‘yar ƙasar Iran.

A nan ne yayi karatunsa na firamare da kuma na sakandare har zuwa jami’a inda ya gama karatunsa a fannin injiniya a shekarar 1977, inda a dai wannan shekarar ce ya shiga harkokin siyasa inda ya shiga ƙungiyar Dawa Party wacce take adawa da gwamnatin kama-karya ta Saddam Husain ta ƙasar Iraƙin. A shekarar 1979 ne ya gudu daga ƙasar Iraƙin zuwa ƙasar Iran bayan da gwamnatin Saddam ɗin ta haramta ayyukan jam’iyyar Dawa Party ɗin a duk faɗin ƙasar. An ce ya zauna ne a garin Ahwaz tare da sauran Iraƙawa ‘yan gwagwarmaya da suke cikin Iran inda suka ƙulla wani haɗin gwiwa tare da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran wajen samun horo da kuma ƙwarewa na soji don faɗa da gwamnatin kama-karya ta Saddam ɗin. Ya ci gaba da rayuwa a ƙasar Iran har zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatin Saddam da kuma mamaye Iraƙin da Amurkawa suka yi.

Bayan komawarsa ƙasar Iraƙin a shekara ta 2003, Abu Mahdi al-Muhandis ya zama babban mai ba wa firayi ministan ƙasar Iraƙi na lokacin Ibrahim Ja’afar shawara kan harkokin tsaro. Sannan a shekara ta 2005 kuma an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Babil ƙarƙashin jam’iyyar Dawa Party ɗin.

A shekara ta 2011 bayan janyewar sojojin mamayar Amurka daga ƙasar Iraƙi, da kuma kafa dakarun sa kai na Kata’ib Hezbollah a ƙasar da nufin ba da kariya da kuma faɗa da ƙungiyoyin ta’addanci da suka shigo ƙasar, Abu Mahdi al-Muhandis ya zamanto shugaban waɗannan dakarun sakamakon ƙwarewar aikin soji da yake ita, kana daga baya kuma bayan kafa dakarun sa kai na gaba ɗaya na ƙasar da ake kira da Al-Hashd al-Sha’abi (Popular Mobilization Forces) sakamakon mamaye wasu yankuna da jihohi na ƙasar Iraƙin da ‘yan ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh suka yi da kuma kiran da malaman addini suka yi na wajibcin kafa wannan dakaru, Abu Mahdi Muhandis ya zamanto mataimakin babban kwamandan waɗannan dakarun matsayin da ya ci gaba da riƙewa har lokacin da yayi shahada.

Ko shakka babu Abu Mahdi al-Muhandis ya taka gagarumar rawa wajen kawo ƙarshen kungiyar Daesh da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da suke samun goyon bayan wasu ƙasashen yankin a Iraƙi har ma da Siriya lamarin da ya sanya waɗannan ƙasashe musamman Amurka sanya masa ƙahon zuƙa da ƙoƙarin ɓata masa suna ta hanyar zarginsa da wasu ayyuka da suka siffanta su da ayyukan ta’addanci da kuma neman kashe shi.

Daga ƙarshen dai a ranar 3 ga watan Janairun wannan shekara ta 2020 ne, Allah Ya arzurta shi da yin shahada bayan harin da Amurka ta kai masa a kusa da filin jirgin sama Baghdaza tare da babban kwamandan rundunar Quds ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran Shahid Ƙasim Sulaimani inda suka yi shahada tare da wasu da suke tare da su.