A+ R A-
01 July 2022

Yadda Ake Sallar Idi A Mazhabar Ahlulbaiti, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Su

Karamar salla dai ita ce sallar da ake yi bayan an kawo karshen azumin watan Ramalana, wato bayan an ga watan Shawwal kenan. Ruwayoyi daban-daban sun bayyana cewa akwai wasu ayyuka da addu'o'i da ake yi a wannan rana da kuma daren ta (daren karamar sallar) kamar haka:

1.    An so a karanta addu'an Imam Sajjad (a.s) da ke cikin Sahifat al-Sajjadiyya yayin ganin wata. Mai son karin bayani sai ya koma ga wannan littafi.

2.    An so a raya wannan dare da ibadu, zikiri da kuma addu'o'i. An ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa "Duk wanda ya raya daren idi, to zuciyarsa ba za ta mutu ba a ranar da zukata suke mutuwa".

3.    An so a yi wanka sau biyu a wannan dare, na farko bayan faduwar rana na biyun kuwa karshen daren.

4.    An so kuma a karanta ziyarar Imam Husaini (a.s). Ana iya komawa ga littattafan addu'o'i don ganin wannan addu'a (ziyara).

5.    An so yin takbiri kafin wadannan salloli guda hudu, wato Magriba da Lisha na daren sallan da kuma sallar Asuba da kuma Idi na ranar sallar. An ruwaito Imam Sadiq (a.s) yayin da yake fassara wannan aya "...Kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku..." (Surar Bakara; 2:185), ya ce: Sai ku ce:

6.     

"Allaahu Akbar, Allaahu Akbar, Laa ilaaha illallaah wallaahu Akbar. Allaahu Akbar, Wa lillaahil hamd. Alhamdulillah alaa maa hadaanaa walahu Shukr alaa maa aulana."

 

Har ila yau a ranar sallar an so mutum ya yi wanka da kuma ado da sabbin kaya ko kuma wasu kayansa wankakku gwargwadon iko. Haka nan kuma ya karanta wasu addu'o'i da aka ruwaito da A'imma (a.s). Haka nan kuma dai an so mutum ya ci wani abu kafin tafiya sallar idi.

Kamar yadda kuma aka so ya fitar da zakkar fidda kai (Zakatul Fitr) kafin ya tafi zuwa ga sallar idi.

Ita dai wannan zakka ana fitar da ita ne daga kayayyakin abincin da mutanen suka saba ma'amala da su, hakan kuwa ya dogara ne da wurin da mutum ya ke zaune. Kamar dai a kasashenmu na Hausa mun fi ma'amala da dawa, gero, masara, shinkafa da dai sauransu, to an so mutum ya fitar da zakkar daga wadannan abubuwa. Kuma ga kowani mutum akan fitar da kilo uku ne na kayan abincin da za a fitar da shi din, a ba wa mabukaci. Kuma hakkin mutum ne ya fitar wa iyalansa da duk dai wadanda suke karkashinsa wannan zakka. Mai son karin bayani dai yana iya komawa da littattafan fikhu.

Bayan duk wannan kuma sai a tafi sallar idi, wacce ita ma tana da nata lada na musamman da kuma kara daukaka ga wanda ya je ta.

 

Yadda Ake Sallar Idi

 

Sallar idi dai wajaba ce matukar dai sharuddan wajibcinta sun cika, kuma lokacinta shi ne daga fitowar rana har zuwa lokacin sallar azahar na ranar sallar.

Ga yadda ake yin sallar:

1.    Sallar idi dai tana da ra'aka biyu ne kamar sallar asuba.

2.    A raka'a ta farko, akan karanta fatiha da sura, sai kuma ayi kabbara sau 5, bayan kowace kabbaran kuma ana yi Kunut (daga hannun don addu'a). Mutum yana iya kowace addu'a yayin wannan kunutin, sai dai kuma an fi so a yi addu'o'in da aka ruwaito su daga A'imma (a.s). To bayan kabbara ta biyar da kuma kunuti, sai ya tafi zuwa ga ruku'i, bayan haka sai ya dago, sai ya tafi zuwa ga sujada, kamar dai yadda yake yi a sauran salloli.

3.    To daga nan kuma sai ya zo da raka'a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, sai dai kuma a raka'a ta biyun kabbarori hudu ba biyar ba kamar yadda ya yi a ta farko. Bayan duk ya gama hakan kuma sai ya yi ruku'u da sujada, kana ya yi tahiyya ya sallame.

To a takaice wannan shi ne yadda ake yin sallar idi. Karin bayani kuma kan hukumce-hukumcenta da dai sauran abubuwan da suka shafe ta suna nan a cikin littattafan fikhu, sai a koma gare su don karin bayani.