A+ R A-
25 May 2020

Jagora: Iran Tana Adawa Da Hari Kan Fararen Hula, A Boston Ne Ko A Peshawar, Ko Bagdad Ko Siriya

A yammacin yau Laraba (17-4-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandojin soji, zababbun ma’aikata da membobin sansanonin dakarun sa kai na Basij da kuma wasu daga cikin iyalan sojojin Iran don tunawa da ranar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin abin alfahari sannan kuma sojojin masu kare hakkokin mutane, ma’abota ilimi, akida kana kuma kwararru a bangarori daban-daban. Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da rashin hikimar ma’abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka cikin matsayar da suke dauka, Jagoran cewa ya yi: Kasashen yammaci suna fuskantar cin kasa da rugujewa sakamakon karo da junan cikin halaye da dabi’unsu, rashin hankali, son amfani da karfi da kuma rashin girmama koyarwa ta bil’adama.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: A Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mutane suna girmama sojoji da kuma goyon bayansu ne sakamakon irin sadaukarwa da kokarin da suke yi, ba wai saboda nuna karfi da iko ba.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan irin ci gaban da sojojin Iran suka samu a bangaren ilimi da kere-kere, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Irin ci gaban da sojojin Iran suka samu a bangaren kera makamai na kariya wani lamari ne mai ban mamaki da ba za a taba kwatanta shi da kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, kai hatta ma shekarun farko-farko na nasarar ba.

Jagoran ya ce: An sami dukkanin irin wadannan ci gaban ne a daidai lokacin da makiyan al’ummar Iran suka hana su duk wani irin taimako da suke bukata. To amma kokari da kuma irin kwarewar da matasa da ‘ya’yan wannan al’umma suke da ita lamari ne mai ban mamaki.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan bangaren na riko da addini da akida da sojojin na Iran suke da shi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Aikata aiki saboda jin cewa hakan wani nauyi ne na addini a kai, shi ne ya sanya sojojin Iran suka zamanto wasu sojoji masu tsayin da kuma riko da koyarwa ta addini da abubuwa masu kima. Don haka ne ma Ayatullah Khamenei ya ce: Irin wadannan sojojin kuwa ko shakka babu za su yi nasara a gaban duk wata jarabawa da suka fuskanta.   

Jagoran juyin juya halin Musuluncin kuma babban kwamandan dakarun soji na Iran ya bayyana irin nasarar da sojojin Iran suka samu a lokacin kallafaffen yaki na shekaru 8 da aka kallafa wa kasar a matsayin daya daga cikin jarrabawar da sojojin suka fuskanta sannan kuma suka yi nasara a yayin wadannan jarrabawan. Don haka ne Jagoran ya kirayi sojojin da cewa: Lalle ku yi alfahari da kasantuwarku sojoji, sannan kuma ku kara himma wajen kiyaye wannan siffa da kuke da ita da kuma kara ta.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da da’awar Amurkawa na cewa suna adawa da kashe mutane inda ya ce: Sabanin wannan ikirarin, jiragen Amurka marasa matuka suna ci gaba da kashe kananan yara da mata da mutanen da ba su ci ba su sha ba a Afghanistan da Pakistan, sannan kuma ‘yan ta’addan da Amurkan take goyon bayansu suna ci gaba da kashe mutane a kasashen Iraki da Siriya.

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan karo da juna da ke cikin wannan ikirari na Amurkan, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Amurka da sauran masu da’awar kare hakkokin bil’adama sun yi gum da bakunansu dangane da kisan gillan da ake yi wa mutanen da ba su ci ba su sha ba a kasashen Pakistan, Afghanistan, Iraki da Siriya, to amma bayan ‘yan wasu hare-hare da aka kai Amurka, sai ga shi sun cika duniya da surutu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bisa riko da koyarwar Musulunci tana adawa da kuma yin Allah da duk wani tada bam da kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba, shin a Boston na Amurka ne ko kuma a Pakistan ko Afghanistan ko Iraki ko Siriya.

Jagoran ya kara da cewa: Akwai karo da juna cikin dabi’ar Amurka da sauran masu ikirarin kare hakkokin bil’adama dangane da kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. A saboda haka ne muka yi amanna da cewa Amurka da sauran masu kiyayya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mutane ne marasa hikima.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wannan wace irin hikima ce a ce babu matsala idan Amurkawa suka kashe kananan yara da mata a Afghanistan da Pakistan haka nan kuma ‘yan ta’addan da Amurka da kasashen yammaci da sahyoniyawa suke goyon bayan su suka kashe al’ummar Iraki da Siriya, amma idan wani abu ya fashe a Amurka ko wata kasar yammaci, shi kenan wajibi ne cutarwar da ke cikin hakan ta shafi kasashen duniya.

Don haka ne Jagoran ya ce: Irin wannan tunani na Amurka da sauran kasashen yammaci da suke ganin kansu a matsayin wadanda suke sama da saura, shi ne dalilin da zai yi sanadiyyar faduwa da kuma gushewarsu.

Daga karshe Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjina wa iyalai da matan sojojin saboda irin sadaukarwa da kuma hakurin da suka nuna inda ya kiraye su da su yi alfahari da samun irin wadannan mutanen.

Kafin jawabin Jagoran, sai dai babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Iran Laftanar Janar Ata’ullah Salehi ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyukan da sojojin suke yi da kuma irin shirin da suke da shi wajen tinkarar duk wata barazana.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook