A+ R A-
29 February 2020

Jaddadawar Jagora Kan Sauya Siyasar Amurka Kafin Tattaunawa Da Iran

A yammacin ranar Alhamis (22-3-2013) wanda ya yi daidai da ranar farko ta sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ta 1392 Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan al'ummar Iran da suka taru a hubbaren Imam Ridha (a.s) da ke birnin Masshad inda ya gabatar da wani jawabi mai matukar muhimmanci da ya shafi lamurran cikin gida da kuma wajen kasar ta Iran.  

A yayin jawabin nasa,  Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya tabo lamurra da suka shafi takunkumin zaluncin da kasashen yammaci suka sanya wa al'ummar Iran, batun nukiliyan zaman lafiya na kasar, tayin tattaunawar da jami'an Amurka suke ci gaba da gabatar da shi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma barazanar da jami'an HKI suke ci gaba da yi na kawo wa Iran din hari.

Dangane da abin da ya shafi takunkumin kuwa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara ne da manufar Amurka da kawayenta na kara tsananta wannan takunkumin a shekarar da ta gabatan inda ya ce manufar hakan ita ce kamar yadda tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta bayyana ita ce dunkufar da kuma gurguntar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. To sai dai Jagoran ya ce, makiyan al'ummar Iran ba wai ma kawai ba su cimma wannan manufa da suka sa a gaba ba ne, face dai hakan ya sa share wa al'ummar Iran fagen bayyanar da irin kwarewar da suke da ita ne da kuma samar da yanayin dogaro da kansu a dukkanin fagage. Jagoran ya yi ishara da irin ci gaban da Iran ta samu a fagagen ilimi, kere-kere, fasahar nukiliya, kiwon lafiya da sauransu a matsayin lamarin da ke tabbatar da rashin nasarar da makiya suka samu a fagen sanya wa Iran takunkumi.

Tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci Amurka ta dau siyasar kiyayya da al'ummar Iran da kuma tsarin Musulunci na kasar. Ko shakka babu juyin juya halin Musulunci ya 'yantar da Iran daga mulkin mallakan Amurka, hakan shi ne ummul aba'isin din irin wannan gaba da Amurkan take yi da Iran da fatan ko za ta sami samar sake dawo da ikonta a kasar. Bayan shekara da shekaru na kokari da kulla makirce-makirce da nufin kifar da gwamnatin Musulunci ta Iran da kuma irin gazawar da suka yi wajen cimma wannan manufa ce ya sanya Amurkawan a halin yanzu fara maganar neman tattaunawa da Iran da kuma sanar da cewa su dai a halin yanzu sun yi watsi da batun kifar da gwamnatin Musulunci. A jawabin nasa na jiya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya mayar wa Amurkawan da martani da cewa wannan batun dai ba wani abu ba ne da zai faranta wa al'ummar Iran rai don kuwa a baya ma lokacin da Amurkan take da karfi sannan kuma take ta kokari wajen kifar da gwamnatin Musuluncin, hakan bai taba razana al'ummar Iran ba. Don haka al'ummar Iran ba ta damu da ko Amurka tana da wannan shirin na kifar da gwamnatin Musulunci ko kuma a'a ba, dabara dai ta rage wa mai shiga rijiya.  

Yayin da ya koma kan batun tayin tattaunawa da jami'an Amurka suke ci gaba da gabatarwa kuwa, Jagoran cewa ya yi shi dai ba ya ganin akwai wani alheri cikin wannan tattaunawar amma dai ba zai hana a yi ta ba, sai dai kuma ya sake jaddada cewar wajibi ne Amurkan ta bayyanar da kyakkyawar aniyar da take da ita kan wannan batu idan har da gaske take yi. Ayatullah Khamenei ya ce hanya guda kawai da yake ganin za a iya magance matsalar da ke tsakanin kasashen biyu ita ce gwamnatin Amurkan ta yi watsi da irin kiyayyar da take nunawa Iran da al'ummarta, in kuwa ba haka ba, to babu wani abin da zai sauya.  

Yayin da ya koma kan barazanar da jami'an HKI suke ci gaba da yi na kawo wa Iran hari kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai cewa yayi HKI dai ba ta kai matsayin da al'ummar Iran za su dauke ta a matsayin makiyarsu ba, don ba ta kai wannan matsayin ba, to sai dai kuma duk da haka ya ja kunnen jami'an HKIn da cewa matukar gigi ya debe su, suka kawo wa Iran hari, to kuwa su kwana da sanin cewa Iran za ta rusa Tel Aviv da Haifa da mai she su turbaya.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook