A+ R A-
13 July 2020

Jagora Ya Gana Da 'Yan Majalisar Kwararu Ta Jagoranci

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a yayin ganawar da ya yi a safiyar yau Litinin (7-3-2013) da shugaba da membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar Iran, ya yi karin haske dangane da yunkurin ci gaba na al'ummar Iran tsawon shekaru 34 da suka gabata da kuma irin kalubalen da suke gaba inda ya bayyana: riko da Musulunci, tsayayyiyar azama, dogaro da karfi na mutane da kuma karfafa ruhin fatan da ake da shi a matsayin lamurra masu muhimmanci sannan kuma masu lamunce ci gaba da tafiya a kan tafarkin ci gaba da kuma samun nasarori masu girma da kuma tsallake matsaloli da suka bijiro.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hangen nesa cikin batutuwa na gudanar da kasa da kuma manyan manufofin tsarin Musulunci a matsayin lamurra masu muhimmanci kuma na wajibi wajen ci gaba da tafiya a kan tafarkin isa ga manufofin da tsarin Musulunci ya shata su yana mai cewa: akwai ingantacciyar fahimta cikin dangane da yadda ake kallon manufofin da aka sa a gaba da kuma makiyan da ake da su, wanda ta hakan ne za a iya gano wahalhalu da matsalolin da za a iya fuskanta.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan da a ce ba a da irin wannan hangen nesan a lokacin gwagwarmaya, ko shakka babu da wannan gwagwarmayar ta sha kasha. To amma sakamakon imani da Allah, tsayin daka da kuma ruhin da ke cike da kyakkyawan fata ga makoma, haka marigayi Imam (r.a) ya tsaya kyam sannan kuma ya kai wannan gwagwarmayar zuwa ga nasara duk kuwa da matsaloli da wahalhalun da aka fuskanta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana yanayin da ake ciki a halin yanzu a matsayin yanayi da ya fi tsanani da wahala sama da lokutan da suka gabata don haka sai ya ce: A irin wannan yanayin wajibi ne a yi watsi da kallon hadarin kaji wa lamurra sannan kuma ta hanyar riko da Musulunci da kuma dogaro da mutane da ruhin da ke cike da fata, a ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki na ci gaba.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokari wajen kiyayewa da kuma karfafa ruhin kyakkyawan fata a tsakanin mutane musamman matasa a matsayin daya daga cikin nauyin da ke wuyan malamai inda ya ce wajibi ne a koda yaushe a ba wa wannan batu na kyakkyawan fata muhimmanci musamman bisa la'akari da alamu masu faranta rai da sanya kyakkyawan fata da ake da su da yawa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin nasarorin da al'ummar Iran suke ci gaba da samu a kullum a matsayin daya daga cikin alamun irin kyakkyawan fatan da ake da shi, daga nan sai ya ce: irin daukakar da ake da ita a halin yanzu, yadda tunani al'ummar Iran ya samu karbuwa a duniyar musulmi, yadda koyarwar Musulunci ya samu gindin zama cikin zukatan al'ummar Iran, ci gaban ilimi da fasaha da ake samu, bakin magana na siyasa sannan kuma a fagen kasa da kasa da tsarin Musulunci na Iran ya samu sannan kuma kokarin tabbatar da adalci a cikin kasa, dukkanin wadannan wasu nasarori ne da al'ummar Iran suka samu wadanda kafin nasarar juyin juya halin Musulunci ko kuma a farko-farkonsa ba ma za a yi tunanin samunsu ba.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce irin fushi da matsin lambar da makiya suke yi wa al'ummar Iran shi ne wata alama ce ta irin nasarar da al'ummar Iran din suka samu yana mai cewa: Idan da a ce gwamnatin Musulunci ta Iran ba ta samu wani ci gaba ba, to da makiya ba su yi irin wannan fushin da suka yi din ba.

A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana batun nukiliyar kasar Iran a matsayin daya daga cikin kalubalen da wannan tsari na Musulunci ya ke fuskanta sai dai kuma Jagoran ya ce lamarin nukiliya din dai ba lamari ne mai cutarwa ga al'ummar Iran ba, face dai wani lamari ne da zai amfane ta.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan zaman tattaunawa ta baya-bayan nan da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya shida (5+1) a kasar Kazakhstan, Jagoran cewa ya yi: A yayin wannan tattaunawar dai kasashen yammacin babu wani abin a zo a gani da suka yi da har za a iya cewa sun sassauto wasu abubuwan. Abin da suka yi shi ne sun dan amince da wani bangare dan kadan na hakkin al'ummar Iran.

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan kaurin sunan da kasashen yammaci suka yi wajen karya alkawarin da suka dauka, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne a jira zama na gaba don tabbatar da gaskiyar kasashen yammacin cikin maganganun da suke fadi.

Ayatullah Khamenei ya bayyana takunkumi a matsayin wani kalubalen da ake fuskanta, sannan kuma yayin da yake bayanin dalilin hakan cewa ya yi: A zahiri abin da suke fakewa da shi wajen sanya wadannan takunkumi shi ne batun nukiliya, amma babban dalilin wani abu ne da kasashen yammaci suka jima sun hakonsa.

Jagoran ya bayyana kokarin haifar da rikici da fada tsakanin mutane da gwamnatin Musulunci (ta Iran) a matsayin babbar manufar wannan takunkumin da makiya suke sanya wa Iran inda ya ce: Fatan da kasashen yammacin suke da shi, shi ne cewa ta hanyar matsa wa mutane lamba, za su sanya su yin bore wa wannan tsarin. To amma al'ummar Iran sun bada musu kasa a ido a ranar 22 ga watan Bahman (na irin gagarumar fitowar da mutane suka yi a bikin tunawa da zagayowar ranar da juyin juya halin Musulunci ya yi nasara).

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske inda ya ce: Kididdigar da masana suka gudanar na nuni da cewa irin fitowar da mutane suka yi a ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekarar ta dara ta shekarar da ta gabata.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin wannan fitowar da mutane suka yi sannan kuma cin farin ciki da annashuwa duk kuwa da matsalolin da suke fuskanta a matsayin mayar da martani ga wannan takunkumin da makiyan suke kiransa da takunkumi mai gurguntarwa.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da shugaban majalisar kwararrun Ayatullah Mahdawi Kani ya yi karin haske kan abubuwan da aka tattaunawa a yayin zaman majalisar na kwanaki biyu.

Shi ma a nasa bangaren Ayatullah Muhammad Yazdi na'ibin shugaban majalisar kwararrun ya gabatar da wani rahoto kan zaman majalisar da kuma mika godiyar ‘yan majalisar ga al'ummar Iran sakamakon kasantuwarsu a fagage daban-daban na nuna goyon baya ga wannan tsari na Musulunci musamman yayin jern gwanon ranar 22 ga watan Bahman

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook