A+ R A-
25 May 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Ba Wa Zakaran Gasar Olympic Kyautar Zobensa

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba wa daya daga cikin zakarun ‘yan wasan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da suka sami kambin zinare a gasar Olympics da aka gudanar a shekara ta 2012 a Ingila mai suna Behdad Salimi kyautar zoben da ke hannunsa.

Wannan lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin (11-3-2013) a wata ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi da ‘yan wasan Iran da suka yi rawar gani a wasanni daban-daban na kasa da kasa da suka hada da gasar Olympics da aka gudanar a shekarar bara don jinjina musu kan irin gagarumin aikin da suka yi.

Bayan jawabin da wasu ‘yan wasan suka yi ne da kuma jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi a lokacin ganawar, Jagoran ya shigo cikin mahalarta taron don tattaunawa da su kai tsaye inda a nan ne shi wannan dan wasan Behdad Salimi, zakaran zakarun gasar daga nauyi a gasar Olympics din ta bara da aka gudanar a Ingila, ya roki Jagoran da ya ba shi kyautar zoben da ke hannunsa inda nan take Jagora ya amince da wannan bukata tasa ya cire zoben da mika masa.

 

Ana Iya Ganin Cikakken Labarin Wannan Ganawar Ta Nan:

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook