A+ R A-
29 February 2020

Fatawar Jagoran Imam Khamenei (h) Dangane Da Hukumce-Hukumcen Jami’i Mai Kula Da Sayo Kayayyaki Na Wata Ma’aikata

Abin da ke biye, amsar da Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma Jagoran musulmi Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei ya bayar ne dangane da wata tambaya da aka gabatar masa da take cewa:

 

Tambaya: Mutumin da ya kasance yana aiki a wata ma’aikata (shin ta gwamnati ce ko kuma wacce ba ta gwamnati ba) a matsayin mai sayo kayayyakin da ma’aikatar take bukata. Duk da cewa akwai shaguna da wajaje daban-daban da ake sayar da irin kayayyakin da ake aikansa ya sayo, to amma sai ya ke tafiya wajen wani da ya san shi da kafa masa sharadin cewa zai dinga sayen kayan a wajensa amma da sharadin zai ba shi wani abu daga cikin ribar da aka samu din. To tambaya a nan ita ce:

(1). Mene ne hukuncin wannan sharadin a shar’ance?

(2). Idan har yana yin hakan ne bisa izinin shugaba ko kuma wani babban jami’in wannan kamfanin ko ma’aikatar fa, mene ne hukuncin hakan?

(3). Idan kamfani ko shagon da ake sayen kayan a wajensa ya gabatar wa wannan ma’aikatar da farashin da ya dara ainihin farashin wadannan kayayyakin a kasuwa sannan kuma aka kulla yarjejeniyar sayen kan hakan, mene ne hukuncin hakan?

(4). Mene ne hukuncin kudin da masu shagunan da ake sayen kayayyakin a wajensu suke ba wa wannan jami’i mai sayen kayayyakin baya ga hakikanin kudin da aka rubuta a jikin rasidin (receipt) kayayyakin, mene ne hukuncin hakan a wajen su masu shagon da kuma shi kansa jami’i mai sayen kayan?

(5). Idan shi wannan mutumin da aka ambatan, baya ga kasantuwarsa jami’i mai sayen kayayyaki ga wannan ma’aikatar, har ila yau kuma yana aiki wa wani kamfani a matsayin mai nemo masa (kamfanin) kasuwa. Don haka sai ya yi wannan aiki na neman kasuwar ga wannan kamfanin, shin yana iya karbar wani abu daga wajen kamfanin a matsayin riba.

(6). Idan mutum ya sami wata riba daga cikin wannan mu’amalar da aka ambata a sama, mene ne hukunci na shari’a a kansa dangane da wannan ribar?

 

Amsa:

 

(1). Wannan sharadin ba shi da wata fuska ta shari’a, don haka batacce ne.

(2). Izinin shugaba ko kuma babban jami’in wannan ma’aikatar a wannan yanayi ba shi da wani matsayi na shari’a don kuwa shi kansa sharadin ba shi da wata fuska ta shari’a ko kuma doka.

(3). Idan har farashin ya dara asalin farashin da yayi daidai da adalci ko kuma ya zamana za a iya samo wadannan kayayyakin da farashin da ya ke kasa da haka a kasuwa, to a irin wannan yanayin wannan yarjejeniya ta kasuwanci da aka kulla ba ta inganta ba.

(4). Ba ya halalta. Duk wani abin da jami’in sayo kayayyakin ya karba a wannan bangaren, wajibi ne ya mayar da shi ga wannan ma’aikata da ya ke mata aikin sayo kayayyakin.

(5). Ba shi da hakkin karbar wani kaso cikin kudin. Duk wani abin da ya karba a wannan bangaren, to wajibi ne ya mayar da shi ga wannan ma’aikatar. Sannan kuma idan har wannan yarjejeniyar da suka kulla din ta saba wa maslahar ma’aikatar, to tun asali ma batacciya ce.

(6). Dukkanin abin da mutum ya karba da ya saba wa shari’a, wajibi ne ya mayar da shi ga wannan ma’aikatar da ta nada shi a matsayin mai sayo mata kayan.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook