A+ R A-
07 August 2020

Hirar Jagora Imam Khamenei Bayan Sallamarsa Daga Asibiti

Shimfida: Abin da ke biye fassarar hirar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi da dan jaridar gidan radiyo da talabijin na Iran ne a ranar Litinin 15, Satumba, 2014, a hanyarsa ta komawa gida bayan sallamarsa daga asibiti.

 

Dan Jarida: Salamun Alaikum.

Jagora: Salamun alaikum wa rahmatullah.

Dan Jarida: Godiya ta tabbata ga Allah, bayan mako guda da aikin tiyata, a halin yanzu ga shi kana shirin barin asibiti. Al’ummarmu da sauran al’ummomin kasashen musulmi da masoyanka a duk fadin duniya, za su so jin yanayin jikinka da kuma ranakun karshe-karshen na zamanka a asibiti.

Jagora: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Alhamdu lillahi an gudanar da tiyatar da dukkanin ayyukan share fagen hakan da kuma abubuwan da suka biyo baya cikin mafi kyawun yanayi. A zahiri dai ga shi zan koma gida cikin koshin lafiya. Jiki na dai lafiya, to amma zuciya da ruhina, cike suke da nauyin irin gagarumar so da kauna da tausayawar da aka nuna min tsawon wannan lokaci. A hakikanin gaskiya kafadar mutum ta yi nauyin gaske saboda irin wannan kaunar da mutane – bangarori daban-daban na mutane – suka nuna min. Babu wata rana da za ta gushe, ba tare da daruruwa ko kuma ma dubban sakonnin nuna kauna, tamkar ruwan saman da ke sake raya zuciyar duk wani matacce ko kuma wata kasa da ta bushe ba, sun iso gare ni ba. (Wadannan sakonni dai sun fito ne daga wajen mutane daban-daban); kama daga malamai masu girma, maraja’ai masu girma, jami’an gwamnati, manyan daraktocin kasa, mutane daga bangarori daban-daban. Irin kaunar da suka nuna min ta sa ni jin nauyinsu sosai.

Baya ga mutanen kasar mu, sauran al’ummomi ma – wanda na sha fadin cewa al’ummar Iran suna da wani matsayi mai girma wanda ya kebance su, babu wata kasa ko wani tsari da muka sani wanda yake da irin wannan tushe na kauna da alaka ta soyayya da akida da imani da sauran al’ummomi, amma mu muna da hakan – lalle sun nuna min irin wannan kaunar cikin ‘yan kwanakin nan.

Ala kulli hal, lalle na sami sauki, a bangaren ruhi ma alhamdu lillahi ina cikin nishadi, sai dai ina jin nauyin irin wannan so da kauna da aka nuna min tsawon wannan mako guda daga bangarori daban-daban, daga kungiyoyi daban-daban – na daga ‘yan siyasa, daga bangarori daban-daban na al’umma, daga wajen masu ayyukan fasaha da ‘yan wasa. Wasu an nuna su a talabijin; wasu ninkin ba ninkiya ma ba a gansu ba. Dukkaninsu suka nuna min so da kauna, ko suka rubuto ko kuma aka watsa a kafafen watsa labarai na internet. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya saka musu gaba daya da alheri.

Amma dangane da batun likitoci da aikin likitanci; wani lamarin shi ne cewa lalle ina gode wa wadannan likitoci da dukkanin wadanda suke da hannu cikin lamarin maganin da aka min. To wannan dai wani nauyi ne na wajibi da babu kokwanto cikinsa; lalle sun gudanar da aikinsu da kyau sosai; to amma sama da godiyar, shi ne cewa lalle ni ina alfahari da wadannan likitoci na mu. Ina alfahari da cewa kasarmu mai girma Iran, a fagen aikin likitanci, ta kai wani matsayi da al’ummar Iran za su yi alfahari da hakan saboda irin yawan likitoci, malaman fida, da sauran nau’oi na likitoci na bangarori daban-daban, da malaman jiyya da ake da su. Lalle wajibi ne mu yi alfahari da cewa alhamdu  lillahi muna da irin wannan gagarumin arzikin; gagarumin arziki na mutane a daya daga cikin mafi muhimmancin bangarori na rayuwar mutane wanda shi ne bangaren kiwon lafiya. Na ga irin yadda suke jin cewa lalle akwai wani nauyi a wuyansu da wajibi ne su sauke shi, haka nan kuma ga irin ilimi da kwarewar da suke da ita cikin ayyukansu. Lalle da man na san hakan, wato a koda yaushe wannan ita ce mahanga ta dangane da bangaren likitoci da kiwon lafiya; to amma a lokacin da mutum ya sami kansa a karkashin kulawarsu, sannan ya ga irin yanayin aikinsu, to a nan ne mutum zai kara samun tabbaci da sakankancewa. Mutum zai ji a jikinsa cewa lalle muna da gagarumin arziki na kasantuwar wadannan likitoci masu girman. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya saka musu da alheri.

Na’am, kamar yadda na fadi godiyarmu gare su ba za ta takaita kawai da wadannan kalmomi biyu zuwa uku ba ne. Na gaya wa Dakta (Ali Ridha) Marandi – wanda shi ne ya dauki nauyin jagorantar tawagar likitocin da suka yi min aiki; kamar yadda ya saba nuna mana kauna – na gaya masa cewa ya isar da sakon godiya ta, ta duk hanyar da ya ga ta dace ga wadannan likitoci abin kauna.

To yanzu kuma bari in ce wani abu kan wani abin da bai shafi batun zaman asibiti ba, wanda shi ne kuwa cewa cikin ‘yan kwanakin nan – wato kwanaki biyu zuwa uku na baya-bayan nan – na ji dadi da farin ciki. Wannan farin cikin kuwa saboda maganganun Amurkawa ne dangane da kungiyar Da’ish (ISIS) da kuma fada da ita; maganganu ne na holoko da wasa da hankali don cimma wata manufa kawai. Daga cikin abubuwan da suka faranta min rai shi ne yadda na ga sakataren wajen Amurka, haka nan ita ma wannan yarinyar – wato kakakinsu – a fili suke fadin cewa ba za mu gayyaci Iran cikin hadin gwiwan fada da Da’ish din ba! Da farko dai lalle wannan babban abin alfahari ne a gare mu a ce Amurka ta yanke kauna sannan kuma ba ta so mu kasance cikin wani aiki da ya saba wa doka, wani aiki na kuskure da take son yi. Lalle wannan abin alfahari ne a gare mu, ba abin bakin ciki ba ne.

Na biyu na ga cewa dukkaninsu karya suke yi. Saboda tun a ranar farko da wannan batu na Da’ish ya kunno kai a kasar Iraki, Amurkawa ta hanyar jakadansu da ke Iraki, ya bukaci jakadanmu da ke Irakin cewa ku zo mu zauna mu hada kai dangane da batun Da’ish. Jakadan na mu ya isar mana da wannan magana; wasu daga cikin jami’anmu ma dai ba sa adawa da hakan; ni ne na ki amincewa; don kuwa ba za mu hada kai da Amurka cikin wannan lamarin ba. Saboda hannayensu dumu-dumu suke (cikin wannan lamarin), ta ya ya za mu zo mu hada kai da mutumin da hannunsa a gurbace yake, sannan niyyarsu ma gurbatacciya ce? Daga baya kuma shi kansa  wannan ministan harkokin waje na Amurka (John Kerry), wanda ya fito gaban duniya yana fadin cewa: “Ba za mu gayyaci Iran ba”, shi da kansa ya bukaci Dakta Zarif (ministan harkokin wajen Iran) da cewa ku zo mu hada kai cikin wannan lamarin; Dakta Zarif ya yi watsi da maganar. Mataimakiyarsa ma – wacce wata mace ce, kun san ta – ta bukaci malam Arakchi (mataimakin ministan harkokin wajen Iran) a tattaunawar da suke yi, ta ce masa ku zo mu yi aiki tare. Shi ma ya yi watsi da hakan. Bayan da suka yi watsi da wannan maganar sannan mu ma a fili muka fadi cewa ba za mu hada kai da su cikin wannan lamarin ba, to sai ga shi a halin yanzu suna cewa ba za mu shigo da Iran cikin wannan lamarin ba.

Kafin wannan lokacin sun taba hada hadin gwiwan kasashe a kan kasar Siriya – sun ta tada jijiyoyin wuya a duniya inda suka sami damar tattaro kasashe talatin, arba’in zuwa hamsin – amma babu wani abin da suka iya yi a Siriyan; haka lamarin zai kasance dangane da Iraki ma. Ba da gaske suke ba. Abin da aka yi a Iraki da kuma karya kashin bayan kungiyar Da’ish a Irakin, ba Amurkawa ne suka yi hakan ba. Su kansu sun sani, haka nan su ma ‘yan Da’ish din sun sani, su ma mutanen Iraki a fili sun sani. Sun san cewa aikin mutanen Iraki ne, aikin sojojin Iraki ne, aiki ne na mutane, wadanda suka fahimci yadda za su yi fada da Da’ish. Sun yi fadar kuma sun musu bugun mummuke, a nan gaba ma za su sake yi musu. Lalle za ku gani.

Amurkawa suna son fakewa da hakan ne, wajen samun wata dama da za su aikata irin abin da suke aikatawa a Pakistan. Duk da kasantuwar tsayayyiyar gwamnati da kuma sojoji masu karfi a Pakistan – don kuwa sojojin Pakistan sojoji ne masu karfi – amma ba tare da izini ba suke shiga kasar su yi ruwan bama-bamai a duk inda suke so. Irin hakan ne suke son yi a Iraki da Siriya. To amma ya kamata su san cewa idan har suka aikata hakan, to kuwa za su fuskanci irin matsalolin da suka fuskanta shekaru goman da suka gabata kan lamarin kasar Iraki.

Gaskiyar lamarin shi ne jin wannan lamarin, shi din ma a kan gadon asibiti, ya faranta min rai.

Dan Jarida: Ina godiya. Tsarkakan zukatan miliyoyin mutane a koda yaushe suna tare da kai da kuma yi maka addu’oin fatan alheri.

Jagora: Na gode

Dan Jarida: Muna bukatar addu’oinku.

Jagora: Insha Allah. Allah ya kasance tare da ku.