A+ R A-
31 October 2020

Cikakken Jawabin Jagora Imam Khamenei Yayin Bikin Shekaru 31 Da Rasuwar Imam Khumaini (r.a)

Abin da ke biye fassarar jawabin da jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi ne a ranar 3 ga watan Yunin 2020 don tunawa da shekaru 31 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a).

--------

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu kuma Annabinmu Abul Ƙasim al-Mustafa Muhammad tare da Alayensa tsarkaka Ma'asumai musamman Wanzajjen Allah a bayan ƙasa.

A yau ana gabatar da bikin tunawa da marigayi Imam Khumaini da wani yanayi ba irin wanda aka saba gabatarwa ba. Yadda aka gudanar da biki ba shi ya ke da muhimmanci ba; asalin lamari kana kuma abu mai muhimmanci shi ne kalaman marigayi Imam waɗanda ƙasarmu take buƙararsu a yau da kuma a nan gaba. Shekaru bayan rasuwa ta zahiri da kuma rashinsa na zahiri, mu a wajen mu har yanzu Imam yana raye tare da mu kuma wajibi ne ya ci gaba da zama tare da mu, don kuwa lalle muna amfanuwa da kasantuwarsa da ruhinsa da tunaninsa da kuma shiryarwarsa.

A yau ɗin nan ina so ne in yi magana ne kan ɗaya daga cikin siffofi masu muhimmanci da Imaminmu mai girma ya keɓanta da su; duk kuwa da cewa shi ɗin nan wani mutum ne ma'abocin ɓangarori da kuma fitattun siffofi masu yawa da ya keɓanta da su. Waɗannan siffofin da a yau za mu yi magana kansu suna daga cikin siffofi mafiya muhimmanci da Imam ya keɓanta da su, su ne kuwa ruhin samar da sauyi da kuma son samar da sauyin da Imam yake da su. Imam a ruhance ya kasance mutum mai son sauyi kana kuma ma'abocin sauyi da samar da shi. Dangane da batun samar da sauyi, rawar da ya taka ba kawai rawa ce ta malami kana mai karantarwa kawai ba; (rawar da ya taka) wata rawa ce ta wani kwamandan yaƙi a yayin wani hari na soji kana kuma wani jagora da dukkanin ma'anar kalmar. A zamaninsa ya samar da mafi girman sauyi a fagage daban-daban masu yawan gaske, wanda a yau zan yi ishara da wasu daga cikinsu.

Da farko tsawon lokacin wannan ruhi na neman kawo sauyi ya kasance tare da wannan babban bawan Allah; ba wai wani abu ne da ya bayyana a tattare da shi a farko-farkon wannan yunƙuri na Musulunci a shekarar 1341 (1962) ba. A'a, shi ɗin nan tun lokacin samartakarsa ya kasance mutum ne mai son kawo sauyi, alamar hakan kuwa shi ne abin da ya rubutu tun yana saurayi – tun yana kimanin shekaru 30 – a littafin marigayi Waziri Yazdi, wanda marigayi Waziri ya taɓa nuna min wannan rubutun wanda Imam ya rubuta da hannunsa; na gani kuma daga baya ma an buga kuma da dama sun gani. A wannan rubutun, ya ambaci ayar nan ta «قُل إِنَّما أَعِظُکُم بِواحِدَةٍ أَن تَقوموا لِلَّهِ مَثنىٰ وَفُرادىٰ» (Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! Wato ku tsayu domin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai) wacce take kiran mutane zuwa ga yunƙuri saboda Allah; ya kasance yana da irin wannan ruhin. Ya aiwatar da wannan ruhin a aikace, wanda kuma kamar yadda na faɗin ya haifar da sauyi. A aikace ya kasance a fagen sauyin ba wai kawai a magana da ba da umurni ba. Ya fara da samar da sauyi a tsakanin wasu gungun ɗaliban addini matasa a Ƙum – wanda a nan gaba zan yi ƙarin bayani kan hakan – har zuwa ga samar da gagarumin sauyi a tsakanin al'ummar Iran.

Wannan batu na Ƙum kuwa shi ne darasin Akhlaƙ (kyawawan halaye) da ya kasance yana karantarwa a can. Shekaru aru-aru kafin fara yunƙurinsa, baya ga darasin Fiƙihu da Usul, shekaru yayi yana karantar da Akhlaƙ a Ƙum. Koda ya ke mu a lokacin da muka je Ƙum, an daɗe da dakatar da waɗannan darussan, ba a yin su. Mutanen da suka shaidi waɗancan darussan suna faɗin cewa –sau ɗaya a kowane mako ya kasance yana ba da darasi a makarantar Fa'iziyya inda ɗalibai matasa su kan taru – yayin da yake magana, ya kan haifar da wani irin yanayi na sauyi a zukata. Mu ma da kanmu mun ga irin hakan a yayin darasinsa na Fiƙihu da Usul. Wato hatta a darussan Fiƙihu da Usul da yake bayarwa, a wasu lokuta ya kan yi magana kan kyawawan halaye, inda ɗalibai su kan fashe da kuka, lokacin da yake magana kan kyawawan halaye, ya kan zubar da hawaye. Haka maganganunsa su kan kasance masu tasiri da kuma haifar da sauyi da kuma ruhi na juyi. Wannan shi ne irin tafarkin Annabawa; Annabawa Allah a cikin dukkanin yunƙurinsu suna farawa ne da samar da sauyi na ruhi a tsakanin mutane. Abin da Amirul Muminina (a.s) yake faɗin na cewa: “Don su shiryar da su zuwa ga cika alƙawarin halittunSa, su sanar da su ni’imominSa…sannan su buɗe musu taskokin hikima da aka ɓoye” shi ne wannan. Wato “sannan su buɗe musu taskokin hikima da aka ɓoye” yana nufin suna farkar da waɗannan hikimomi da suke tattare da mutane da kuma shigar da su fagen motsi da yunƙuri da shiryar da dukkanin matakai da ayyukan mutane. Shi ma Imam da haka ya faro. Duk da cewa ni ba zan iya ikirarin cewa tabbas yana gudanar da waɗannan darussa ne don saboda daga baya hakan yayi sanadiyyar haifar da wani gagarumin yunƙuri na siyasa ba; lalle ni ban san hakan ba. To amma abin da babu kokwanto cikinsa shi ne cewa ƙoƙarin motsarwa da kuma yunƙurar da zukata wani tafarki ne da Imam ya riƙa yayin darasinsa na Akhlaƙ. Daga nan ne ya faro har ya haifar da gagarumin sauyi a fage mai faɗi na al'umma; shin a lokacin gwagwarmayar ne – wanda zan yi ishara da kuma kawo misalan hakan a nan gaba – ko kuma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, lalle ya haifar da gagarumin sauyi a cikin al'ummar Iran.

Ya kamata ku san cewa waɗanda yake magana da su su ne al'ummar Iran. Kafin fara yunƙurin Imam, akwai wasu gwagwarmaya da ake yi a Iran, akwai yunƙuri da gwagwarmaya ta siyasa a Iran, shekaru aru-aru kenan akwai ƙungiyoyi daban-daban da suke gwagwarmaya, to sai dai fagen aikinsu taƙaitacce ne sosai, misali a kan wasu 'yan ɗaliban jami'a, misali ɗalibai 100 ko 150. Amma lamarin Imam bai taƙaita ga wata ƙungiya taƙaitacciya ko waɗansu jama'a ayyanannu ba ne; lamari ne da ya shafi dukkanin al'ummar Iran. Al'ummar tamkar teku ne, motsa teku kuwa ba aiki ne na kowane mutum ba. Ana iya motsar da wani ɗan ƙarami wajen wanka, to amma motsar da teku ba ƙaramin aiki ba ne. Al'umma wata teku ce, wannan shi ne abin da Imam yayi; ya samar da gagarumin sauyi.

Wani sauyin kuma shi ne sauyi cikin ruhin rashin motsi da kuma miƙa wuya na wata al'umma. A lokacin samartakanmu, a lokacin da wannan yunƙuri ya faro, al'ummar Iran wata al'umma ce wacce ba ta da kataɓus ko bakin magana cikin harkokinta. Mutane sun kasance sun miƙa wuya, marasa motsi, hatta dangane da rayuwarsu ta ɗaiɗaiku ma ba su kasance masu nuna wata damuwa ba. Amma irin wannan ruhi na yunƙurawa, shigowa cikin fage, neman haƙƙi, shi ɗin ma neman wasu abubuwa masu muhimmanci da kuma girma,to babu shi a cikin ɗabi'u da ayyukan al'ummarmu, Imam ne ya samar da hakan. Ya mayar da wannan al'umma maras motsi kana ma'abociyar miƙa kai zuwa ga wata al'umma mai neman haƙƙi. Irin wannan jawabai masu motsarwa na Imam, sun motsar da wannan al'umma da mai she ta ma'abociyar neman haƙƙi. Misalin hakan su ne abubuwan da suka faru a shekarar 1341 (1962) – wanda shi ne mafarin wannan yunƙurin – misalin hakan shi ne irin wannan gagarumin taron mutane a garuruwa daban-daban wanda daga ƙarshe dai ya samar da abin da ya faru a ranar 15 ga watan Khordad (5 Yunin 1962). A wannan ranar ta 15 ga watan Khordad duk kuwa da irin zubar da jinin mutane da wancan gwamnatin ta yi, amma ta gagara dakatar da wannan yunƙurin. Haka nan da sauran tarurrukan da mutane suka dinga yi tsawon lokaci har zuwa ƙarshen zamanin gwagwarmayar. Lalle wannan wani gagarumin sauyi ne da Imam ya samar.

Wani sauyin kuma shi ne sauyi cikin yadda mutane suke kallon kansu da kuma al'ummarsu; al'ummar Iran ta kasance tana kallon kanta da cewa ba a bakin komai ta ke ba. Wato babu wani da ma yake tunanin cewa wannan al'ummar za ta iya yin wani abu saɓanin abin da masu tinƙaho da ƙarfi na duniya suke so. Ba ma wai masu ƙarfi na duniya ba, hatta masu iko na cikin gida, kai hatta a kan wani jami'i, misali wani jami'in tsaro ko ɗān sanda, babu wanda ma yake tunanin hakan. Mutane sun kasance suna jin ƙasƙanci, ba sa jin suna da wani ƙarfi, amma Imam ya sauya hakan zuwa ga jin ɗaukaka, jin ƙarfi na dogaro da kai. Ya fitar da mutane daga jin cewa hukumar kama-karya wani lamari ne da babu yadda za a yi da ita – wanda haka lamarin ya ke a wancan lokacin. A wancan lokacin tunaninmu shi ne cewa tun da dai hukuma tana hannun wani mutum kuma yana da ƙarfi, don haka babu yadda za mu yi, wannan wani lamari ne da ya zama ruwan dare- amma Imam ya mayar da wannan al'ummar ta zamanto wata al'umma wacce ita ce take zaɓa wa kanta irin nau'in hukumar da take so. Daga cikin irin taken da mutane suke rerawa yayin juyin, da farko dai akwai cewa tsarin Musulunci suke so, hukuma irin ta Musulunci, daga nan kuma sai jamhuriyar Musulunci; mutane sun kasance su ne masu zaɓin makomarsu, su ne masu neman abin da suke so. Haka nan kuma a yayin zaɓuɓɓuka daban-daban da aka gudanar, su ne suke zaɓan shugaba, jami'an ɓangarori daban-daban na gwamnati; wato an sauya irin wancan yanayi na ƙasƙanci da mutane suka kasance a ciki zuwa ga wani yanayi na ɗaukaka da dogaro da kai.

Wani sauyin na daban kuma shi ne sauyi cikin abubuwan da mutane suke so. Wato abin da mutane suke iya buƙata daga wajen gwamnati ko kuma wani mai iko shi ne misali a yi musu kwaltar lungunsu ko kuma a yi musu titi, buƙatun na su ba su wuce haka ba; amma sai ga shi Imam ya mayar da su zuwa ga mutane masu neman 'yancin kansu, wato wasu abubuwa masu girma da muhimmanci. Ko kuma taken "Ba mu yarda da gabashi ba, haka nan ba mu yarda da yammaci ba" haka aka sauya buƙatun mutane. Wato an sauya yanayi daga buƙatar 'yan wasu abubuwa marasa ƙima zuwa ga wani lamari na siyasa, mai girma, na ɗan'adamtaka da ma na ƙasa da ƙasa.

Wani sauyin na daban da Imam ya kawo, shi ne irin kallon da ake yi wa addini. A wancan lokacin mutane suna kallon addini a matsayin wani abu da ke da alaƙa da lamurran da suka shafi lamurra na ɗaiɗaiku na ƙashin kan mutum, da suka shafi ibada, mafi tsanani dai shi ne suna ganinsa a matsayin wani lamari da ya shafi mutum a kan kansa ne. Kawai wani lamari ne da ke da alaƙa da salla da azumi da batutuwa na kuɗi da aure da saki; cikin waɗannan abubuwan. Suna taƙaita addini ga waɗannan abubuwa. Amma Imam ya gabatar da addini a matsayin wani lamari mai samar da tsari na siyasa da ci gaba da gina al'umma da ɗan'adam da makamantan hakan; ya sauya irin yadda mutane suke kallon addini.

Wani sauyin na daban kuma shi ne sauyi cikin yadda mutane suke kallon makomarsu. A wancan lokacin da wannan yunƙuri ya faro sannan Imam ya shigo cikin fage, duk da irin taken da wasu jam'iyyu da ƙungiyoyi suke rerawa – waɗanda 'yan wasu ayyanannu kuma ƙanana ne – ba a taɓa ganin abin da ya shafi makomar mutane a cikinsu ba. Wato mutane ba su da wani fata ko kuma wata makoma mai kyau da suke gani; Imam ya mayar da hakan zuwa ga wata mahanga irin ta Musulunci. Wato idan ka kalli al'ummar Iran a yau ɗin nan, wannan hannu mai albarka na Imam ne ya kai ta ga wannan mataki da take kai. Mutane suna neman kafa irin ci gaba na Musulunci; su samar da gagarumin tafarkin haɗin kai na Musulunci, su kafa al'umma musulma. Wannan ita ce mahangar mutane.

A fage mai faɗi kuma na ƙwarewa ma (an sami sauyi, wanda), shi ne sauyi a fagen tushen ilimi da masaniya; Imam ya samar da hakan. Wannan dai wani fage ne da ke buƙatar ƙwarewa, suna daga cikin lamurran makarantar Hauza da waɗanda suke da masaniyya a wannan fagen Fiƙihu da kuma fagen Usul da makamantan hakan. Imam ya shigo da Fiƙihu cikin fagen samar da tsari na siyasa; haka ya shigo da irin waɗannan abubuwan cikin fage na Fiƙihu. Duk kuwa da cewa batun Wilayatul Faƙih ya kasance a tsakankanin malaman Fiƙihu shekaru dubun da suka gabata kuma ana gabatar da shi, to amma da yake babu wannan fatan na cewa za a tabbatar da wannan batu na wilayatul faƙih, don haka ba a ma maganarsa. To amma haka Imam ya shigo da su cikin fage na Fiƙihu. Ya gabatar da hakan a makarantar hauza ta Najaf sannan ya gudanar da bahasi kan hakan; bahasi na ilimi mai zurfi inda ya janyo hankulan mutanen da suke da ra'ayi a wannan fagen. Ko kuma batun maslahar tsari (gwamnati) – wanda wannan maslahar na tsari shi ne maslaha da amfani na dukkanin al'umma, manufofi na ƙasa, babu wani abu da sama da hakan, Imam ya gabatar da hakan cikin Fiƙihu. Sanannen lamarin nan na Usul da Fiƙihu na 'tazahum' da 'Aham wa Muhim’ waɗanda ake amfani da su cikin ƙananan batutuwa da kuma batutuwan da suka shafi ɗaiɗaikun mutane, Imam ya shigo da su fage na al'umma, cikin fage na gudanar da ƙasa, ya gabatar da waɗannan batutuwa biyu cikin tsarin gudanarwa. Wato ya shigar da waɗānnan abubuwan cikin Fiƙihu wanda hakan ya haifar da wani gagarumin sauyi cikin Fiƙihu; ya buɗe hannayen fiƙhu ta yadda zai iya shiga cikin batutuwan daban-daban. A ra'ayina wajibi ne makarantun hauza su jinjina wa hakan sannan kuma su yi amfani da shi, su yi na'am da hakan. Tabbas irin wannan aikin da Imam yayi a fagen fiƙhu, wani lamari ne da ke bisa doka da kuma hanya; wato yayi daidai da fiƙhun da shi kansa Imam yake kira da Fiƙihun jawahiri, wato ba wata bidi'a ce cikin Fiƙihu ba. Wato wani ingantaccen amfani ne da sanannun tushe na Fiƙihu, wanda aka ajiye shi a hannun malaman Fiƙihu.

Wani misalin na daban na irin wannan sauyi a fagen addini da kuma batutuwa na addini, shi ne jajircewa kan bauta a daidai lokacin da ake kallon lamurra da mahanga ta zamani; wato Imam ya kasance wani faƙihi ne mai kallon lamurra da mahanga ta zamani, wani malami ne mai kallon lamurra da mahanga ta zamani, wato yana kallon lamurra da idanuwa na zamani a daidai lokacin da kuma mutum ne mai tsananin riƙo da tushe na abubuwan bautar Allah. A wancan lokacin akwai malaman da malamai ne masu kyakkyawan tunani suna kuma magana, kuma masanan addini ne sosai amma yanayin da ake ciki yayi musu tasiri, ba sa riƙo sosai da wasu abubuwa na koyarwar addini, na'am suna kula da waɗannan abubuwan a mu'amalarsu ta ƙashin kai, to amma ba sa ba da muhimmanci kan waɗannan al'amurra yayin wa'azinsu. Haka Imam ya zo, a tattare da irin wannan kallo na zamani da yake wa batutuwa na Fiƙihu da batutuwa na Musulunci da na addini da sauransu, haka nan ya tsaya ƙyam dangane da irin waɗannan batutuwa na bauta. Girmama abubuwa na bauta cikin hukunce-hukunce haka nan cikin bukukuwa na addini. Misali irin muhimmancin ga yake bayarwa batutuwan da suka shafi majalisin juyayi da makamantan hakan, dukkanin waɗannan abubuwa ne da suke nuni da riƙonsa ga abubuwa na addini.

Wani fagen kuma da ya samar da sauyin shi ne sauyi cikin kallon da ake yi wa matasa. Lalle shi ɗin nan yana girmama tunani da kuma ayyukan matasa; lalle wannan ma wani sauyi ne mai girma. Misali ku ɗauki cibiyar dakarun kare juyin juya halin Musulunci da aka kafa; ya amince da shugabancin matasa 'yan shekaru ashirin da wani abu a kan wannan cibiyar, wato wasu matasa ne waɗanda mafi yawan shekarun su shi ne talatin; su ne suke jagorantar dakarun kare juyin juya halin Musulunci, su ne kwamandojin dakarun, su ne dai waɗannan matasan da aka ba su nauyin gudanar da waɗannan manyan ayyuka. A fagage na daban ma haka lamarin ya kasance; a fagen shari'a da sauran wajaje na daban ma ya kasance ya yarda da matasa. Ya kasance yana ba su ayyuka, ya kasance mai yarda da kuma amincewa da ayyukan matasa.

Sai dai kuma a daidai lokacin ba ya kore irin dama da kuma ƙwarewar da waɗanda ba matasa ba suke da su. A halin yanzu da muke yawan nanata batun girmama irin ƙarfi da ƙwarewar matasa, wasu suna tunanin hakan yana nufin a kawar da tsoffi daga fage ne. A'a, wannan ba ita ce mahangar Imam ba. Ya kasance yana dogaro da matasa a matsayin su na wata taska ga tsarin nan, a matsayinsu na wata dukiya ga tsarin nan, haka nan kuma ya kasance mai girmama da kuma dogaro da ƙarfin da waɗanda ba matasa ba suke da shi. Ga misali a daidai lokacin da ya naɗa ni – wanda a lokacin dai ban tsufa sosai ba – a matsayin limamin juma'ar Tehran, a daidai wannan lokacin kuma ya naɗa marigayi shahid Ashrafi ɗan shekaru 80 a duniya a matsayin limamin juma'ar Kermanshah ko kuma marigayi Dastgaib ko kuma sauran shahidan mehrab; waɗanda dukkaninsu mutane ne 'yan shekaru sittin zuwa saba'in. Ko kuma a cikin sojoji; a misali a cikin dakarun kare juyin juya halin Musulunci, ya sanya matasa, a ɓangaren sojoji kuma ya sanya irin su Shahid Fallahi ko kuma marigayi Zahirnejad waɗanda mutane ne 'yan shekaru sittin zuwa sama. Lamarin ba shi ne cewa a yayin da muka ce a dogara da matasa, shi kenan sai a fitar da dukkanin waɗanda ba matasa daga fage, ko kuma a cibiyar agaji inda ya naɗa marigayi Asghar Auladi wanda ba matashi ne sosai ba.

Don haka da muka ce ya kasance yana dogaro da matasa – wanda a yau ma wannan shi ne imanin da muke da shi cewa wajibi ne a dogara da matasa, wajibi ne a yi amfani da matasa wajen ciyar da ƙasa gaba, wanda a nan gaba zan yi magana kan hakan – hakan da ma'anar cewa su ɗin nan wata taska ce, wata dukiya ce ga ƙasa wanda wajibi ne a amfana da wannan dukiyar; amma ma'anar hakan ba ita ce cewa kada a yi amfani da masu ƙwarewa waɗanda ba matasa ba waɗanda su ma wata dukiya ce ga ƙasa.

A saboda haka, Imam ya samar da wannan sauyin, to amma wani sauyi mai muhimmanci na daban da ya samar wanda mai yiyuwa ya ɗara wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen muhimmanci shi ne mahanga da kuma kallon da ake yi wa masu tinƙaho da ƙarfi na duniya. A wancan lokacin babu wani da ke tunanin cewa wani zai iya faɗin wani abu saɓānin na Amurka, a yi wani abu saɓanin abin da Amurka take so. Amma Imam yayi aikin da su kansu shugabannin Amurkan suna faɗin cewa Khumaini ya ƙasƙantar da mu; lalle haka lamarin ya ke. Imam da waɗanda suke tare da shi da matasan da suke gudanar da ayyukansu ƙarƙashin umurnin Imam sun ƙasƙantar da masu tinƙaho da ƙarfi na duniya, su karya lagonsu da kuma fitar da su daga fage. Imam ya tabbatar wa mutane cewa ana iya tinƙarar masu tinƙaho da ƙarfi, za a iya yin nasara a kansu kuma a nan gaba ma hakan lamari ke nuni. Ku dai ga yadda makomar tsohuwar Tarayyar Sobiyeti ta kasance, irin halin da Amurka ma take ciki a halin yanzu da kuma irin abubuwan da kuke ganin suna faruwa a Amukan. A baya babu wanda yake tunanin faruwar hakan. Amma Imam tun a wancan lokacin ya sanya hakan cikin zukatan mutane da nuna musu cewa lalle su ɗin nan za a iya yin nasara a kansu.

Toh, abu mai muhimmanci shi ne cewa marigayi Imam duk da irin waɗannan sauyi masu girma da ya kawo, wanda a haƙiƙanin gaskiya shi ya kawo wannan sauyin, to amma shi yana ganin hakan cewa daga Allah ne; ba ya taɓa jingina hakan ga kansa, yana ganin hakan daga Allah ne. Shi kansa wannan sauyi na ruhi da ya haifar cikin matasa – wanda an rubuta shi cikin littafin nan na Sahifeye Imam, ku duba ku gani a cikin jawabansa ya sha bayyana mamakinsa, wato abin mamaki ne a gare shi; shi kansa ne ya aikata hakan,  amma yana ganin hakan da cewa wani aiki ne na Allah. Tabbas haka lamarin yake cewa daga Allah ne, Babu wani ƙarfi ko wata dabara in ba daga Allah Maɗaukaki ba. Lalle Imam daga tsakiyar zuciyarsa ya yi imani da wannan ayar da take cewa "Kuma ba ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa". Lalle ya kasance mai ba da muhimmanci ga irin wannan yunƙuri da kuma sauyi na matasa, ya kasance mai mamakin wannan lamari. A wani wajen yana faɗin cewa irin wannan sauyi da ya faru a zukatan matasa ya fi nasarar da aka samu a kan ɗagutu. Don kuwa nasara a kan gwamnatin ɗagutu, nasara ce a kan ɗāgutun, amma wannan sauyin da aka samu a kan matasa wata nasara ce a kan Shaiɗan kuma Shaiɗan ya ɗara dagutu. Wato haka yake kallon lamarin. Wannan shi ne dangane da abin da na faɗi.

A saboda haka Imam ya kasance ma'abocin sauyi ne. Wannan bahasin da muke yi, ba wai da nufin mu ƙara samun masaniya dangane da Imam ba ne – duk da cewa shi kansa hakan yana da nasa muhimmancin – muna yin hakan ne don mu ɗau darasi; wajibi ne mu ɗau darasi daga Imam. Kowace al'umma rayayyiya tana buƙatar sauyi; mu ɗin nan a yau muna buƙatar sauyi a ɓangarori daban-daban. To sai dai ina son in sanar da ku cewa bayan rasuwar Imam, ƙasar nan ba ta tsaya waje guda da kuma yin watsi da sauyi ba. Alhamdu lillahi al'ummar Iran ta ci gaba da riƙo da wannan tafarki na sauyi na Imam kuma ta samu ci gaba. Lalle mun sami sauiyi a fagage daban-daban sannan kuma mun yi ƙarfi sama da yadda muka kasance a baya, a wasu fagagen ma mun ɗara yadda muka kasance a baya sosai; akwai waɗannan fagagen. Shi kansa irin sauyi da ci gaba na ilimi da muka samu ba ƙaramin abu ba ne, lamari ne mai muhimmancin gaske.

A ɓangaren ilimi, a wancan lokacin yanayin mu ba wani yanayi ne na a zo a gani ba. A yau a duniya ana maganarmu a matsayin waɗanda suke gaba-gaba a fagen yunƙuri na ilimi. Ko kuma a fagen kariya; wanda a yau ana iya cewa ƙarfin da muke da shi na kariya ya kusan kai wa ga matsayin zama gagarbadau. Wannan wani lamari ne mai muhimmancin gaske da muka samu. Ko kuma a fagen siyasa wanda wani fage ne na ɗāukaka ga wannan ƙasar ta mu a duniya. A yau ana ganin Jamhuriyar Musulunci a matsayin wata ƙasa mai ƙarfi a duniya. Dukkanin waɗānnan wasu sauyi da ci gaba ne da suka faru waɗānda ana iya ganinsu.

Cikin waɗannan shekaru talatin ɗin ba a dakatar da irin wannan sauyi da Imam ya kawo ba, an ci gaba da yi. A wasu fagagen ma an gina wasu tushe na sauyi da ci gaba sosai, to sai dai har yanzu ba mu kai ga ƙoluluwar da ake son kai wa ba. An samu ci gaban amma dai ba su wadatar ba. Abin da na ke son faɗi shi ne cewa akwai wasu wajajen da ba mu samu ci gaba ba, akwai wasu wurin da wataƙila mun ci baya, wannan kuwa wani abin baƙin ciki ne kuma ba abin a yarda da shi ba ne wanda kuma hakan ya saɓa wa yanayin juyin. Ci gaba da kiyaye juyin juya hali yana cikin ci gaba da samar da sauyi da ci gaba ne; sauyi yana nufin tashi da wani yanayi zuwa ga wani yanayi da ya fi wanda muke kai, wato wani ci gaba, wani yunƙuri mai girma a fagage daban-daban. Lalle muna buƙatar hakan; akwai wasu fagagen da lalle ba mu kai ga hakan ba.

Kishiyar juyin juya halin shi ne koma baya. Da dama daga cikin juyin juya hali na duniya sun fuskanci matsalar koma baya; wato bayan shekaru biyar, goma, sha biyar da nasarar juyin, sakamakon rashin kulawarsu, sai suka fuskanci matsalar koma baya. Don haka wannan koma bayan ita ce kishiyar juyin juya hali. Dukkanin biyun, wato ci gaba irin na juyi da kuma ci gaba da ma'anar koma bayansa – duk suna da alaƙa da iradar mutane ne. Idan har mutane suka yunƙura yadda ya dace, to kuwa za su ci gaba da kyau. Idan kuwa suka yunƙura bisa kuskure to za su sami koma baya, wanda Alƙur'ani mai girma yayi ishara da dukkanin biyu. A cikin suratur Ra'ad yana cewa: "Lalle ne Allah ba Ya canza abin da ke ga mutane har sai sun canza abin da ke ga zukatansu", wanda yanayin ayar tana nuni da ɓangare mai kyau ne, wato a lokacin da kuka samar da wani sauyi mai kyau a tattare da ku, to Allah Maɗaukakin Sarki zai haifar muku da wani sauyi mai kyau. Aya ta biyu a cikin Suratul Anfal ne inda Ya ke cewa: "Wancan ne domin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda Ya ni'imtar da ita a kan wasu mutane ba face sun sake abin da yake ga rayukansu", wannan ɓangare ne mara kyau, ɓangare ne na ci baya ne. Wato idan Allah Ya ba wa wata al'umma wata ni'ima amma sai ba ta yi abin da ya dace ba, to Allah zai karɓe wannan ni'imar daga gare su. A cikin Dua Kumail kuna karanta cewa: Ya Allah Ka gafarta min zunubin da ke sauya ni'ima" wannan sauyin ni'imar yana nufin ƙwace ni'imar, wanda hakan ya samo asali ne daga irada. Wajibi ne mu yi taka tsantsan kada mu fuskanci wannan matsalar.

A saboda haka a wannan tsarin akwai wannan batun cewa lalle bayan rasuwar Imam an ci gaba da riƙo da wannan tafarki na ci gaba, to sai dai yanayin da abin ke tafiya bai wadatar ba. Lalle saboda dalilai daban-daban muna da ƙarfin ciyar da ƙasar nan da kuma wannan tsarin gaba a ɓangarori daban-daban. To sai dai akwai wasu fata da na ke da su a kaina da matasanmu da al'ummominmu da masananmu, wanda shi ne mu zamanto masu tunanin samar da sauyi da ci gaba a fagage daban da ake da buƙata.

To waɗanne ɓāngarori ne ake buƙatar waɗannan ci gaban? Shi kansa hakan wani bahasi ne na daban, wanda a nan gaba zan yi ishara da hakan. To amma akwai wasu abubuwa a ɓāngaren sauyi da ci gaba, waɗanda matuƙar muna son samar da sauyi na haƙiƙa to wajibi ne mu kula da su.

Batu na farko shi ne cewa neman sauyi ba lalle ya zama da ma'anar nuna rashin amincewa ba face dai da ma'anar: tabbatar da aƙidar neman kyautata abubuwa, to wannan shi ne neman sauyi. Wato kada a wadatu da abubuwan da ake da su. Hakan yana iya zama shi ne tushen sauyi. Koda yake mai yiyu ne tushen hakan ya zamanto nuna rashin amincewa da yanayin da ake ciki, to amma ba ko yaushe ne lamarin yake zama haka ba. A wasu wajaje masu yawa sauyi yana nufin kada mu ji mun wadata da abubuwan da muke da su. Mu ci gaba da neman kai wa ga mataki na sama. Ba lalle sai mun sha kashi a wani wajen kafin mu fara neman sauyi ba. A'a, akwai wani wajen da ba ma sai mun ji mun sha kashi ba.

A nan wani sakamakon na ke son nunawa? Abin da na ke son faɗin shi ne cewa hatta a wajajen da muka samu nasarori – misali a fagen ilimi – to bai kamata wani ya ce to shi kenan tun da dai mun sami cigaba don haka ba mu buƙatar wani abu a wannan fagen ba. A'a, bai kamata mu wadatu da abin da muke da shi ba, bai kamata mu wadatu da nasarorin da muka samu ba, wajibi ne mu ci gaba da ƙoƙari wajen ƙara samun ci gaba hatta a waɗannan fagagen da muka samu nasarar. A saboda haka sauyi da ci gaba yana nufi shauƙin ci gaba da kuma sauri cikin tafiyar da muke da kuma nesantar koma baya. Waɗannan su ne ma'anar sauyi da ci gaba, hatta a wajajen da ba mu da koke-koke. To wannan shi ne batu na farko.

Batu na biyu shi ne ingantaccen sauyi yana buƙatar ci gaba na tunani; wato duk wani yunƙuri wanda babu tunani da hangen nesa a cikinsa, to ba za a iya kiransa da sauyi ko ci gaba ba. Ba za a iya ɗaukar wasu yunƙuri waɗanda ba na a zo a gani ba a matsayin sauyi ba; sauyi yana buƙatar ƙarfafawa ta tunani. Ga misali ɗaya daga cikin batutuwan da wajibi ne a samar da sauyi a cikinsu shi ne batun tabbatar da adalci. Wajibi ne mu samar da sauyi a fagen tabbatar da adalci wanda wajibi ne hakan ya dogara da wani tushe na tunani mai ƙarfin gaske. Me muke buƙata a fagen tabbatar da adalci, to a nan ne za mu samar da sauyin. Wato wannan ƙarfafawa ta tunani ɗaya ne daga cikin abubuwan da muke buƙata, waɗanda su ne hukunce-hukunce na Musulunci da dokokin na Musulunci da ayoyin Alƙur'ani mai girma da kalaman Ahlulbaiti (a.s). Wajbi ne mu yi amfani da su sannan kuma bisa su ne za mu samar da sauyin.

Duk wani abin da Imam ya aiwatar a wannan fage na samar da sauyi, sun dogara ne da wannan yunƙuri na Musulunci da kuma koyarwa ta Musulunci; bisa wannan tushen Imam ya gudanar da ayyukansa. Matuƙar aka rasa wannan ƙarfafawa ta tunani, to wannan sauyi na mutum zai zama bisa kuskure, mai yiyuwa ma mutum ya sanya ƙafarsa inda ba ta dace ba. Wato ba zai samun damar tabbatuwa a kan wannan tafarkin ba.

Mutum ya kan tuno da wasu mutane. A wannan juyi na mu ma dai mu na da wasu mutane, waɗanda sun kasance magoya bayan wannan juyin, suna ƙaunarsa, to amma da yake tushen tunaninsu ba wani tushe ne mai ƙarfi ba, tushen imaninsu ba wani tushe ne mai ƙarfi da ya ginu bisa tushe na tunani da dalilai masu ƙarfi ba, bayan gushewar wani lokaci sannan kuma bayan sun ƙetare shekarun samartaka sai suka koma tamkar waɗancan mutanen da aka yi juyin saboda su. Wato juyin juya halin Musulunci ya yi waje rod da wasu mutane masu karkatacciyar tunani. A haƙiƙanin gaskiya wasu daga cikin matasan juyin, bayan sun shiga mataki na samartaka da kuma ƙetare matakai daban-daban na rayuwa, wasu sun kusa ko kuma wasu sun sauya sun koma da kuma zama kamar waɗancan mutanen waɗanda aka bar su a baya.

Wani batun na daban wanda ke da muhimmanci shi ne bai kamata a yi kuskuren fahimtar sauyi da zagwanyewar tunani ba. 'Yan lokuta kafin hukumar Pahlawi da kuma bayanta, wanda lamarin ya fi faruwa ne a lokacin hukumar Pahlawi, an shigo da wani lamari mai sunan sabuntawa, wanda suke bayyana hakan a matsayin wani sauyi cikin rayuwar al'ummar Iran. To wannan dai ba sauyi ba ne, wannan kawar da al'ummar Iran ne da kuma kawar musu da irin matsayi da mutumcin da suke da shi. Wato al'ummar Iran ta rasa irin wannan matsayi da kishi na addini, kishin ƙasa da kuma girma irin na tarihi da take da ita, a yayin wannan sabuntawar. Wannan sabuntawar wanda wani ɓangare na ta an yi shi ne a zamanin Pahlawi wani ɓangaren kuma a lokacin Ridha Khan aka aiwatar da ita ta hanyar goyon bayan wasu 'yan boko masu tunanin yammaci wanda Ridha Khan ya shigo da su da ba su goyon baya da taimako, a haƙiƙānin gaskiya an kawar da mutumcin al'ummar Iran ne, wato an cire wa al'ummar Iran irin wannan girma da mutumci da take da shi. Wannan shi ne zagwanyewa ce, wannan ba sauyi ba ne. Dole ne sauyi ya zamanto zuwa ga ci gaba ne, amma wannan ci baya ne. Idan har al'umma ta rasa irin wannan mutumci nata, ta rasa wannan matsayi na addini, to a haƙiƙanin gaskiya za a iya ƙirga hakan a matsayin wata mutuwa da koma baya ga wannan al'ummar.

Abin baƙin ciki haka lamarin ya faru ga ƙasar mu. A bahasi na ilimi, a bahasi na zamantakewa, a bahasi na jami'oi, lamarin ya kai matsayin da maganar wani masani ɗan ƙasashen yammaci ya zamanto tamkar wahayi. Idan ana bahasi aka ce ga abin da wani masanin yammaci ya faɗi toh shi kenan komai ya ƙare. Ma'anar hakan ita ce cewa mun rufe ƙofar tunani. A lokacin da lamari ya zama sai dai koyi, batun koyi da wasu ya shigo fage, mutum bai isa ya ce wani a fagen ilimi saɓanin na masanan yammaci ba, ma'anar hakan shi ne cewa a ajiye batun tunani gefe, wajibi ne a ajiye batun ijtihadi gefe, wanda hakan ita ce kishiyar wancan koyarwar ta annabawa da suka zo don su bayyanar da taskar hikima da aka bisne su cikin kwakwale. Lalle wannan kishiryar hakan ne. To wannan shi ma wani batun ne.

Wani batun kuma na daban shi ne cewa ba lalle ne sauyi ya zamanto wani lamari ne da za a same shi lokaci guda ba; sauyi a sannu a hankali yake samuwa, bai kamata a nuna rashin haƙuri ba. Matuƙar dai muka gano manufa da abin da muke so da kyau, sannan kuma muka yunƙura yadda ya dace, to ko da mun yi jinkiri wajen isa ga manufar hakan ba matsala ba ce. Abu mai muhimmancin dai shi ne mu kama hanya, mu yunƙura, kada mu nuna rashin haƙuri. Tunanin cewa wajibi ne mu sami komai lokaci guda, lalle ba haka lamarin yake ba.

Matsalar wannan sabuntarwar da hukumomin 'yan amshin shata suka samar mana da ita ita ce cewa ba ta da wani mai shiryarwa; wannan ɗaya ne daga cikin matsalolinta. Wajibi ne a yayin wannan sauyin da aka tsara za mu samu a sannu a hankali ya zamana akwai wani mai shiryarwar da hankalinmu ya kwanta da shi wanda zai dinga sanya ido kan hakan. Idan kuwa ba haka ba, to kuwa lamarin zai zama tamkar irin yanayin da muka kasance cikinsa ne a baya. To shi ma wannan wani batu ne.

Wani batun na daban kuma shi ne cewa bai kamata mu yi kuskuren fahimta da kuma haɗa sauyi da wasu 'yan ayyuka waɗanda ba na a zo a gani ba. Wasu daga cikin 'yan wasu ayyukan waɗanda ake gudanar da su cikin gaggawa, waɗannan ba sauyi ba ne. Wasu lokuta ana gudanar da irin waɗannan ayyukan ne don nuna kai kawai, lalle waɗannan ayyukan ba su da wata ƙima. Sauyi wani aiki ne mai girman gaske, aiki na asasi da wajibi ne hakan ta faru. Na'am sauri cikin aiki yana da muhimmanci, to amma akwai bambanci tsakanin sauri da kuma gaggawa. Toh, waɗannan dai wasu batutuwa ne da suka shafi sauyi da wajibi ne mu yi la'akari da su, wajibi ne al'ummar Iran musamman matasa su yi la'akari da su.

To tambaya a nan ita ce a wasu fagage ne ya zama wajibi a samar da waɗannan sauyin? A baya na faɗi cewa wannan dai wani bahasi ne mai tsawon gaske, wanda wajibi ne mu ayyana fagagen da muke da giɓi cikin, sai mu yi ƙoƙarin haifar da sauyi na haƙiƙa a cikinsu. To sai dai ya kamata ne mu tsara su. Ana iya kawo wasu misalan hakan: misali a fagen tattalin arziki sauyin zai kasance ne ta hanyar cewa za mu sami ƙarfin da za mu iya katse dogora da man fetur a cikin tattalin arzikinmu; wato za mu iya samar da tattalin arzikin da bai dogara da man fetur ba. Wannan wani sauyi ne da ma'anar kalmar. Ko kuma ku ɗauka a fagen kasafin kuɗi na gwamnati. Majalisar da gwamnati su cimma yarjejeniya ta yadda za a gudanar da ayyuka da shi gwarwadon aikin da za a yi, wato abin da ake kira da 'kasafin kuɗi na aikatau' koda yake a mafi yawan lokuta gwamnatoci su kan yi wannan ikirarin, duk kuwa da cewa ba hakan ba ne. Matuƙar aka tsara kasafin kuɗin ƙasa da kyau, to lalle za a iya samar da gagarumin sauyi cikin tattalin arzikin ƙasa. Ko kuma misali a fagen batutuwan da suka shafi ilimi da tarbiyya; a haƙiƙanin gaskiya muna buƙatar sauyi a wannan fagen. Sauyi a fagen ilimi da tarbiyya shi ne mu samar da wani irin koyarwa mai zurfi a jami'oi da makarantun sakandaren mu kai hatta ma a makarantun firamare, wasu irin ilimi masu amfani ba kawai na hadda ba; a dinga gabatar da darussa masu amfani.

Wasu daga cikin darussan da ake karantarwa a makarantunmu ko a jami'oinmu, ba su da wani amfani da wanda ake karantar da su tsawon rayuwarsa. Don kuwa ba ilimi ne ake kwarewa a kansu ba sannan masaniyar da ake ba shi ba wata masaniya ce da za a iya amfani da ita ba. Kamar wasu ilmummuka ne na gaba ɗaya waɗanda ko an koye su ma ba su da wata fa'ida. Wato a fagen ilimi da tarbiyya, matuƙar muna son samun sauyi na haƙiƙa, to dole ne mu samar da sauyi ta yadda da darussan da za a karantar za su zama masu amfani da fa'aida. Wannan tsarin da aka tsara saboda ɓangaren ilimi da tarbiyya, matuƙar aka yi aiki da shi, to zai magance wani ɓangare na wannan matsalar.

Ko kuma a fagen lamurra na zamantakewa, misali batun tabbatar da adalci ko kuma magance matsaloli irin su shaye-shaye; tabbas waɗannan matsaloli ne na zamantakewa da wajibi ne mu magance su. Ko kuma a ɓangaren matsalar iyali, wanda wajibi mu magance su. A halin yanzu labarai da ingantattun rahotanni suna zuwa mana da suke cewa ƙasar mu ta kama hanyar tsofa, wannan lamari ne mai tada hankali, labara ne mara kyau. Wannan yana daga cikin abubuwan da sakamakonsu za su bayyana ne a lokacin da babu yadda za a iya. Toh wajibi ne a magance hakan ta hanyar sauyi, wajibi ne a yi wani abu a wannan fagen.

To wani sharaɗi mai muhimmanci na samar da sauyi shi ne rashin tsoron maƙiya da kuma ƙiyayyarsu. Allah Yana gaya wa Annabinsa cewa: "Kana tsoron mutane, alhali kuwa Allah ne mafi cancantar ka ji tsoronsa", wato bai kamata ka ji tsoron mutane ba, bai kamata ka ji tsoron maganar wannan da wancan ba. Daga ƙarshe dai duk wani aiki mai kyau yana da masu adawa da shi. Ɗan adawa, zai yi adawa. A yau ɗin nan sakamakon samuwar kafafen watsa labarai na zamani, a mafi yawan lokuta nau'in adawar tana zama mai cutarwa. Matuƙar dai ana son aiwatar da wani aiki mai kyau da inganci, bai kamata a yi la'akari da su ba. Haka nan bai kamata a dinga la'akari da maƙiya 'yan waje ba ma. Don wani yunƙuri na ci gaba da za a gudanar a ƙasar nan, akwai wani sansani na maƙiya da a koda yaushe suna zaune suna tunanin yadda za su cutar ta dukkanin hanyoyi masu sauƙi da masu tsanani. Masu sauƙin su ne ta hanyar munanan farfaganda da baƙanta duk wani mataki mai muhimmanci, ingantacce wanda yayi daidai da hankali da za a ɗauka. Su dinga sanya alamun tambaya kansa ta hanyar irin ikon da suke da shi kan kafafen watsa labarai waɗanda suke hannun sahyoniyawa. Bai kamata a ji tsoron su ba. Wajibi ne a yunƙura. A ra'ayina hanyar cimma hakan ita ce matasa su shigo fage; don kuwa waɗanda ba sa tsoro da kuma la'akari da wani abu yayin da suke tafiya su ne matasan. Koda yake kasantuwar matasan da irin yadda na faɗi a baya ɗin nan, wato ta hanyar amfani da tunanin matasa da ruhin matasa da kuma jaruntakar da matasa suke nunawa yayin da suka yunƙura. Ba wai da ma'anar kore kasantuwar mutanen da ba matasa ba; sharaɗin hakan shi ne dai kada a yi hakan.

Abin farin cikin shi ne cewa a lokacin da ƙasar nan ta dogara da Allah, sakamakon hakan shi ne dai abin da a halin yanzu kuke gani. Ɗaya ɓangaren maƙiyan ita ce tsohuwar Tarayyar Sobiyeti, wacce ƙarshenta ya zo; ɗaya ɓangaren kuma ita ce Amurka, wanda a yau dai kuna ganin halin tsaka mai wuyan da Amurka take ciki. Abubuwan da a halin yanzu suke faruwa a garuruwa da jihohin Amurka, bayyanar wata haƙiƙa ce da a koda yaushe suke ɓoyewa. Waɗannan ba wani baƙon abu ba ne, bayyanar wata haƙiƙa ce kawai, wanda a halin yanzu take bayyanar da kanta. Haka lamarin yake. Ga misali a samu wani ɗan sanda cikin rashin tausayi, ya sanya gwuiwarsa a kan wuyan wani baƙin fata, ya ci gaba da danne shi da matse shi har ya mutu – yana roƙonsa, yana neman ɗauki amma haka wannan maras imanin ya ci gaba da danne shi – a gefe guda ga wasu 'yan sandan ma suna tsaye suna kallo babu wani abin da suka yi, to wannan dai ba wani sabon abu ba ne. Wannan ita ce ɗabi'ar Amurka. Wannan shi ne abin da ya zuwa yanzu Amurka take yi wa ƙasashen duniya. Haka ta yi wa Afghanistan, haka ta yi da Iraƙi, haka ta yi da Siriya, haka ta yi da da dama daga ƙasashen duniya ciki kuwa har da na baya da Vietnam. Wannan ita ce ɗabi'ar Amurka, wannan ita ce ɗabi'ar gwamnatin Amurka. A yau ga shi sun nuna kansu. Taken da a halin yanzu mutane suke rerawa na cewa: "Ku bari mu numfasa" ko kuma "Ba zan iya numfashi ba", wanda a halin yanzu ya zama taken Amurkawa a garuruwa da jihohi daban-daban na ƙasar, a haƙiƙanin gaskiya maganganu ne da suke cikin zukatan al'ummomin da Amurka take zalunta a ƙasashen su. Haka lamarin yake.

Ala kulli hal, cikin yardar Allah da tausayinsa, Amurkawa sun yi kunya da wulaƙanta sakamakon ayyukansu. Irin yadda suka gudanar da lamarin corona ɗin nan ya kunyata su a duniya kuma har yanzu suna cikin wannan jin kunyar, duk kuwa da cewa sun fuskanci wannan matsala ta coronan ne bayan wasu ƙasashe da dama sun fuskanta, wanda hakan ya ba su damar su amfanu da ƙwarewar da wasu suka samu kamar yadda suna da damar da za su yi shirin da ya kamata (na tinƙarar cutar) amma irin raunin shugabanci da ake da shi a ƙasar ya sa aka sami irin wannan adadi mai yawan gaske na waɗanda suka mutu wanda ya ninninka na sauran ƙasashe. Sun gagara jagorantar lamarin kuma ma ba za su iya ba; hakan kuwa saboda irin fasadin da ke cikin cibiyoyin gudanar na Amurkan ne. Wannan shi ne yanayin tafiyar da mutane, wannan ita ce yanayin mu'amalarsu da mutane a daidai lokacin da suke cika duniya da surutu. Suna kashe mutane cikin yanayin na rashin imani a fili, sannan kuma ko neman afuwa ba sa yi; amma suna ta surutu, suna maganar kare haƙƙoƙin bil'adama. Shi wannan baƙin fatan da aka kashe, daga dukkan alamu shi ba ɗan'adam ba ne, kuma ba shi da haƙƙi. Haka suke.

Ala kulli hal, a ra'ayina al'ummar Amurka – a wani lokaci a baya na taɓa faɗi, a yanzu ma zan sake faɗi – suna cikin kunya saboda irin waɗannan gwamnatoci na su. Lalle suna da haƙƙin su dinga jin kunya dangane da irin wannan gwamnati da a halin yanzu take mulkarsu. Su ma mutanen da – shin waɗanda suke cikin ƙasar mu ne, wato Iraniyawan da suke cikin ƙasar mu, ko kuma wasu Iraniyawan da suke waje – suke goyon bayan Amurka da kare ta, a ra'ayina su ɗin ma ina ga ba za su iya ɗaga kansu ba sakamakon irin wannan abin da ke faruwa a can ɗin.

Muna fatan insha Allah abubuwan da suke faruwa a duniya za su zamanto masu amfani ga al'ummar Iran, su ƙara irin ƙarfi da ɗaukakar da Jamhuriyar Musulunci take da shi. Muna roƙon Allah da Ya tayar da ruhin marigayi Imam mai tsarki, maɗaukakar shahidanmu da kuma shahidinmu mai girma na baya-bayan nan, shahid (Ƙasim) Sulaimani tare da waliyansa insha Allah.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah.