A+ R A-
29 February 2020

Jagora Imam Khamenei: Iran Za Ta Ruguza Tel Aviv Da Haifa Matukar 'Isra'ila Ta Kawo Mata Hari

A yammacin yau Alhamis, wadda ta yi daidai da ranar farko ta sabuwar shekarar 1392 hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan al'ummar garin Masshad da masu ziyarar haramin Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s) da ke garin inda ya gabatar da wani jawabi mai muhimmanci inda ya yi karin haske kan irin nasarorin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu cikin shekarar da ta gabata ta 1391 duk kuwa da irin kafar ungulun da makiya suka yi, batun tayin tattaunawa da Iran da jami'an Amurka suke gabatarwa, wajibcin gudanar da tsare-tsare da kuma kumaji na tattalin arziki don fada da takunkumin da makiya suke sanya wa al'ummar Iran, kamar yadda kuma yayi karin haske kan zaben shugaban kasar Iran da za a gudanar nan gaba da kuma kiran al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatansu yayin zaben.

A cikin jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake tayar al'ummar Iran murnar shigowar sabuwar shekara ta hijira shamsiyya yana mai bayyana wajibcin da ke cikin sake dubi cikin bangarorin da ake da karfi a cikinsu da kuma inda ake da rauni don a gudanar da tsare-tsaren da suka dace don ciyar da kasar Iran gaba. Jagoran ya bayyana cewar: Kamar yadda kowane mutum yake da bukatar dubi da kuma sanya ido a koda yaushe cikin lamurransa na kashin kansa, haka nan ake bukatar sanya ido da kuma dubi cikin lamurra da suka shafi don a dau darasi da kuma amfani da abin da aka koya don gobe.

Lamarin da Jagoran ya fara magana kansa shi ne batun takunkumin da gwamnatin Amurka ta sanya wa Iran da nufin gurguntar da al'ummar Iran kamar yadda jami'an kasar suke bayyana hakan a fili, inda ya ce: A irin wannan yanayi dake cike da kalubale, al'ummar Iran, sakamakon basira da sanin ya kamatansu bugu da kari kan karfin da suke da shi, sun sami nasarar mayar da wannan barazana zuwa ga wata dama ta samun nasarori. Jagoran ya ci gaba da cewa: idan har aka kalli irin wadannan nasarorin da Iran ta samu, to kuwa ko shakka babu ana iya cewa al'ummar Iran ce ta yi nasara a wannan fagen.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Irin nasarorin da al'ummar Iran suka samu a wannan yanayi, ya kai matsayin da hatta masana da 'yan siyasar kasashen duniya daban-daban ciki kuwa har da na kasashen da suke adawa da Iran sun jinjina wa al'ummar ta Iran.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan wasu mutane wadanda a koda yaushe suke bayyanar da rashin jin dadinsu dangane da irin nasarorin da al'ummar Iran suke samu kuwa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Irin wadannan mutane, wadanda su ne makiyan al'ummar Iran suna amfani da hanyoyi biyu ne wajen fada da irin wannan ci gaban da al'ummar Iran ta samu: Hanya ta farko dai ita ce ta hanyar yin kafar ungulu da kokarin hana irin wadannan ci gaban ta hanyar sanya takunkumi, barazana da kuma kokarin shagaltar da jami'an gwamnati, masana da kuma al'umma da wasu abubuwa na gefe marasa muhimmanci. Hanya ta biyu kuwa ita ce yada bakar farfaganda da nufin boye irin wadannan nasarorin da al'ummar Iran suka samu da kuma kanbama wasu 'yan matsaloli da ake da su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana shekarar 1391 da ta gabatar a matsayin shekarar da makiyan al'umma Iran suka fi shagaltar da kansu wajen kulla makirce-makirce wa al'ummar Iran inda ya ce: A fili sun da cewa manufarsu ita ce gurguntar da al'ummar Iran da kuma dunkufar da su. A saboda haka ne suke ganin matukar suka bari al'ummar Iran ta tsaya da kafafunta da kuma samun ci gaba, to kuwa mutumcinsu zai zube. Daga nan sai Jagoran ya gabatar da wasu tambayoyi guda biyu: Na farko: Ina ne asalin cibiyar kulla makirci ga al'ummar Iran? Na biyu kuma shin su wane ne asalin makiyan al'ummar Iran?

Yayin da ya ke amsa tambayar farko dai, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Asalin cibiyar kulla makirci ga al'ummar Iran dai ita ce Amurka. A yau bayan gushewar shekaru 34, daga an ambaci sunan makiyi, nan take kwakwalan al'ummar Iran su kan koma ne ga Amurka. Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an Amurka su yi tuntuni sosai kan wannan batun, da kuma tambayar kansu me ya sa al'ummar Iran suke kallonsu a duk lokacin da aka ambaci sunan makiyi?

Har ila yau kuma a ci gaba da magana kan makiyan al'ummar Iran din, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Baya ga Amurka, wacce ita ce babbar makiyar al'ummar Iran sannan kuma cibiyar kulla mata makirci, akwai kuma wasu makiyan, daga cikin su kuwa akwai lalatacciyar gwamnatin Ingila, duk da cewa ita gwamnatin Ingila ba ta da 'yancin kanta, 'yar amshin shatar Amurka ce. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ta da wata matsala da gwamnati da kuma al'ummar Faransa, to amma a cikin 'yan shekarun nan musamman tun daga lokacin gwamnatin Sarkozy, gwamnatin Faransar ta share fagen kiyayya da al'ummar Iran, wanda kuma har ya zuwa yanzu gwamnatin Faransar ta yanzu ma tana ci gaba da bin wannan siyasar.

Yayin da yake magana kan haramtacciyar kasar Isra'ila kuwa, Jagoran cewa ya yi: Haramtacciyar kasar Isra'ila 'yar fashin kasa, ba ta kai matsayin da za a sanya ta cikin sahun makiyan al'ummar Iran ba. Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan wasu barazanar da jami'an haramtacciyar kasar Isra'ilan suke na kawo wa Iran hari, Jagoran cewa ya yi: Matukar dai gigi ya debe su (suka kawo wa Iran hari), to kuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta rusa Tel Aviv Da Haifa da mai she su turbaya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A koda yaushe Amurkawa suna bayyana 'yan wadannan makiyan na al'ummar Iran a matsayin 'kasashen duniya', alhali kuwa kasashen duniya ba sa adawa da kuma kiyayya da al'ummar Iran da kuma kasar Musulunci ta Iran.

Har ila yau kuma a ci gaba da bayanin asalin makiyan al'ummar Iran na hakika, Jagoran ya yi karin haske kan irin makirce-makirce da kiyayyar da suka nuna wa al'ummar Iran tsawon shekarar barar (1391) inda ya ce: Sabanin nuna abokantaka ta zahiri da suke yi wa al'ummar Iran, tun daga farkon shekarar barar Amurkawan suka fara tsananta irin takunkumin da suka sanya wa Iran a bangaren mai da hada-hada ta bankuna, amma kuma suna kokari wajen ganin ba a dauke su a matsayin makiya ba, duk kuwa da irin wannan kiyayyar da suke nunawa.

Jagoran ya bayyana wannan siyasar ta Amurka a matsayin ci gaban irin wancar siyasar ta su ta sakin fuska a zahiri amma kuma da kokarin cutarwa ta bayan fage inda ya ce: Sabanin wannan yaudarar da suke kokarin yi, wadannan mutane suna ci gaba da gudanar da wata siyasa wacce suke fatan bayan wani lokaci za ta tilasta wa al'ummar Iran za ta mika wa bakar siyasarsu ta tursasawa kai. To amma sabanin hakan ne ya faru.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce ko shakka babu takunkumin da suka sanya wa Iran ya yi tasiri, sai dai kuma ya ce hakan ya samo asali ne daga wata siyasa ta kuskure da aka gudanar a Iran din da suka hada da dogaro da man fetur da aka yi. Don haka Jagoran ya kirayi gwamnatin kasar da ta sanya siyasar wadatuwa daga man fetur din cikin siyasarta ta tattalin arziki.

Bayan bayani kan irin kiyayyar da makiya suka nuna wa Iran a fagen tattalin arziki a shekarar da ta gabatan, daga nan kuma Jagoran ya yi karin haske kan makirce-makircen da makiyan suka kulla a fagen siyasa a shekarar barar. Jagoran ya ce: Daya daga cikin makirce-makircen da masu adawa da al'ummar Iran suka kulla a fagen siyasa shi ne kokarin mai da gwamnatin Musulunci ta Iran saniyar ware, to amma nasarar da Iran ta samu wajen shiryawa da kuma daukan bakuncin taron shugabannin kasashen 'yan ba ruwanmu inda shugabanni da manyan jami'an adadi mai yawan gaske na kasashen duniya suka halarta ya sanya wannan makirci na makiyan ya zamanto aikin Baban Giwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokarin sanya shakku cikin zukatan al'ummar Iran da kuma hada su fada da jami'an gwamnati a matsayin wani makircin da makiyan suka kulla a fagen siyasa inda ya ce: Fitowar da al'ummar Iran suka yi kwansu da kwarkwatansu a lokacin gangamin ranar 22 ga watan Bahman don tunawa da ranar da juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya samu nasara da kuma nuna goyon bayansu ga Musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci, yana a matsayin bada wa makiya kada a fuska ne.

Haka nan kuma Jagoran ya yi ishara da wasu kokarin da makiya suka yi wajen dagula lamurran tsaro da kuma kashe-kashen da suka yi a Iran cikin shekarar da ta gabatan a matsayin wani makircin na daban da suka yi.

Bayan dukkanin wadannan bayanai, daga nan kuma sai ya yi karin haske da kuma bayani kan irin ci gaban da Iran ta samu a shekarar da ta gabatan a fagagen ilimi, fasaha, kere-kere, tsaro da sauransu, inda ya ce ta hanyar irin wadannan ci gaban da aka samun, al'ummar Iran sun tabbatar wa duniya da cewa rashin dogaro da Amurka ba wai kawai ma ba ya kawo ci baya ba ne face ma dai yak an zama hanya ce ta samun ci gaba.

A wani bangare kuma na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ci gaba da tayin tattaunawa da Iran da Amurkawa suke gabatarwa ne inda ya ce: Tun da jimawa Amurkawa suke aiko mana da sako ta hanyoyi daban-daban da cewa suna son tattauna ta kai tsaye da Iran dangane da shirin nukiliyanta. To sa dai bisa ga abubuwan da suka faru a baya, lalle ba na ganin akwai wani abin da za a iya cimmawa. Don kuwa a cewar Jagoran: A mahangar Amurkawa, tattaunawa tana nufin tilasta wa bangaren da ake tattaunawa da shi din amincewa da abin da suke fadi ne. A saboda haka ne mu dai a koda yaushe muna ganin irin wannan tattaunawar a matsayin wani kokari ne na tilasta abin da suke so, alhali kuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika musu wuya ba.

Jagoran dai ya ce shi dai ba ya adawa da tattaunawa da Amurkan, sai dai kuma ya yi karin haske kan wasu abubuwa da wajibi ne a lura da su yayin wannan  tattaunawar.

Batu na farko da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da shi a wannan bangaren shi ne maganar Amurkawan na cewa a halin yanzu dai ba su da niyyar sauya gwamnatin kasar Iran. Dangane da wannan batun ne Jagoran ya ce: Mu dai babu wani lokacin da muka taba damuwa dangane da niyyar Amurkawan na sauya tsarin Jamhuriyar Musulunci a Iran. Don kuwa a wancan lokacin ma da kuke da wannan niyyar sannan kuma a fili kuke fadi, gun gagara yin wani abu sannan a nan gaba ma ba za ku iya ba.

Batu na biyu da Jagoran ya yi ishara da shi, shi ne maganar Amurkawan na cewa da gaske suke yi kan wannan tayi na tattaunawa na su, inda ya ce: Mu dai a lokuta daban-daban mun sha bayyana cewar ba ma nufin kera makaman nukiliyan, to amma Amurkawa suna fadin cewa mu dai ba mu yarda da gaskiyar wannan magana ta ku ba. To a irin wannan yanayi da wani dalili ne mu ma za mu gaskata maganganun da Amurkawan suke fadi dangane da batun tattaunawar.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Fahimtarmu dai ita ce cewa gabatar da batun tattaunawar wata dabara ce da Amurka ta kirkiro ta da nufin yaudarar al'ummomin duniya da kuma al'ummar Iran. Idan kuwa ba haka ba ne, to wajibi ne Amurkawan sun tabbatar da abin da suke fadi a aikace.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A wani lokaci sun ce wai wasu mutane daga wajen Jagoran al'ummar Iran sun tattaunawa da Amurka, alhali kuwa babu gaskiya cikin hakan, karya ce kawai tsagoronta. Ya zuwa yanzu babu wani mutum daga bangaren Jagora da ya tattauna da Amurka. Jagoran ya ce a kan wasu batutuwa ne wakilan gwamnatocin da suka gabata suka tattauna da Amurkawan, wanda a yayin wadancan tattaunawar ma an daure su da cewa wajibi ne su kiyaye abubuwan da Jagoran ba zai taba amincewa da su ba. A nan gaba ma wajibi ne su kiyaye hakan.

Wani batun kuma da Jagoran ya yi ishara da shi kan wannan batu na tattaunawa shi ne niyyar da Amurkawan suke da ita na nesantar isa ga sakamakon da kuma kawo karshen tattaunawar. Daga nan kuma sai ya gabatar da hanyar da yake ganin idan aka bi za a magance wannan matsala da ke tsakanin kasashen biyu yana mai cewa: Hanya guda kawai ta magance wannan matsala ita ce Amurkawan su kawo karshen kiyayyar da suke yi da al'ummar Iran. Jagoran ya ce shekaru 34 kenan Amurkan take gudanar da wannan siyasa ta kiyayya da al'ummar Iran sannan kuma suna shan kashi, inda ya ce idan har suka ci gaba da gudanar da wannan siyasar to za su ci gaba da shan kashin.

Batu na karshe da Jagoran ya yi magana kansa shi ne batun zaben shugaban kasar da za a gudanar nan gaba kadan inda ya kirayi al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatansu don ba wa marada kunya da kuma tabbatar da hakkinsu na zaban mutumin da zai dau nauyin gudanar da kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa, kamar yadda kuma ya kiraye su da su yi taka tsantsan daga makirce-makircen makiya wadanda za su yi kokarin ganin sun dagula lamurra yayin wannan zaben.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook