A+ R A-
26 May 2020

Sakon Jagora Na Sabuwar Shekarar 1392 Hijira Shamsiyya

Shimfida: Abin da ke biye fassarar sakon sabuwar shekara ta hijira shamsiyya ta 1392 da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar ne a yau din nan 20 ga watan Maris, 2013 don taya al'ummar Iran da sauran al'ummomin da suke gudanar da wannan bikin na Norouz (sabuwar shekara) murna:

 

-------------------------------------------------

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

"Ya Mai sassauya zukata da idanuwa, Ya Mai jujjuya dare da rana, Ya Mai sauya karfi da yanayi, Ka sauya yanayinmu zuwa ga mafi kyawun yanayi".

Ya Ubangiji Allah, ka yi salati ga Abar kaunarka Shugabar matar duniya Fatima bint Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa. Ya Allah ka yi dadin tsira a gar eta ga mahaifinta da mijinta da 'ya'yanta.

"Ya Ubangiji Allah, Ka zamanto majibinci, garkuwa, shugaba, mataimaki, mai shiryarwa da kuma nuna hanya ga Waliyinka, Al-Hujjat dan Al-Hasan, tsira da amincinka su tabbata a gare shi da kuma iyayensa, a wannan lokacin da kuma dukkanin lokuta har ka tabbatar da shi doron kasarka yana mai maka biyayya da kuma tabbatar da shi na tsawon lokaci.

Ya Ubangiji Allah! Ka ba shi abubuwan da idanuwansa za su haskaka da su sannan kuma zuciyarsa za ta ji dadinsu cikin kansa da zuriyarsa da ‘yan Shi'ansa da wadanda suke karkashinsa, na kurkusa da shi da kuma dukkanin mabiyansa da kuma dukkanin mutanen duniya."

Ina taya dukkanin 'yan'uwanmu masu girma a duk fadin kasar nan, da kuma dukkanin Iraniyawa da suke fadin duniya, da kuma dukkanin al'ummomin da suke girmama (idin) Norouz, musamman dakaru masu sadaukarwa, iyalan shahidai da sojojin da suka sami raunuka, da kuma dukkanin mutanen wadanda suke hidima a kan tafarkin ci gaban wannan tsari da kuma wannan kasa ta mu mai girma, murnar wannan idin. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya sanya wannan rana da wannan farkon shekarar ta zama abar faranta rai da nishadi ga al'ummarmu da kuma dukkanin musulman duniya, sannan kuma ya ba mu dacewa wajen sauke nauyin da ke wuyanmu. Ina kiran al'ummarmu masu girma da su lura da cewa ranakun shahadar Fatima al-Zahra (a.s) sun fado cikin tsakiyar ranakun idin nan, don haka kiyayewa da kuma girmama wadannan ranaku wani lamari ne da ya zamanto wajibi a kan dukkaninmu.

Lokacin sauyi da shigowar sabuwar shekara, a hakikanin gaskiya, wani kan iyaka ne tsakanin karshen wani waje da kuma mafarin wani waje; wato karshen shekarar da ta gabata da kuma mafarin sabuwar shekara. Tabbas wajibi ne mu ba da himma kan abubuwan da ke gabanmu. Mu kalli sabuwar shekara, don mu shiryar da kanmu da kuma yin tsare-tsaren da suka dace. Duk da cewa duba baya da kuma abin da muka yi a baya zai kasance mai amfani a gare mu, don mu ga me muka yi, ya ya yunkurinmu ya kasance, mene ne sakamakon abubuwan da muka yi, sannan kuma mu dau darasi daga cikinsu.

Shekara ta 1391, tamkar sauran shekarun da suka gabata, shekara ce da abubuwa daban-daban suka faru; akwai abubuwa masu faranta rai, haka nan kuma da akwai masu sosa rai; mun sami nasarori, kamar yadda kuma muna da abubuwa na koma baya. Tsawon tarihi haka rayuwar dan'adam ta kasance; tana da kwane-kwane da kuma fadi tashi; abin da ke da muhimmanci shi ne mu yi kokari ficewa daga wadannan tuddan masu matsaloli, sannan mu isar da kanmu zuwa ga kololuwa ta ci gaba.

Abin da ya fito fili a shekara ta 1391 a fagen fadarmu da duniyar ma'abota girman kai shi ne kara kaimi da matsin lambar makiya a kan al'ummar Iran da kuma tsarin Jamhuriyar Musulunci. Koda yake zahirin lamarin, shi ne tsanantawar makiyar; amma badinin lamarin shi ne kwarewa da nasarorin da al'ummar Iran suka samu a fagage daban-daban. Makiyanmu sun yi kokarin cutar da bangarori daban-daban na kasar nan; bangaren da suka fi ba shi muhimmanci shi ne bangaren tattalin arziki da siyasa. A fagen tattalin arziki, a fili suke fadin cewa suna son su gurguntar da al'ummar Iran ne ta hanyar wadannan takunkumi (da suke sanyawa). To amma sun gaza wajen gurguntar da al'ummar Iran, don kuwa cikin yarda da kuma taimakon Ubangiji mun sami nasarori a bangarori daban-daban; wanda an yi wa al'ummar Iran karin bayani kansu, sannan kuma a nan gaba ma za a yi musu; ni ma idan har ina raye, a jawabin da zan yi a ranar daya ga watan Farbardin (gobe kenan), zan yi ishara da wadannan abubuwa a jumlatance.

Tabbas a fagen tattalin arziki an matsa wa mutane lamba, an haifar musu da matsaloli; musamman ma da yake wasu matsalolin daga cikin gida ne; an nuna gazawa da rikon sakainar kashi ga wasu batutuwa a cikin gida wanda hakan ya taimakawa makiya cimma manufar da suka tsara; to amma a yanayi na gaba daya, yunkurin da jami'an gwamnati da kuma jama'a suka yi, wani yunkuri ne zuwa ga ci gaba, wanda cikin yardar Allah a nan gaba za a ga sakamakon wannan yunkuri da aka yi.

A fagen siyasa ma, a bangare guda makiya sun ba da himma ne wajen sun mai da al'ummar Iran saniyar ware, a bangare guda kuma su sanya al'ummar Iran cikin shakku da kokwanto; su raunana irin himmar da suke da ita. To amma sabanin hakan ne ya faru; a hakikanin gaskiya kishiyar hakan ce ta faru. A fagen kokarin mai da al'ummar Iran saniyar ware, ba ma wai kawai sun gaza wajen takaita irin siyasarmu ta kasa da  kasa  da kuma wannan yankin ba ne, face ma dai mun sami nasarar gudanar da tarurruka irin su taron shugabannin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta duniya inda shugabani da manyan jami'an kasashe da yawan gaske suka zo nan Tehran sannan kuma akasin abin da makiyanmu suke so ne ya faru. Wato ba wai kawai ba a kaurace wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ne, face dai duniya tana ganin Jamhuriyar Musulunci da kuma kasar Musulunci ta Iran da idon girmamawa ne.

A fagen batutuwa na cikin gida kuwa, al'ummarmu masu girma a duk wajen da aka sami dama sannan da kuma bukatar a bayyanar da irin so da kaunar da ake da ita ta taso – a mafi yawan lokuta a ranar 22 ga watan Bahman na shekarar 1391 – lalle sun bayyanar da kansu da kuma shigowa cikin fage; ta yadda irin fitowar da suka yi ta fi ta shekarun da suka gabata yawa. Wani misalin kuma shi ne irin fitowar da mutanen lardin Khorasan ta arewa suka yi (don tarbar jagoran a lokacin da ya kai ziyara can) duk kuwa da wannan takunkumin da aka sanya inda suka bayyanar da irin so da kaunar da suke yi wa wannan tsari na Musulunci da kuma jami'an gwamnati da kuma masu yi musu hidima. Alhamdu lillahi, tsawon wannan shekarar an gudanar da ayyuka masu girma; an gudanar da ayyuka daban-daban a fagen ilimi, gina kasa, mutane da kuma al'umma sun yunkura ainun. Cikin yardar Allah an samar da hanyoyin ci gaba; shin a fagen tattalin arziki ne ko kuma a fagen siyasa, haka nan a sauran bangarori na rayuwa.

Sakamakon taimako na Ubangiji da kuma himmar al'ummar musulmi (ta Iran) an share fagen fata mai kyau cikin shekara ta 1392, cikin yardar Allah za ta zamanto shekara ce ta ci gaba da yunkuri da kuma samun kwarewa. Koda yake ba wai da ma'anar cewa za a kawo karshen kiyayyar makiya ba ne, face dai da ma'anar cewa irin shirin da al'ummar Iran suke da shi da kuma kasantuwarsu a fagage masu tasiri da kuma gina makoma za su karu cikin ikon Allah.

Tabbas abin da ke gabanmu a shekara ta 1392, lalle a mafi yawan bangarori zai zamanto ne a fagen tattalin arziki da siyasa. A fagen tattalin arziki wajibi ne a kara himma kan abubuwan da ake samarwa a cikin gida, kamar yadda hakan ya kasance shi ne taken shekarar da ta gabata. Tabbas an gudanar da ayyuka masu yawa; to amma karfafa samar da abubuwan da ake samarwa a cikin gida da kuma aiki tukuru da kuma goyon bayan ayyukan 'yan gida, wani shiri ne na tsawon lokaci; ba za a iya cimma shi cikin shekara guda ba. Abin farin cikin shi ne cewa a watanni shida na karshe na shekarar bara (1391) an amince da dokar karfafa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida sannan kuma an sanar da ita – wato a hakikanin gaskiya an share wannan hanyar – wanda a bisa wannan dokar majalisa da gwamnati za su iya tsara ayyuka, su fara wani yunkuri mai kyau sannan kuma cikin yardar Allah ta hanyar himma da aiki tukuru a samu ci gaba.

A fagen lamurran siyasa, babban aikin da ake da shi a wannan shekarar ta 1392 shi ne zaben shugaban kasa da za a gudanar; wanda a hakikanin gaskiya shi ne zai tsara irin siyasar gudanar da kasar nan cikin shekaru hudu masu zuwa. Mutane ta hanyar shigowarsu wannan fagen, insha Allahu, za su sami damar ciyar da kasar nan da kuma kansu gaba. Tabbas wajibi ne mutane su ba da himma da kuma aiki tukuru ba kama hannun yaro a fagen tattalin arziki, haka nan a fagen siyasa. Wajibi ne a shigo wannan fage cikin kumaji da azama, da gagarumar himma da kuma kyakkyawan fata, haka nan kuma da zuciyar da take cike da kyakkyawan fata da nishadi don a sami cimma manufofin da aka sa a gaba.

A saboda haka na sanya wa wannan shekara ta 1392 sunan "Shekarar Yunkuri Na Siyasa Da Karfafa Tattalin Arziki", sannan kuma muna fatan cikin yardar Allah, al'ummarmu masu girma da kuma jami'an gwamnati masu kishi, za su sami nasarar cimma manufar wannan yunkuri da hobbasa ta tattalin arziki da kuma siyasa.

Da fatan samun kulawa ta Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma addu'oin mai girma Imam Mahdi (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) sannan kuma gaisuwa da sallama ga ruhin marigayi Imam Kumaini da shahidai madaukaka.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Mun samo wannan labarin ne daga Shafin Jagora

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook