A+ R A-
25 May 2020

Jagora Ya Fitar Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sayyid Mujtaba Musawi Lari

A yammacin yau Asabar (9-3-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyyar rasuwar babban malami, marubuci sannan kuma wakilin Jagoran a garin Lorestan, Hujjatul Islam wal Muslimin Hajj Sayyid Mujtaba Musawi Lari:

Abin da ke biye fassarar matanin wannan sako na Jagoran ne:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Cikin tsananin bakin ciki na sami labarin rasuwar babban malami kuma marubuci mujahidi, marigayi Hujjatul Islam wal muslimin Hajj Sayyid Mujtaba Musawi Lari.

A hakikanin gaskiya irin hidimar da wannan malami mai girma ya yi wajen yada koyarwar Musulunci da mazhabar Ahlulbaiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) a duk fadin duniya, wata hidima ce maras tamka a cikin shekarun baya-bayan nan. Dubban mutane masu adalci da kuma kaunar gaskiya ne suka sami shiriya da kuma isa ga gaskiya sakamakon rubuce-rubucensa da suke cike da ilimi da kuma hikima a dukkanin nahiyoyi biyar na duniya, sannan kuma suka fahimci Musulunci da kuma yin imani da shi.

Wannan malami mai tsoron Allah, ba tare da wani nuna kai, sannan shi kadai din sa ba tare da dogaro da wannan da wancan ba, ya sadaukar da dukkanin rayuwarsa a fagen wannan babban jihadi (kokari) da kuma yin himma wajen neman yardar Allah.

Ina isar da sakon ta'aziyyar rasuwar wannan malami mai tsarkin zuciya ga mutane Lorestan masu girma da lardin Fars sannan kuma ga dukkanin masoya da dalibai da kuma wadanda suka amfana da littafansa musamman iyalansa masu girma. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi masa rahama da gafara da kuma kara daukaka matsayinsa.

 

Sayyid Ali Khamenei

19, Esfand, 1391.

(9, Maris, 2013).

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook