A+ R A-
29 February 2020

Hirar Shugaban Kasar Siriya Dr. Basshar al-Asad Ta Tashar Talabijin Ta Al-Manar

Abin da ke biye fassarar hirar da shugaban kasar Siriya Dakta Basshar al-Asad ya yi da tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon ne, a ranar Alhamis 30, Mayun, 2013, wadda Sayyida Batul Ayyub ta gudanar:

 

Tambaya: A halin yanzu dai ga mu nan a Fadar Al’umma (sunan fadar shugaban kasar Siriya). Shekaru biyu da rabi kenan na rikicin kasar Siriya, alhali kuwa tunanin wasu shi ne cewa gwamnatin (Siriyan) za ta fadi cikin ‘yan makonni ne. Ya ya aka yi ka iya samun nasarar hana ‘yan adawa da makiya cimma hakan? Mene ne sirrin wannan tsayin dakan da kuka yi?

 

Shugaba Asad: Akwai bangaren kasar Siriya da ya ruguza wannan makircin sannan kuma akwai bangaren su kansu wadanda suka kulla makircin, inda su da kansu suka rusa kansu. Da farko dai sun rusa kansu ne ta hanyar rashin fahimtar hakikanin yanayin kasar Siriya da kuma rashin gudanar da bincike kan hakikanin yanayin kasar Siriyan. Da farko dai sun fara ne da fakewa da sunan juyin juya hali. Juyin juya hali kuwa yana bukatar wasu abubuwa a kas, babu yadda za ka iya haifar da juyin juya hali da kudi. Don haka sun gagara samar da irin wannan yanayin da ake bukata wajen kaddamar da juyin juya hali na hakika.

Daga nan sai suka koma suna magana irin ta mazhaba da kabilanci da nufin haifar da rikici a tsakanin al’ummar Siriya. Sun sami nasarar kutsawa ta hanyar wasu abubuwa na gefe da ake da su a cikin al’ummar Siriya, wadanda kuma kowace al’umma ma tana da su. Wadannan bangarori kuwa su ne jahilci da raunin fahimta. To amma duk da haka sun gagara haifar da wannan wutar a yanayi na hakika. Da a ce sun sami nasara, to da kuwa an raba kasar Siriya tun farko-farkon rikicin ma.

Sun sake amfani da wani maudhu’in na daban inda a nan ne suka fada rami (da tarkon da suka dana), hakan kuwa shi ne cewa rikicin da ke faruwan, wani rikici ne na neman mulki. To a fili yake cewa rikicin ba rikici ne na mulki ba, face dai rikici ne na kishin kasa, ba rikici ne na mulki ba. Babu wani mutum da zai yi yaki da kuma yin shahada saboda tabbatar da mulki ga wani mutum.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, a yayin wannan gumurzun, daga dukkan alamu sai bayan shekaru biyu da rabi ne gwamnatin Siriya ta fara samun ci gaba a fagen daga, hakan ya haifar da tambayar cewa me ya sa sai bayan shekaru biyu da rabi kuka zabi tashi daga matsayi na kariya zuwa ga matsayin kai hari. Ba ka ganin kun makara wajen daukar wannan matsayi na kai hari ta yadda a halin yanzu kun fuskanci gagarumar matsala idan muka dauki garin Qusayr a matsayin misali?

 

Shugaba Asad: A bangaren dababar kariya ko hari na soji, ba mu dogara kawai da dabarar yaki da ake amfani da ita a kananan yakukuwa ba. Muna mu’amala da lamarin ne ba wai kawai ta bangaren soji ba, face dai ta hanyoyi daban-daban, irin su bangaren siyasa da zamantakewa.

A farkon lamarin dai wani adadi mai yawa na mutanen Siriya sun rudu. Haka nan wasu kasashe kawayenmu ma da dama da ba su fahimci yanayin da ake ciki ba. Ba za a iya yin wani abu ba a cikin gida idan ya zaman ba a yi ittifaki kan wani lamari ayyananne ba. Ko shakka babu abubuwan da suka ta faruwa sun taimakawa al’ummar Siriya fahimtar hakikanin abin da ke gudana. Hakan ya taimaka wa sojojinmu sauke nauyin da ke wuyansu. Abin da ke faruwa a halin yanzu ba wai sauyi ne daga kariya zuwa kai hari ba, face dai sauyi ne na ma’aunin karfi da hakan ya taimaka wa sojojinmu.

 

Tambaya:  Ta ya ya aka sami wannan sauyin ma’aunin karfin? Wasu suna sukan kasar Siriya da cewa ta nemi taimakon mayaka daga waje. Ba tare da wani noke-noke ba, ana zarginku da amfani da mayakan kungiyar Hizbullah. Idan kana iya tunawa a hirar da ta gabata ka ce mu mutanen Siriya mu miliyan 23 ne, ba ma bukatar taimakon wani. To me Hizbullah take yi a Siriya?

 

Shugaba Asad: Dalili na farko da ya samar da irin wannan sauyi na ma’aunin karfi shi ne sauyin irin goyon bayan masu dauke da makamin suke samu. Da farko a wasu yankunan an samu wadansu mutane da suka goyi bayan masu dauke da makamin. A nan ba wai saboda karancin kishin kasa ba ne, face dai saboda karancin masaniya. Akwai labaran wasu mutane da suka mika kai ga ‘yan ta’adda da zaton cewa abin da ke faruwa wani yunkuri da juyi ne kan munanan abubuwan da ake da su. To amma daga baya an sami sauyin irin wannan goyon bayan. Akwai wani adadi mai yawa na masu dauke da makamin da suka fice daga cikin wadannan kungiyoyi (na ‘yan ta’adda) inda suka dawo cikin rayuwarsu ta ‘yan kasa, wannan shi ne babban dalilin.

A wajena maganar da ake yi a halin yanzu kan Hizbullah da shigowar mayaka daga wajen Siriya wani lamari ne mai girma da fadin gaske wanda kuma yake da bangarori da dalilai da yawa. Idan har muna son mu yi karin bayani kansa, wajibi ne mu yi karin haske kan batutuwan da suke da alaka da shi:

Ba za mu iya raba abin da a halin yanzu ake fadi dangane da batun Hizbullah da gumurzun garin Qusayr da kuma harin da “Isra’ila” ta kawo ba; lamurra ne guda uku a waje guda. Bari in yi magana a fili ba tare da wani noke-noke ba. A baya-bayan nan musamman bayan jawabin da Sayyid Hasan Nasrallah (babban sakataren kungiyar Hizbullah) ya yi, kafafen watsa labaran kasashen larabawa da wadanda ba na larabawa ba suna ta maganar cewa mayakan Hizbullah sun shigo cikin kasar Siriya don kare gwamnatin Siriya. Idan har za mu yi magana daidai da hankali, idan har Hizbullah tana son ta kare Siriya da gwagwarmaya, sanann idan tana son ta tura mayakanta, guda nawa za ta tura? Daruruwa, dubu guda, dubu biyu? Muna magana ne kan wani yaki da a cikinsa akwai daruruwan dubban sojojin kasar Siriya da gomomin dubban ‘yan ta’adda, idan ma ba su wuce haka ba, daruruwan dubbai don kuwa adadinsu karuwa yake yi. Wato kasashen makwabta da sauran gwamnatocin da suke goyon bayan ‘yan ta’addan suna ci gaba da shigo da ‘yan ta’addan. A saboda haka adadin da kungiyar za ta iya bayarwa don kare gwamnatin a wannan gumurzun idan aka kwatanta da yawan ‘yan ta’addan da kuma yawan sojojin gwamnati da kuma irin fadin kasar Siriya, to wannan adadin ba za su kare gwamnati ba.

Wannan a bangare guda kenan, idan kuma sun ce suna kare gwamnati ne, to me ya sa sai yanzu? Me ya sa a wannan lokacin? Wannan rikici dai ya faro ne bayan watan Ramalanan shekara ta 2011, sannan kuma ya ci gaba da girma har zuwa bazarar shekara ta 2012. Sun fara ne da yakin ‘yanto Damaskus, inda suka ayyana lokacin farawa na farko da na biyu, inda suka kashe manyan kwamandojin tsaro su hudu, sannan kuma aka samu ficewar wasu daga gwamnati. Da dama sun zaci cewa lokacin faduwar gwamnatin ya yi, amma ba ta fadi ba. Duk da hakan kungiyar Hizbullah ba ta shigo a lokacin ba, to amma me ya sa ta shigo a yanzu? Wannan bangare ne mai muhimmanci. Me ya sa ba mu ga Hizbullah a Damaskus da Halab ba, don kuwa mafi girman gumurzun da aka yi a Damaskus da Halab ne ba wai a Qusayr ba. Qusayr wani karamin gari ne. Me ya sa ba mu ga Hizbullah din a Homs ba? Dukkanin wadannan abubuwan da suke fadi ba haka ba ne. Qusayr gari ne mai muhimmanci don kuwa waje ne da ‘yan ta’addan suke amfani da shi wajen shigo da ‘yan ta’adda da kuma makamai. A saboda haka dukkanin abubuwan da aka fadi dangane da shigowar Hizbullah ba haka lamarin yake ba.

Dukkanin irin ihu bayan hari da muke ji a kafafen watsa labaran larabawa da abubuwan da jami’an kasashen larabawa suke fadi da ma na kasashen yammaci, kai har ma Ban Ki Moon (babban sakataren majalisar dinkin duniya) ya fadi cewa yana cikin damuwa da tsoron kasantuwar Hizbullah a Qusayr. Dukkanin wadannan maganganu ne da nufin bata sunan gwagwarmaya, ba shi da wata alaka da batun kare gwamnatin Siriya. Don kuwa wadannan ci gaban da kika yi ishara da su sun faru ne a Halab da Damaskus da garuruwan da suke wajen Damaskus da sauran wajaje, amma ba mu ji irin wadannan ihu da maganganun da ake yi ba.

 

Tambaya: Yanayin yakin da kuke yi a garin Qusayr tare da kungiyar Hizbullah ya sa wasu suna zargin cewa kuna yin wannan yakin ne don share wata hanya da za ta hada gabar Tekun Siriya da birnin Damaskus ta yadda idan har yanayi ya sanya za a raba kasar Siriya ko kuma wani sauyi na yanayin yankin nan ya faru za ku sami damar kafa gwamnatin Alawiyawa. Ya ya yanayin wannan yaki yake, shin yana da alaka da rikicin da ake yi da ‘“Isra’ila”’.

 

Shugaba Asad: Da farko dai gabar ruwan Labanon da Siriya ba ta wuce ta Qusayr ba idan ana magana ne a bangaren waje, babu gaskiya cikin wannan maganar. Abu na biyu: babu wani da yake yaki don a raba kasar nan. Idan wani yana yaki saboda raba kasa, to yana iya yin yaki don raba kasar, to amma mu kan ba muna yaki ne a duk fadin kasar Siriya da nufin raba kasar ba. Yanayin yadda yakin yake gudana ba ya nuni da cewa akwai wanda yake son raba kasar Siriya, face dai wannan yakin yaki ne don tabbatar da hadin kan kasar Siriya, ban da akasin hakan.

Batu na uku kakaninmu sun gwada hakan da turawan Faransa a lokacin da Faransa ta gabatar da batun raba kasar Siriya. Tun a wancan lokacin kakanninmu sun kasance sun fahimci wannan lamarin. Shin mai yiyuwa ne mu din nan jikokinsu bayan shekaru aru-aru mu zamanto marasa fahimta da tunani?

Ina sake jaddada cewa wannan yakin da ma dukkanin abin da ke faruwa a Qusayr, da kuma dukkanin irin wadannan maganganun da ake fadi duk suna da alaka ne da ‘“Isra’ila”’. Yakin Qusayr yana da alaka ne da harin da ‘“Isra’ila” ta kawo. Abin da ake so shi ne kawo karshen gwagwarmaya. Wannan tsohon rikici da yaki, a kowane lokaci ya kan sauya salo. A halin yanzu lamarin ba shi ne garin Qusayr a matsayinsa na gari ba, abin da ke da muhimmancin shi ne kan iyaka. Abin da ake son yi shi ne takurawa kungiyar gwagwarmaya (Hizbullah) ta kasa da ruwa. A saboda haka a nan tambaya ta kan taso cewa: ana fadin cewa kamata ya yi kungiyar gwagwarmaya ta yi amfani da makamanta ne kan makiya, wato zuwa kudanci (‘“Isra’ila”). An fadi wannan maganar a ranar 7 ga watan Mayu a lokacin da wasu ‘yan amshin shatan “Isra’ila” a Labanon suka yi kokarin lalata hanyar sadarwar kungiyar gwagwarmayar (Hizbullah), inda suka ce kungiyar gwagwarmayar ta yi amfani da makaminta a cikin gida. Wannan shi ne abin da suka fadi dangane da sojojin kasar Siriya na cewa kamata ya yi su yi yaki ne a kan iyakan kasar da “Isra’ila”. Mu dai a fili mun fadi cewa sojojinmu za su yaki makiya a duk inda suka same su. A saboda haka idan makiyi ya kasance arewaci ko kuma ya zo ta arewaci, to sai mu tinkari arewacin ko gabashi ko yammaci. Haka lamarin yake dangane da kungiyar gwagwarmaya. Me ya sa Hizbullah suka kasance a kan iyaka cikin Labanon ne ko cikin Siriya, saboda yakin, yaki ne da “Isra’ila”wa makiya ko kuma da wakilansu a kasar Siriya ko kuma a Labanon.

 

Tambaya: Dangane da shigowar ‘“Isra’ila”’ cikin rikicin kasar Siriya a baya-bayan nan ta hanyar harin da ta kai wajen birnin Damaskus. Kai tsaye “Isra’ila” ta sanar da cewa ba tana son yaki ba ne sannan kuma ba tana son shigowa cikin rikicin Siriyan ba ne. To tambaya a nan ita ce me “Isra’ila”n take so, sannan wani irin tsoma baki cikin harkokin Siriya take son yi?

 

Shugaba Asad: Wannan shi ne abin da ke tabbatar da abin da na fadi na cewa dukkanin abin da ke faruwar yana da alaka da kokarin murkushe gwagwarmaya a matakin farko. Wato hatta shigowar “Isra’ila” tare da ‘yan ta’adda ko kuma irin goyon bayan da take ba wa ‘yan ta’addan, wasu abubuwa guda biyu suke son cimmawa:

Na farko shi ne makure kungiyar gwagwarmaya. Na biyu kuma rusa makaman kariyar kasar Siriya. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa wadannan su ne manyan manufofin “Isra’ila”, (idan ta cimma wadannan biyu) to sauran ba su dame ta ba.

 

Tambaya: To mai girma shugaban kasa, da ya ke manufar “Isra’ila”ta fito fili, hakan ne ya sanya wasu zargin jagorancin Siriya da kuma gwamnatin kasar da rauni wajen mayar da martani. Kowa ya zuba ido da fatan ganin martanin da Siriya za ta mayar. Sai dai abin da gwamnatin Siriya ta ce shi ne ta bar wa kanta hakkin mayar da martanin a lokacin da kuma wajen da ta ga ya dace. Me ya sa ba a mayar da martani kai tsaye ba. Shin abin da aka jiyo daga wasu majiyoyi na cewa an shirya makamai masu linzami zuwa “Isra’ila”da kuma cewa za a mayar da martani ga duk wani hari ba tare da an koma ga jagorori don neman izini ba, ya wadatar?

 

Shugaba Asad: Mun sanar da kasashen larabawa da wadanda ba na larabawa ba, mafiya yawansu ma wadanda ba na larabawa din ba ne da suka bugo mana, cewa za mu mayar da martani a duk wani sabon harin da za su kawo mana. Na’am “Isra’ila” ta yi kokarin kutsawa a lokuta da dama kuma an mayar mata da martani kai tsaye. To amma mayar da martani na wucin gadi ba shi da wata kima; wato martani na siyasa. Idan har muna son mayar wa “Isra’ila” da martani, to wajibi ne ya kasance wani raddi ne na hakika kuma mai girman gaske.

 

Tambaya: Ta ya ya, ta hanyar bude sansanin Golan (ga ‘yan gwagwarmaya) a matsayin misali?

 

Shugaba Asad: Da farko dai hakan ya dogara ne da yanayi na mutane da ake da shi, shin mutane sun kama hanyar gwagwarmaya ne ko kuma a’a?

 

Tambaya: Yaya yanayi yake a kasar Siriya?

 

Shugaba Asad: A takaice dai akwai matsin lamba na mutane don a bude sansanin Golan ga ‘yan gwagwarmaya. Akwai kumaji na larabawa. Kai akwai ma wata tawaga ta larabawa da ta zo nan, tana fadin cewa: A ina ne ake rajistar mutane? Suna son su zo su yaki “Isra’ila”. To ayyukan gwagwarmaya dai ba aiki ne mai sauki ba. Lamarin ba shi ne kawai bude fagen daga ba. Lamari ne na akida da siyasa da zamantakewa, sannan kuma wani lamari ne na soji.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, idan muka yi la’akari da abin da ya faru a Golan ta hanyar harin da aka kai wa wata motar sojin “Isra’ila” da ta ketare layin tsagaita wuta da aka shata (da sojojin Siriyan suka kai kwanakin baya). Shin hakan yana nufin an sami sauyi ne daga yanayin da ake ciki zuwa ga wani yanayi na fito na fito. Idan har haka lamarin ya ke, to mene ne wannan sauyin da aka samun?

 

Shugaba Asad: Sauyi na hakika cikin yanayin fito na fiton zai faru ne a lokacin da ya zamanto akwai yanayi na mutane da suka kama hanyar gwagwarmaya. Duk wani sauyi da aka samu, sauyi ne na gajeren lokaci, sai dai idan mun kama hanyar yaki. Duk wani mayar da martani zai zamanto na karfafa gwiwa ne ko kuma daga waje. Ni dai ban yi imani da hakan ba. Sauyi na hakika shi ne mutane su kama hanyar gwagwarmaya. Wannan shi ne sauyi na hakika kuma mai tasiri.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa…ba ka ganin wannan maganar ta zo a makare? Me ya sa sai bayan shekaru arba’in na tsagaita wuta a Golan…amma a yanzu ana maganar bude fagen dagar Golan din, saboda me?

 

Shugaba Asad: A koda yaushe suna maganar cewa Siriya tana budewa da kuma rufe fagen daga. Gwamnati dai ba ta samarwa ko kuma kirkiro gwagwarmaya. Matukar dai gwagwarmaya ba ta kasance ta al’umma kuma ta gama gari ba, to ba gwagwarmaya ba ce, sannan kuma babu yadda za a iya samar da ita. Ita dai gwamnati ko dai ta taimaka ko kuma ta hana gwagwarmayar kamar yadda yake faruwa a wasu kasashen larabawa. Ni dai na yi imani da cewa duk wata gwamnatin da take hana gwagwarmaya to gwamnati ce da bata san inda aka sa gaba ba.

A saboda haka lamarin ba shi ne cewa kasar Siriya, bayan shekaru arba’in, ta kuduri aniyar komawa ga wannan bangaren ba ne. Akwai sojoji da suke gudanar da aikinsu, don haka mutane suna jin cewa akwai wani da yake gudanar da wannan aikin, yana aiki don ‘yantar da yankin da aka mamaye. Idan da a ce babu sojoji, kamar yadda ya faru a kasar Labanon a lokacin da kan sojojin kasar ya rabu haka ita ma gwamnati kanta a rabe yake, wato a lokacin yakin basasa kenan, to kuwa da tuni an kaddamar da gwagwarmaya.

To a irin wannan yanayin akwai wasu abubuwa da suka sanya mu daukar wannan matsayar. Na farko ci gaba da hare-haren da “Isra’ila” take kawo wa, hakan shi ne babban dalilin da motsa mutane. Na biyu shagaltuwar da sojojin Siriya suka yi da fada a yankuna daban-daban na kasar. Hakan shi ne ya sanya da dama daga cikin mutane jin cewa lalle wajibinsu ne a halin yanzu su motsa don taimakon sojoji a Golan.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa….Netanyahu (firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila) ya bayyana cewar “Isra’ila” ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kai hari kan Damaskus a duk lokacin da suka ga za a aika wa kungiyar Hizbullah makaman da za su iya sauya yanayin karfin da ake da shi. Idan har “Isra’ila” ta aikata hakan, ina son in ji amsa kai tsaye daga wajenka, me kasar Siriya za ta yi?

 

Shugaba Asad: Kamar yadda na ce, mun sanar da wasu gwamnatoci cewa lalle za mu mayar da martani kan duk wani harin da aka kawo mana. Na’am abu ne mai wahala a halin yanzu a bayyana hanyar da za a bi wajen mayar da wannan martani a bangaren soji. Hakan lamari ne da ke hannun kwamandojin soji. To amma mu dai akwai abubuwan da muka tsara da mai yiyuwa su faru, hakan ya dogara ne da irin yanayin da ake ciki a yayin harin. Wato yanayin da zai ba da damar amfani da hanya kaza ko makami kaza ta hanyar da ta fi dacewa da kuma yin tasiri.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa…bayan harin “Isra’ila” na baya-bayan nan a kan birnin Damaskus, an fara magana kan makamin nan samfurin S300 da cewa makami ne mai tasirin gaske. A saboda haka ne Netanyahu ya kai ziyara birnin Mosko. Tambaya a nan ita ce, shin wadannan makamai masu linzami suna kan hanyarsu ta zuwa Damaskus? Shin Siriya ta mallaki wadannan makaman ne a halin yanzu?

 

Shugaba Asad: A al’adance dai ba ma magana kana abin da ya shafi soji, wato irin makaman da suka iso gare mu da kuma wadanda muke da su. To amma dangane da batun yarjejeniyar da muka kulla da kasar Rasha, ba ta da alaka da wannan rikicin da ke faruwa. Mun kasance muna tattaunawa da su kan nau’oi daban-daban na makamai tun shekaru. Sannan kuma nauyi ne a kan Rasha ta cika yarjejeniyar da ta kulla da Siriya. Abin da nake son fadi shi ne cewa ziyarar Netanyahu ko kuma wannan rikicin ba za su yi tasiri cikin turo wadannan makaman ba. Dukkanin abubuwan da muka cimma yarjejeniya kansu da Rasha za a cika su. A kwanakin nan ma wasu daga cikinsu sun iso. Mu da Rasha za mu ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniyar da aka kulla.

 

Tambaya: Mun yi magana kan tsayin dakan jami’ai da gwamnatin Siriya, haka nan mun yi magana kan irin nasarorin da kuke samu a fagen daga da kuma irin karfafa hadin gwiwan da ke tsakanin Siriya da kungiyar gwagwarmaya (Hizbullah), dukkanin wadannan abubuwa ne da suke faruwa a fagen daga. A daya fagen kuma, akwai kokari na diplomasiyya tun shekaru biyu da rabin da suka gabata. Kafin mu je ga batun taron Geneva da kuma sharuddan da Siriya ta kafa, akwai wata hanya da shugaban hadin gwiwan ‘yan adawan Siriya mai murabus Mu’az Khatib ya gabatar kan yadda za a magance matsalar Siriyan. Ya ce za a bar shugaban kasar Siriya tare da wasu mutane 500 da zai zaba su bar kasar cikin kwanaki 20 shi kenan sai a kawo karshen rikicin. Me ya sa ba za ku amince da wannan bukatar ba, don a kawo karshen wannan rikicin?

 

Shugaba Asad: Ni a koda yaushe ina magana bisa wani tushe, wanda shi ne cewa batun ci gaba da zaman shugaban kasa ko saukarsa lamari ne da ya shafi al’ummar Siriya. Duk wanda zai yi magana a wannan bangaren wajibi ne ya fadi wa yake wakilta daga cikin al’ummar Siriyan. Shin al’ummar Siriya ne suka wakilta shi ko kuma? Amma dangane da wannan shawarar, a hakikanin gaskiya ni dai ban karanta ta ba, ni dai na ji ta ne kawai. To amma dai na yi farin ciki ainun cewa ya bani kwanaki 20 da kuma mutane 500. Ni dai bani da tabbas cewa wannan shawarar tasa ce ko kuma ta wani mutum na daban. Ni ba kasafai na ke damuwa da sunaye ba.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, abin da ya gabatar shi ne cewa ya ba ku kwanaki 20 da mutane 500 amma shi din ma ba tare da lamuni ba. Za a iya fita waje amma dai ba za mu ba da lamunin cewa ba za a iya gurfanar da su a gaban kotu ba. To mai girma shugaban kasa, wannan ne zai kai mu zuwa ga batun tattaunawa. Muna magana ne dangane da taron Geneva na 2. Gwamnatin Siriya ta sanar da amincewarta a yanayi na gaba daya.To a tattaunawa dai akwai batun teburin da za a zauna a kai. Idan har aka gudanar da wannan taro na tattaunawar, zai zamana akwai tutar Siriya da kuma tutar ‘yan adawa. Ta ya ya za ka iya kwantar wa mutanen Siriya da hankali cewa bayan shekara biyu da rabi na wannan rikicin ga shi yanzu kana zaune a teburi guda tare da ‘yan adawa?

 

Shugaba Asad: Da farko dangane da batun tuta, a koda yaushe na kasance ina fadin cewa tuta dai ba ta da ma’ana ba tare da mutanen da take wakilta ba. A lokacin da muka sanya tuta a kan wani waje na teburi muna nuni ne da mutanen da suke da alaka da tutar. Muna iya tambayar wadanda suke son ajiye wata tuta wacce ba ta Siriya ba a karkashin inuwar kasar Siriya. Tuta ba ta da wata kima matukar dai ba tana wakiltar mutane ba ne.

Wannan bangare na farko kenan. A daya bangaren kuma za mu tafi wajen wannan taron ne a hukumance a matsayin halaltattun masu wakiltar al’ummar Siriya, to amma su, wa suke wakilta. Mu dai a lokacin da aka gama taron za mu dawo Siriya ne, za mu dawo gidajenmu, za mu dawo cikin al’ummarmu. To amma su idan idan aka gama taron (ina za su koma)…zuwa manyan otel-otel da aka sauke su ko kuma zuwa ga ma’aikatun harkokin wajen kasashen da suke wakilita…ba wai Siriya ba kan…don su gabatar musu da rahotanni ko kuma zuwa ga kungiyoyin leken asirin wadancan gwamnatocin. A saboda haka a lokacin da muka tafi wajen wannan taron, wajibi ne mu fahimci cewa wani bangare na wadanda za su zauna a kan wannan teburin, na ce wani bangare ne saboda har ya zuwa yanzu yanayin yadda za a gudanar da taron bai bayyana ba tukun, mene ne matsayar ‘yan adawa na cikin gida kan lamarin, haka nan mece ce matsayar sauran kungiyoyi da suke cikin gida da sauran su. Dangane da ‘yan adawa da suke waje wadanda kike magana kansu da kuma ayyukansu, mu dai mun san cewa za mu je ne mu tattauna da kasashen da suke goya musu baya, ba wai su ba. Don kuwa a lokacin da kake tattaunawa da bawa, a hakikanin gaskiya kana tattaunawa ne da ubangijinsa. Wannan ita ce hakikar.

 

Tambaya: Shin jami’an kasar Siriya suna da tabbacin cewa lalle za a gudanar da wannan taron da kuma tattaunawar a wata mai kamawa?

 

Shugaba Asad: Na’am…mu dai muna fatan ganin hakan sai dai idan wasu gwamnatoci sun yi kafar ungulu. Dangane da mu a Siriya, tun kimanin kwanaki biyun da suka gabata mun sanar da cewa a yanayi na gaba daya za mu halarci taron.

 

Tambaya: Wannan kalma ta ‘a yanayi na gaba daya’, wato amincewa a yanayi na gaba daya, me ya sa a koda yaushe ake maganar yiyuwar dawowa baya daga wannan amincewar?

 

Shugaba Asad:  Saboda taron a kan kansa abu ne mai kyau…to sai dai abin da ya rage shi ne abubuwan da ya kumsa da kuma yadda za a gudanar da shi. Shin a matsayin misali akwai wasu sharuddan da za a kafa. Idan har suka sanya sharudda, to mai yiyuwa ne mu ki amincewa da su. To amma shi kansa taron, ganawa da tattaunawa, lamari ne mai kyau. Wannan shi ne abin da muke nufi.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa…bari mu yi magana kan sharuddan da kasar Siriya za ta kafa…shin mene ne sharuddan kasar Siriya?

 

Shugaba Asad: Sharadi guda muke da shi, shi ne cewa duk wani abin da za a cimma a duk wani taro shin na cikin gida ne ko na waje ciki kuwa har da wannan taron, wajibi ne ya zamanto al’ummar Siriya sun amince da shi da kuma kuri’ar jin ra’ayin al’ummar Siriyan. Wannan shi ne sharadi guda na hakika, wani abu na daban ba shi da wata kima. A saboda haka ne za mu tafi can cikin kwanciyar hankali, ba mu da wani abin damuwa. Suna iya gabatar da duk wani abin da suke so, mu ma muna iya gabatarwa, to amma babu wani abin da za a aiwatar wanda al’ummar Siriya ba su amince da shi ba. To da ya ke a shar’ance mu ne mu ke wakiltar al’ummar Siriyan, don haka babu wani abin da muke jin tsoronsa.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, bari mu kara neman bayani. Akwai duhu da rudu sosai cikin taron Geneva na 1 da Geneva 2 dangane da lokacin rikon kwarya da kuma rawar da shugaban Siriya Basshar al-Asad zai taka a wannan lokacin. Shin kana shirye ka mika dukkanin ikon da kake da shi ga gwamnatin rikon kwaryar? Shin ya ya kake fahimtar wannan kalma ta cewa akwai rudu cikin lamarin.

 

Shugaba Asad: Wannan shi ne abin da na fadi cikin shawarwarin da na gabatar a watan farko na wannan shekarar. Suna fadin cewa suna son gwamnatin rikon kwarya da shugaban kasa ba shi da ta cewa a cikinta. To a hakikanin gaskiya shugaban kasa dai ba shi ne yake jagorantar hukuma ba. A Siriya tsarin shugaban kasa ne ake amfani da shi, a wannan tsari shugaban kasa ba shi ne ya ke jagorancin hukuma ba, akwai shugaban hukuma. Suna son hukuma mai fadadden iko. Kundin tsarin mulkin Siriya ya ba wa hukuma cikakken iko, shi kuwa shugaban kasa shi ne babban kwamandan sojoji da sauran dakaru masu makami, shi ne kuma shugaban majalisar koli ta shari’a. Amma sauran cibiyoyi da hukumomi suna karkashin hukuma ne kai tsaye. Amma dangane da ikon shugaban kasa, yana karkashin kundin tsarin mulki ne. Shugaban kasa ba shi da ikon yayi watsi da ikon da ya ke da shi. Ba shi ne mai kundin tsarin mulki ba. (Idan ana son haka) to akwai bukatar a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin al’umma. Idan suna so suna iya gabatar da hakan a lokacin taron, idan mun cimma abu guda, sai mu koma mu gabatar da shi ga mutane ta hanyar gudanar da kuri’ar jin ra’ayin al’umma. Daga nan sai mu ga ra’ayin al’ummar Siriya, sai mu ci gaba da tafiya. Amma a fara da bukatar a sauya kundin tsarin mulki, to wannan kan ba abu ne da shugaban kasa ko hukuma ba za su yi ba. Saboda a dokance ma ba mu da ikon yin hakan.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, a fili yake cewa dukkanin gwamnatocin waje masu adawa da ku, haka nan dukkanin masu adawa da ku a fagen siyasa suna fadin cewa mu dai ba ma son ganin Asad cikin shugabancin kasar Siriya a nan gaba. Wannan shi ne abin da Sa’ud Faisal (ministan harkokin wajen Saudiyya), haka nan gwamnatin Turkiyya da Qatar da kuma ‘yan adawan Siriya suke fadi. Shin shugaba Asad zai sake tsayawa takaran shugabanci a shekara ta 2014?

 

Shugaba Asad: Ni dai na san cewa Sa’ud Faisal kwararre ne kan abin da ya shafi Amurka, ban sani ba ko ya san wani abu dangane da lamarin kasar Siriya. Idan har yana son sani, to babu matsala cikin hakan. Amma dangane da abin da wasu suke so, to bari in sake fadin cewa babu wata bukata sama da abin da mutanen Siriya suke so. Dagane da batun tsayawa takaran zaben shugaban kasa, wasu sun gabatar da cewa zai yi kyau idan shugaban kasa bai sake tsayawa takara a shekara ta 2014 ba. To ni dai na ce idan lokacin ya zo ne za a iya tantance wannan lamarin. Akwai sauran lokaci, don haka an yi gaggawa wajen gabatar da lamarin a yanzu. Idan lokacin ya yi sannan kuma idan na ji cewa akwai bukatar in sake tsayawa, tabbas wannan bukatar za ta taso ne bayan tuntubar mutane, idan har na ji cewa suna son in tsaya, to kuwa ba zan yi wani jinkiri ba. Amma idan har na ji cewa mutanen Siriya ba sa so, to a fili yake cewa ba zan tsaya ba. Suna bata lokacinsu ne wajen magana kan wannan lamarin.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, ka yi ishara da Sa’ud Faisal, ministan harkokin wajen Saudiyya, hakan ne ya sanya ni gabatar da tambaya dangane da alakar Siriya da Saudiyya, da Qatar da Turkiyya musamman idan muka yi la’akari da matsayarsu a taron ministocin kungiyar hadin kan larabawa na baya-bayan da ya yi kama da sassauci. Wato a fili dai ba su gabatar da bukatar shugaban kasa ya sauka ba. Shin ka ga wani sauyi ko goyon bayan su ga batun magance matsalar kasar Siriya ta hanyar siyasa? Shin kasar Siriya a shirye take ta sake mu’amala da kungiyar hadin kan kasashen larabawan, musamman idan aka yi la’akari da cewa gwamnatin Siriya ta bukaci kungiyar da ta nemi gafara.

 

Shugaba Asad: Dangane da kasashen larabawa, sauyin da muke gani na wani lokaci cikin jawabai ne amma ba cikin aiki ba. Kasashen da suke taimakawa ‘yan ta’adda ba su sauya ba. Suna ci gaba da taimakon ‘yan ta’addan kamar yadda suke yi a baya. Turkiyya ma babu wani abu na a zo a gani a kas. Dangane da kasar Qatar tana nan a wajen da take, mai ba da kudi, bankin da ke ba da kudi da taimakon ‘yan ta’adda ta hannun Turkiyya. A hakikanin gaskiya babu wani sauyi.

Amma dangane da kungiyar hadin kan kasashen larabawa, mu dai a kasar Siriya ba mu dogara da ita ba, ba yanzu ba hatta a baya ma. Abin da muka sami damar yi shi ne magance wasu matsalolin da aka haifar a tarurrukan da ake gudanarwa, shin na shugabannin kasashe ne ko kuma na ministoci. Shin za mu iya dogaro da ita wajen ta taka wata rawa bayan irin matsayar da ta dauka a baya? Mu dai muna tattaunawa da kowa. Ba mu kulle kofa ba. To amma a hakikanin gaskiya wajibi ne mu zamanto masu kallon lamurra yadda suke. Ya kamata mu san cewa babu wani abin da kungiyar za ta iya yi, musamman bisa la’akari da cewa wani adadi mai yawa na kasashen larabawan ba su da ‘yancin kansu, ana ba su umurni ne daga waje. Wasu daga cikinsu suna tare da mu a zuci, to amma ba sa tare da mu a wajen aiki saboda lamurra ba a hannunsu suke ba. Ya kamata mu zamanto masu fadin hakika. Lalle mu dai ba mu da wani fata a kan wannan kungiyar ta larabawa.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, hakan ya kai mu ga tambayar cewa idan wannan shi ne yanayin kasashen larabawa, sannan kuma ga abin da ke gudana a fagen daga, haka nan kuma ga taron Geneva da tattaunawa, to tambaya a nan ita ce cewa me zai faru idan har ba a cimma gaci ba a tattaunawa ta siyasa, me zai faru sakamakon wannan rashin nasarar?

 

Shugaba Asad: Lalle akwai yiyuwar hakan saboda kuwa akwai wadansu gwamnatoci da suke kafar ungulu ga wannan taron tun farko. Idan da ba don wasu dalilai ba, tun farko ma dai tana adawa da tattaunawar, shin a cikin Siriya ne ko kuma a wajenta. Lalle akwai yiyuwar hakan. Hatta Rasha ma a lokuta da dama ta sha bayyanar da tsoronta kan wannan taron. To sai dai wajibi ne mu zamanto masu kallon lamurra yadda suke wajen magana kan wannan taro. Mece ce alakar wannan taro da abin da ke gudana a kas…da dama daga cikin kasashen da suke magana kan abin da ke faruwa a Siriya, ba su da alaka da cikin gidan Siriyan. Ba su da alaka hatta da ‘yan ta’addan kai tsaye. Su kansu ‘yan ta’addan a wasu bangarorin ne suke da alaka da wadannan gwamnatoci kai tsaye. A wasu lokuta wasu ‘yan daba ne da suke karban kudade gwargwadon ayyukan ta’addancin da suka yi. Rashin nasarar wannan taro ba na jin zai sauya wani abu a kas a cikin kasar Siriya don kuwa wadannan gwamnatocin ko da wannan taron ko babu shi, ba za su bar wannan goyon baya da suke bayarwa ba, su ma wadannan ‘yan ta’addan ba za su bar wadannan ayyuka na su na ta’addanci ba.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, rikicin Siriya ya fara naso zuwa wajen kasar, zuwa ga kasashen makwabta, wato abin da ke faruwa a Iraki, ga kuma harin da aka kai Reyhaniyya na kasar Turkiyya, haka lamarin ya ke a kasar Labanon, ga abin da ya faru a Ersal na kasar Labanon, ga abin da ke faruwa a Tripolin (Labanon), da shigowar Hizbullah cikin yakin Qusayr. Ya ya Siriya take ganin abin da ke faruwa a Labanon, shin tana ganin siyasar tsame kai da gwamnatin kasar ta dauka tana ci gaba da gudana sannan kuma ta amince da ita?

 

Shugaba Asad: Bari in gabatar da wasu tambayoyi kan lamurran da suke faruwa a Siriya da kuma Labanon dangane da wannan siyasa tsame kai, don kada a ce ina auna wannan siyasar ko kuma ina fadin wani abu kanta, shin daidai ne ko kuma a’a. Tambayar a nan ita ce, shin Labanon ta iya hana tsoma bakin ‘yan kasarta cikin Siriya, shin ta hana shigo da ‘yan ta’addan da kuma makamai zuwa Siriya ko kuma ba wa ‘yan ta’addan mafaka a Labanon. Ba su yi haka ba. A hakikanin gaskiya kowa ya san cewa kasar Labanon ta taimaka ta mummunan hanya cikin rikicin da ke gudana a Siriya. Kai a baya-bayan nan ma shin Labanon ta iya kare kanta daga sakamakon rikicin Siriya da ya fado kasar? babban misalin hakan shi ne abin da ke faruwa a Tripoli da kuma makamai masu linzamin da ake harbawa zuwa Beirut da wajensa. A aikace dai ta gaza. To wace siyasar tsame kai kuma ake magana. Tsame kan Labanon wani abu ne na daban, tsame kan gwamnatin Labanon kuma wani abu ne na daban. A lokacin da gwamnatin ta tsame kanta daga wani batu na musaman da wani batu da ya shafi al’umma, to kuwa ta tsame kanta ne daga mutane ne.

Ni dai ba ina sukan gwamnatin Labanon ba ne, ina magana ne a yanayi na gaba daya. Ba na so a ce ina sukan wannan hukumar. Idan da a ce gwamnatin Siriya za ta tsame kanta daga lamurran da suka shafi mutanenta, to kuwa da ta ci kasa a lokacin da wata matsala ta kunno kai a makwabtanta. A lokacin da gidan makwabcina ya kama da wuta, ba zan iya cewa babu ruwa na da hakan ba, don kuwa wutar za ta iya kama gidana ni ma. A saboda haka mu dai ba ma ganin wannan magana ce ta hakika.

 

Tambaya: Mai girma shugaban kasa, me za ka ce ga masoya tafarkin gwagwarmaya. A halin yanzu dai muna cikin bukukuwan nasara da ‘yanto (yankunan da haramtacciyar kasar “Isra’ila” ta mamaye a Labanon ne). A cikin irin wannan yanayi na alkawarin nasara da mai girma Sayyid Hasan Nasrullah ya yi, kuma ku na magana kan tabbacin samun nasara cikin wannan rikicin. Me za ka ce wa wadannan mutane. Shin mun kama hanyar fita daga wannan yanayi mai cike da duhu ne?

 

Shugaba Asad: Ni ina ganin babbar nasarar da gwagwarmayar larabawa ta samu cikin wadannan shekaru, a matakin farko ita ce nasara ta tunani. Wannan gwagwamayar ba za ta sami damar nasara ta soji ba idan ba tare da tsayin daka wajen tinkarar farfagandar gurbata ma’anonin abubuwa a wannan yankin ba. Kafin yakin basasar Labanon akwai wani abin da ake fadi cewa karfin Labanon yana cikin rauninta ne, wannan maganar ta yi daidai da fadin cewa wayon mutum yana cikin wautarsa ne, ko kuma daukakar mutum tana tafiya ne cikin lalacewarsa. Wannan dai ya saba wa hankali. Nasarorin da gwagwarmaya ta samu a lokuta daban-daban sun tabbatar da cewa wannan maganar ba gaskiya ba ce. Gaskiyar lamarin shi ne cewa raunin Labanon yana cikin rauninta ne, sannan karfinta kuma yana cikin karfinta. Karfin Labanon yana tare da gwagwarmayarta ne. Karfin Labanon yana tare da wadannan ‘yan gwagwarmayar da kike magana kansu ne.

A yau muna bukatar irin wannan tunanin da irin wannan tsayin dakan cikin ayyukan da wadannan ‘yan gwagwarmayar suke yi a wannan lokacin sama da lokutan da suka gabata. Saboda kuwa abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu ko kuma sama da haka da dan kadan da suka faru a kasashen larabawa sun cutar da wadannan ma’anoni ta yadda wasu daga cikin larabawan sun mance da cewa “Isra’ila” ce makiyarsu. Kiyayyar ta zamanto ta cikin gida, ga adawa ta kabilanci da mazhaba da sauransu. A yau dai mun dogara ne da wadannan ‘yan gwagwarmayar wajen tunatar da al’ummar Larabawa irin nasarorin da suke samu da cewa makiyinmu dai shi ne dai wancan din.

Amma dangane da tabbacin da nake da shi ga samun nasara, idan da a ce ba mu da tabbacin nasara, da ba mu sami karfin tsayin daka da kuma ci gaba da tsayuwa bayan shekaru biyu na wannan yaki da duniya ta kaddamar a kanmu ba. Makiyanmu dai ba su ne bangarori uku kamar yadda ya faru a shekarar 1956 ba, a hakikanin gaskiya yaki ne na duniya aka kaddamar a kan Siriya da kuma tafarkin gwagwarmaya. Lalle muna da tabbacin samun nasara. Ina son in sanar da su cewa Siriya za ta ci gaba da zama yadda take kai sama da haka ma a fagen goyon baya da taimakon gwagwarmaya da ‘yan gwagwarmaya a duk inda suke a kasashen Larabawa.

Ina taya tashar Al-Manar, wannan tasha ta gwagwarmaya, murnar wannan nasara ta ‘yanto yankunan da “Isra’ila” ta mamaye. Ina taya Labanon da dukkanin ‘yan gwagwarmayar Labanon murnar wannan nasarar.