
Jawabin Jagora Ga Mahalarta “Taron Kasa Da Kasa Kan ‘Yan Takfiriyya
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Jawabai
- Hits: 3527

Shimfida: Abin da ke biye fassarar jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ga mahalarta “Taron Kasa Da Kasa Kan Kungiyoyin Takfiriyya A Mahangar Malaman Musulunci” da aka gudanar a birnin Kum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranakun 23 da 24 ga watan Nuwambar 2014.
-----------------------------------
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu al-Mustafa al-Amin Muhammad tare da Alayensa tsarkaka Ma’asumai da sahabbansa zababbu da wadanda suka biyo su cikin kyautatawa har zuwa ranar Lahira.
Da farko ina wa baki masu girma, mahalarta wannan taro masu girma, malaman mazhabobi daban-daban na Musulunci wadanda suka halarci wannan taro, barka da zuwa. Haka nan kuma ina mika godiya ta dangane da yadda kuka halarci wannan taron da kuma irin gudummawa mai amfani da kuka bayar yayin wannan taro na kwanaki biyu. Haka nan kuma wajibi ne in mika godiya ta ga manyan malaman Kum, musamman mai girma Ayatullah Makarim Shirazi da mai girma Ayatullah Subhani wadanda suka kirkiro wannan tunani da kuma aiwatar da shi a aikace. Alhamdu lillahi sun share fagen wannan aikin; wajibi ne a ci gaba da hakan. A takaice ina da masaniya kan jawabai daban daban da aka yi a wadannan ranaku biyu; to ni ma zan dan fadi wasu abubuwa:
Da farko wannan taro ne na tattaunawa kan kungiyar Takfiriyya (masu kafirta musulmi) wadda wata kungiya ce mai cutarwa da kuma hatsarin gaske ga duniyar musulmi. Duk kuwa da cewa wannan kungiya ta takfiriyya ba wata sabuwar kungiya ba ce, tana da tsawon tarihi, to sai dai cikin ‘yan shekarun baya-bayan ne ta sake kunno kai sakamakon makirce-makircen ma’abota girman kai ko kuma bisa taimakon kudaden wasu gwamnatocin yankin nan ko kuma bisa tsare-tsare da kulle-kullen kungiyoyin leken asirin kasashen ‘yan mulkin mallaka – irin su Amurka da Ingila da gwamnatin Sahyoniyawa – sannan kuma ta sami karfi. Wannan taro da kuma wannan yunkuri na ku na tinkara da kuma fada da wannan yunkuri na takfiriyya ne; ba wai kawai da wannan kungiya da a yau ake kira da kungiyar Da’esh (ISIS) ba. Kungiyar da a yau ake kiranta da Da’esh (ISIS), wani reshe ne na wannan lalatacciyar bishiya ta ‘yan takfiriyya. Amma ba ita ce dukkanin lamarin ba. Fasadi da lalatar da wadannan mutane suke aikatawa, wannan halaka shuka da ‘ya’yan dabbobi (kamar yadda ya zo cikin aya ta 205 na Suratul Bakara), wannan zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba, wani bangare ne na danyen aikin wannan kungiya ta takfiriyya a duniyar musulmi. Da irin wannan mahangar ya kamata a kalli wannan lamarin.
Ina bakin ciki ainun, yadda a duniyar musulmi – maimakon mu yi amfani da dukkanin karfinmu wajen fada da makirce-makircen gwamnatin sahyoniyawa da irin wannan abin da take yi wa birnin Kudus da Masallacin Al-Aksa – amma sai ya zamana a yau an tilasta mana shagaltuwa da matsalolin da ma’abota girman kai suka haifar wa duniyar musulmi; babu kuma yadda za mu yi. A hakikanin gaskiya, magana da kuma kokarin magance matsalar ‘yan takfiriyya, wani lamari ne da aka dora wa malaman duniyar musulmi da masananta. Makiya sun tilasta wa duniyar musulmi matsalolin da ya zama wajibi su yi fada da su. To amma batu na asali, shi ne fada da gwamnatin sahyoniyawa; batu na asali shi ne batun Kudus; batu na asali shi ne batun Alkiblar musulmi ta farko, wato Masallacin Al-Aksa. Wannan su ne batutuwa na asali na duniyar musulmi.
Akwai wani lamari wanda ba za a iya inkarinsa ba, shi ne kuwa cewa kungiyoyin tafkiriyya da gwamnatocin da suke goyon bayansu, suna gudanar da ayyukansu ne wajen biyan bukatu da manufofin ma’abota girman kai da kuma sahyoniyawa. Ayyukansu suna lamunce wa Amurka da gwamnatocin mulkin mallaka na kasashen Turai da gwamnatin ‘yan mamaya ta sahyoniyawa ‘yan mamaya, manufofinsu ne. Akwai shaidu da alamu da suke tabbatar da hakan. Kungiyoyin takfiriyya suna jingina kansu ga Musulunci amma a aikace suna hidima ne ga ‘yan mulkin mallaka da ma’abota girman kai masu cutar da duniyar musulmi. Akwai shaidu da suke a fili, wadanda ba za a iya rufe ido kansu ba. A nan zan ambato wasu daga cikin wadannan shaidun:
Na farko shi ne cewa ‘yan takfiriyya sun sami nasarar jirkita yunkurin farkawa ta Musulunci daga ingantaccen tafarkin da yake tafiya a kai. Shi dai wannan yunkuri na farkawa ta Musulunci, wani yunkuri ne na kyama da adawa da Amurka, da mulkin kama-karya da ‘yan amshin shatan Amurka a wannan yankin. Wani yunkuri ne da al’ummomin kasashen arewacin Afirka suka faro shi ne don fada da girman kai da kuma Amurka. To amma ‘yan takfiriyyan sun sauya wa wannan gagarumin yunkuri na fada da ma’abota girman kan da kuma Amurka da ‘yan mulkin kama-karya mahanga, da mai she shi wani yakin basasa tsakanin musulmi da zubar da jinin juna. Isra’ila ita ce babbar abokiyar fada da yakin wannan. To amma ‘yan takfiriya sun mayar da titunan Bagadaza da babban masallacin Siriya da Damaskus da titunan Pakistan da garuruwa daban-daban na Siriya sun zamanto su ne fagen dagan.
Ku dubi halin da kasar Libiya take ciki a halin yanzu; ku dubi yanayin kasar Siriya, kasar Iraki da kasar Pakistan, ku ga da wa musulmi suke fada? Kamata ya yi a ce sun yi amfani da wannan karfi na su wajen fada da haramtacciyar kasar Isra’ila, to amma ‘yan Takfiriyya sun sauya mahangar wannan gwagwarmayar da shigo da shi cikin gida, cikin kan tituna da garuruwanmu. Suna tayar da bam a cikin babban masallacin Damaskus, su kan tayar da bama-bamai a tarurrukan mutanen da ba su ci ba su sha ba a birnin Bagadaza, su na kashe daruruwan mutane a Pakistan, kamar yadda ku ke ganin abin da ke faruwa a kasar Libiya. Dukkanin wadannan abubuwa suna daga cikin ayyukan ta’addancin wadannan kungiyoyi da ba za a taba mancewa da su ba tsawon tarihi. Sauya tafarki da mahangar wannan yunkuri (da ‘yan takfiriyyan suka yi) wani aiki ne da zai amfani Amurka da Ingila da kungiyoyin leke asirin Amurka da Ingila da MOSSAD da makamantansu.
Wata alama da kuma shaida ta daban ita ce cewa wadanda suke goyon bayan kungiyoyin takfiriyyar, suna hada baki da gwamnatin sahyoniyawa wajen yakar musulmi. Ba sa daga tsinke kan haramtacciya kasar Isra’ila, amma suna cutar da al’ummar musulmi da kulla musu makirce-makirce ta hanyar fakewa da batutuwa daban-daban.
Wata shaidar kuma ta daban ita ce cewa wannan fitinar da kungiyoyin takfiriyya suka haifar a kasashen musulmi – a Iraki da Siriya da Libiya da Labanon da sauran kasashe na daban – ta yi sanadiyyar rusa tushen wadannan kasashen. Ku dubi irin kudade da karfi da kayan aikin da lokacin da ake bukata wajen sake gina hanyoyi, matatun mai, ma’adinai, filayen jiragen sama, garuruwa da gidajen da aka rusa su sakamakon wadannan yakukuwa na basasa, sakamakon irin wadannan zubar da jini da aka yi. Wadannan suna daga cikin cutarwar ‘yan kungiyar takfiriyya ga duniyar musulmi cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan.
Wata shaidar ta daban ita ce cewa ‘yan takfiriyya sun shafa wa Musulunci kashin kaji a idanuwan duniya. Duk duniya, ta gani a akwatinan talabijin yadda wadannan mutane suke zaunar da mutum sannan su sare kansa da takobi ba tare da sun bayyana laifin da mutumin yayi ba. “Allah ba ya hana ku, daga wadanda ba su yake ku ba saboda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci. Lalle Allah yana son masu adalci. Allah Yana hana ku kawai game da wadanda suka yake ku saboda addini kuma suka fitar da ku daga gidajenku, kuma suka taimaki juna ga fitar da ku, kar ku jibince su, kuma wanda ya jibince su, to, wadannan su ne azzalumai (Suratul Mumtahana 60:8-9), sabanin hakan suka yi. Suna kashe musulmi, da ma wadanda ba musulmi, sannan kuma su dauki hotunan hakan su watsa wa duniya, duk duniya su gani. Duk duniya sun ga yadda wani mutum da sunan Musulunci, ya farke kirjin wani mutum da aka kashe, ya yanke zuciyarsa da gatsa ta. Kowa ya ga wannan a duniya. Suna aikata hakan ne da sunan Musulunci. Musuluncin da aka san shi da rahama, Musuluncin da ke kira zuwa ga aiki da hankali, Musulunci mai hikima, Musuluncin da “Allah ba ya hana ku, daga wadanda ba su yake ku ba saboda addini”, to amma sai ga shi suna gabatar da wannan Musuluncin da irin wannan (mummunan) yanayi. Shin akwai laifin da ya wuce wannan? Shin akwai fitinar da ta wuce wannan? To wannan shi ne aikin kungiyoyin takfiriyya.
Wata shaidar kuma ta daban ita ce cewa sun yi watsi da kungiyoyin gwagwarmaya. Kwanaki hamsin al’ummar Gaza suka yi suna yaki su kadai. Kwanaki hamsin suka yi suna tsayin daka. Gwamnatocin musulmi ba su taimaka musu ba, ba su ba wa Gaza kudaden man fetur din su ba; alhali wasunsu ma sun taimakawa gwamnatin sahyoniyawan ce.
Wata lalatar kuma ta daban, wata shaidar ta daban ita ce cewa ‘yan takfiriyya sun karkatar da kumaji da hamasar matasa musulmi a duk fadin duniya. A yau a duk fadin duniyar musulmi, matasa sun sami wani irin kumaji da hamasa, farkawar Musulunci ya yi musu tasiri, sun kasance cikin shirin yin hidima ga Musulunci don ya cimma manufofinsa. To amma wadannan ‘yan takfiriyyan, sun karkatar da wannan kumajin. Sun sanya matasan da suke cikin jahilci, wadanda ba su san inda aka sa a gaba ba, suka kama hanyar yanke kan musulmi da kisan gilla wa mata da maza da kananan yara. Wannan wani bangare ne na irin munanan ayyukan kungiyoyin ‘yan takfiriyya.
Ba cikin sauki za a iya rufe ido kan wadannan dalilai da shaidu ba. Dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da cewa ‘yan takfiriyya suna gudanar da ayyukansu ne wajen biyan bukatun ma’abota girman kan duniya, wajen biyan bukatun makiya Musulunci, wajen biyan bukatun Amurka da Ingila da gwamnatin sahyoniyawa. Tabbas akwai wasu shaidun na daban. An gaya min cewa jiragen daukar kaya na Amurka, suna watso wa ‘yan Da’esh na kasar Iraki, a sansanoninsu da ke Irakin, kayayyakin da suke bukata daga sama don taimaka musu. Na ce mai yiyuwa hakan kuskure ne; to amma bayan nanata hakan, kamar yadda aka gaya min har sau biyar, to shin aikata abu sau biyar zai iya zama kuskure? Sai kuma ga shi suna bayyana cewar sun hada hadakar fada da Da’esh; wanda karya ce tsagoronta. Wannan hadakar tana da wata bakar manufa da suke cimmawa da ita. Suna so ne su ci gaba da yada wannan fitinar; su hada mutane fada da junansu, su haifar da yakin basasa tsakanin musulmi. Wannan ita ce manufarsu. Koda yake tabbas ba za su yi nasara ba, lalle ya kamata ku san hakan.
A nan akwai wasu ayyuka da ya wajaba a aikata su. Ku din nan malamai masu girma, a yayin wannan taro na kwanaki biyu kun tattauna kan hanyoyin da ya kamata a bi da kuma nauyin da ke wuya. A nan bari in gabatar da wasu ayyuka guda biyu da ba za a iya rufe ido kansu ba: Na farko shi ne malaman mazhabobi daban-daban na Musulunci su yi kokarin samar da wani yunkuri na gama gari na ilimi da hikima don tumbuke tushen yunkurin takfiriyya. Wannan kuwa bai takaita da wata mazhaba ban da wata ba. Dukkanin mazhabobin Musulunci masu kishin Musulunci; wadanda suka yi imani da Musulunci da kuma kishinsa. Suna da rawar da za su taka a wannan yunkuri. Wajibi ne a kirkiro wani gagarumin yunkuri na ilimi. Wadannan mutane suna fakewa ne da batun riko da salihan magabata (Salaf al-Saleh). Don haka wajibi ne a tabbatar wa da duniya irin yadda salihan magabatan suke kyamar irin wadannan ayyuka da suke yi a ilmance sannan kuma ta hanyar nassosi na addini. Wajibi ne a ‘yanto matasa. Akwai wadansu wadanda suka tasirantu da wannan karkataccen tunani. Suna tunanin cewa aikin kwarai suke yi. Su din nan sun kasance alamar ayar nan ta Alkur’ani mai girma da take cewa: “Ka ce, “Ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka?. “Wadanda aikinsu ya bace a cikin rayuwar duniya, alhali kuwa suna zaton lalle ne su, suna kyautata (abin da suke gani) aikin kwarai?” (Suratul Kahf 18:103-104). Suna zaton suna jihadi ne saboda Allah ne. Su din nan su ne mutanen da a ranar Alkiyama za su fadi cewa: “Kuma suka ce: “Ya Ubangijinmu! Lalle mu, mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka batar da mu daga hanya! Ya Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azaba, kuma ka la’ane su, la’ana mai girma” (Suratul Ahzab 33: 67-68). Haka wadannan mutanen suke. Wanda ya kashe wani babban malamin Musulunci a masallacin Damaskus yana daga cikinsu; wanda ya ke kashe mutanen da ba su ci gaba su sha ba ta hanyar tada bam a Pakistan da Afghanistan da Bagadaza da sauran garuruwa daban-daban na Iraki da Siriya da Labanon, yana daga cikin wadannan mutanen da ranar kiyama za su ce: “Ya Ubangijinmu! Lalle mu, mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka batar da mu daga hanya! Ya Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azaba”. A wani wajen na daban Alkur’ani yana cewa: “Ga kowanensu, ninki biyu” (Suratul A’araf 7:38) wato ba su ma takaita da “Ya Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azaba” ba, a’a cewa su ke “Ga kowanensu, ninki biyu” na azaba “Husumar mutanen wuta” (Suratu S: 38:64), suna fada da junansu. Wajibi ne a ceto wadannan mutane. Wajibi ne a ceto wadannan matasa. Hakan kuwa wani nauyi ne da ke wuyan malamai. Malamai suna da alaka da masana haka nan suna da alaka da mutanen gari; don haka wajibi ne su yi kokari. A ranar tashin alkiyama Allah Madaukakin Sarki zai tambayi malamai kan me suka yi? Don haka wajibi ne su yi wani abu. Wannan shi ne aiki na farko.
Aiki na biyu wanda ya zama wajibi shi ne wayar da kan mutane dangane da hannun da ma’abota girman kai, Amurka da Ingila, suke da shi cikin hakan. Wajibi ne a wayar da kan mutane. Wajibi ne duniyar musulmi ta san rawar da siyasar Amurka take takawa cikin hakan. Rawar da kungiyoyin leken asirin Amurka da Ingila da gwamnatin sahyoniyawa suka taka wajen sake raya wannan fitina ta ‘yan takfiriyya. Wajibi ne kowa ya san hakan. Wajibi ne kowa ya san cewa suna musu aiki ne; su ne suke tsara musu abin da za su yi, su ne suke goya musu baya, su ne suke shiryar da su. Kudin (aikata hakan) kuwa yana fitowa ne daga aljihun gwamnatocin ‘yan amshin shatansu na yankin nan. Wadannan su ne suke ba su kudi. Su ne suka sanya duniyar musulmi cikin hatsari da kuma wannan matsalar. Wannan ma wani aiki ne na wajibi, wanda wajibi ne a aikata shi.
Aiki na uku wanda (shi ma) wajibi ne a aikata shi, shi ne damuwa da lamarin Palastinu. Kada ku bari a mance da lamarin Palastinu da Kudus mai girma da kuma batun masallacin Al-Aksa mai alfarma. Wannan shi ne abin da wadancan mutanen suke so. Suna so al’ummar musulmi su mance da lamarin Palastinu. A halin yanzu ku duba ku gani gwamnatin sahyoniyawa ta sanar da cewa kasar Palastinu kasar yahudawa ce. Sun sanar da ita a matsayin wata kasar yahudawa. Tun da jimawa suke son yin hakan, to amma a halin yanzu sai ga shi sun sanar da hakan a fili. Cikin gafalar duniyar musulmi da gafalar daidaikun al’ummar musulmi, gwamnatn sahyoniyawa take shirin kwace Kudus mai alfarma, take nufin kwace masallacin al-Aksa, ta ke nufin raunana al’ummar Palastinu gwargwadon yadda za su iya. Wajibi ne a fahimci hakan. Wajibi ne dukkanin al’ummar musulmi su bukaci gwamnatocinsu da su ba da himma ga lamarin Palastinu; haka su ma malaman musulmi wajibi ne su bukaci hakan daga wajen gwamnatocinsu da su ba da himma ga lamarin Palastinu. Wannan daya ne daga cikin manyan ayyuka masu muhimmanci. Mu dai muna gode wa Allah cewa Jamhuriyar Musulunci, bakin gwamnati da na al’umma sun zo daya. Tun ranar farko gwamnati da marigayi Imam Khumaini suka sanar da siyasar nuna goyon baya ga Palastinu da kuma kiyayya da gwamnatin sahyoniyawa sannan kuma suka ci gaba da riko da hakan. Har ya zuwa yau din nan ana ci gaba da riko da hakan. Shekaru 35 kenan ba mu kauce wa wannan tafarkin ba, sannan kuma al’ummarmu cikin dukkanin so da kauna suke riko da hakan. A wasu lokuta wasu daga cikin matasanmu da ba amsa musu bukatunsu kan wannan lamarin ba, su kan rubuto min wasika suna rokon da in ba su izinin su tafi su kasance a sahun gaba-gaba na fada da gwamnatin sahyoniyawa. Al’ummarmu suna shaukin fada da sahyoniyawa sannan kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ma ta nuna hakan.
Cikin yardar Allah da falalarsa mun tsallake kan iyakar sabani na mazhaba. Irin taimakon da muke ba wa kungiyar Shi’a ta Hizbullah ta kasar Labanon, irin wannan taimakon mu ke ba wa kungiyoyin Hamas da Jihadi Islami, kuma za mu ci gaba da yin hakan. Mu ba mu fada tarkon iyakancewa ta mazhaba ba; ba ma ganin wannan Shi’a ne wannan Sunna ne, wannan Bahanafe ne, wancan Bahambale ne, wannan Bashafi’e ne wannan Bazaide ne. Mu abin da muke kallo shi ne wannan manufa ta asali. Don haka muke taimakawa. Mun sami nasarar karfafa ‘yan’uwanmu Palastinawa a Gaza da sauran yankuna. Da yardar Allah za mu ci gaba da yi. Na sanar kuma ko shakka babu za a yi hakan cewa wajibi ne a karfafa yankin Yammacin Kogin Jordan da makamai kamar yadda aka yi wa Gaza don su sami damar kare kansu.
Ina son sanar da ku, Ya ku ‘yan’uwa masu girma cewa: kada ku bari girman kan Amurka ya razana ku; makiyan sun yi rauni. Makiyan Musulunci, wadanda su ne ma’abota girman kai, sun yi rauni ainun sama da shekaru 100 zuwa 150 din da suka gabata. Ku dubi gwamnatocin ‘yan mulkin mallaka na Turai ku gani: suna cikin tsaka mai wuya na tattalin arziki, na siyasa da na tsaro. A yau gwamnatocin kasashen Turai suna fuskantar matsaloli kala-kala. Amurka kuma ta fi su shiga tsananin; tana fuskantar matsalar kyawawan halaye, matsaloli na siyasa, matsaloli masu tsanani na kudi da tattalin arziki, tana fuskantar matsala cikin matsayin da take da shi na tinkaho da karfi a duk fadin duniya. Ba wai kawai a duniyar musulmi ba, face dai a dukkan duniyar. Haka nan gwamnatin sahyoniyawa ma ta yi rauni ainun idan aka kwatanta ta da shekarun baya. Ita ce dai gwamnatin da ta ke rera taken “Daga Nilu Zuwa Furat”. A fili take daga murya da cewa tun daga Kogin Nilu zuwa Furat duk mallakinmu ne. Amma sai ga shi kwanaki hamsin suka yi a Gaza sun gagara gano ko da rami guda na ‘yan gwagwarmayar Gaza. Wannan dai ita ce wannan gwamnatin. Kwanaki hamsin, sun yi amfani da dukkanin karfin da suke da shi, wajen rusa ramukan ‘yan gwagwarmayar kungiyoyin Hamas da Jihad da Palastinawa, amma sun gagara. Ita ce dai wannan gwamnatin da take fadin daga Nilu zuwa Furat, to amma ku dubi irin bambancin da aka samu da irin raunin da ta yi.
Matsalolin makiya Musulunci suna da yawa. Makiya Musulunci sun gaza a Iraki; a Siriya ma sun gaza; a Labanon ma sun gaza; a yankuna daban-daban ma sun gaza, sun gagara cimma manufofinsu. A fadar da suke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kun ga yadda Amurka da kasashen ‘yan mulkin mallaka na Turai suka hadu da amfani da dukkanin karfinsu wajen dunkufar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin shirin nukiliyanta. Amma sun gagara dunkufar da ita, kuma a nan gaba ma ba za su iya ba.
Wannan shi ne irin raunin da makiyanmu suka yi. Da yardar Allah za ku ci gaba da karfafa a kullum. Makoma ta ku ce. “Kuma Allah ne marinjayi a kan al’amarinsa” (Suratu Yusuf 12:21)
Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
NB