A+ R A-
22 January 2020

Jagora Imam Khamenei Yayi Kakkausar Suka Ga Keta Hurumin Kabarin Sahabi Hijr bn Adi (r.a)

A safiyar yau Litinin (6-5-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami’ai da sauran ma’aikatan hukumar gudanar da zaben shugaban kasa da na kananan hukumomi na Iran inda ya bayyana fitowar jama’a kwansu da kwarkwatansu yayin zaben da za a gudanar din a matsayin wani lamari dai zai lamunce ci gaban kasar Iran kamar yadda kuma ya kirayi jami’ai masu gudanar da zaben da kuma su kansu ‘yan takara da su kiyaye da kuma girmama doka.

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan lamari mai bakanta rai da ya faru a kasar Siriya na keta hurumin kabarin babban sahabin nan Hijr bn Adi, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne al’ummar musulmi musamman manyan cikinsu da suka hada malamai da sauran ‘yan siyasa sun sauke nauyin da ke wuyansu na fada da wannan bakar aniya ta masu kafirta musulmi, sannan kuma su yi abin da za su iya wajen hana yaduwa wutar wannan fitinar.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana zaben a matsayin wata amana mai girma ta kasa da kuma Musulunci yana mai cewa: majalisar kiyaye kundin tsarin mulki da sauran cibiyoyi masu sanya ido da kuma tabbatar da tsaro suna dauke da wannan amana ce mai girma, kamar yadda wannan aiki mai girma da muhimmanci kuma yake wuyansu ne.

Har ila yau yayin da yake ishara da rawar da zabe ya ke takawa wajen sayar rayar da kasa da kuma tsarin Jamhuriyar Musulunci, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Fitowar al’umma a lokacin zabubbukan da aka gudanar tsawon shekaru 34 da suka gabata (a Iran), a koda yaushe sun kasance masu kore wasu bala’oi daga kasar Iran da kuma kara karfin gwuiwa ga kasa, al’umma da kuma wannan juyi na Musulunci ne.

Jagoran ya kara da cewa a wasu bangarorin zaben shugaban kasar Iran da za a gudanar nan gaba kadan ya dara irin wadanda suka gabace shi a fagen muhimmanci inda ya ce: Gudanar da zabubbuka guda biyu na shugaban kasa da kuma na kananan hukumomi a lokaci guda yana daga cikin abubuwan da ya kara wa wannan zaben irin muhimmancin da ya ke da shi.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kafa majalisar kananan hukumomi a dukkanin kauyuka da birane a matsayin wani abu da ke nuni da irin rawar da mutane suke takawa wajen gudanar da kasarsu, don haka sai ya kirayi jami’an gwamnati da sauran al’ummar kasar Iran da cewa: kada su bari muhimmancin da zaben shugaban kasa yake da shi ya dushe haske zaben ‘yan majalisar kananan hukumomin da za a gudanar tare.

Har ila yau kuma yayin da ya ke karin bayani dangane da wani bangare na muhimmancin da zabe mai zuwa yake da shi, jagoran ya yi ishara da irin karfi da ikon da shugaban kasa yake da shi cikin kundin tsarin mulkin kasa da kuma sauran dokoki inda ya ce: irin wannan matsayin lamari ne da ke nuni da irin muhimmancin da zaben shugaban kasa yake da shi ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin wanda ya kafa tushen shigowa cikin fage da kuma taka gagarumar rawa da al’ummar Iran suke yi a fagen gudanar da kasar su, yana mai ishara da irin dagewar da marigayi Imam ya yi wajen a gudanar da jin ra’ayin al’umma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci don su zabi irin tsarin da suke so ya jagorance su.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da kokarin da wasu suke yi na rage kaifin fitowar al’umma da kashe musu gwuiwa wajen fitowa zaben inda ya ce: Wasu sun yi ta kokari wajen ganin sun kawar da kumajin da ke tattare da zaben ko kuma ma kada a gudanar da shi a lokacin da aka tsara, to cikin taimakon Allah sun sha kashi, kuma a nan gaba ma babu inda za su je.

Ayatullah Khamenei ya bayyana fitowar jama’a yayin zaben a matsayin abin da zai karfafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci tana nufin kasantuwar mutane a lokacin da ya dace da kuma yunkurin mutane wajen cimma manyan manufofin da aka sanya su a gaba. Don haka ne ne makiya suke kokari wajen ganin sun rage irin kaifin wannan fitowar ta mutane.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Karfin Jamhuriyar Musulunci ya damfara ne da zukata, so da kuana, hikima da hangen nesa, basira da kuma kasantuwar mutane a fage. Matukar aka rasa wannan gagarumar garkuwa, to kuwa lalatattun ‘yan mulkin mallaka na duniya za su sami hanyar cutar da wannan tsari na Jamhuriyar Musulunci. Daga nan sai Jagoran ya ce: Tabbas, cikin yardar Allah da kuma himmar mutanenmu masu girma, insha Allahu za a gudanar da wannan zabe da ke gabanmu cikin dukkan karfi da kuma fitowar jama’a.

Wani batun kuma da Jagoran ya yi magana kansa a yayin wannan ganawar shi ne batun girmama doka a dukkanin matakai na zaben. Don haka ne ma Jagoran ya yi ishara da irin kokarin da makiya ‘yan kasashen waje suke a wannan bangaren inda ya ce: A shekara ta 2009 (a lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar) wadannan sun sanya wasu mutane su yi abin da ya saba wa doka, ko za su sami damar tunzura mutane su fito don su tinkari wannan tsari na Musulunci, amma cikin tausayawa ta Ubangiji sun gagara cimma wannan manufa ta su.

Jagoran ya yi ishara da wasu ayyuka da aka yi wajen fayyace shakkun da wasu suka gabatar dangane da sakamakon zaben shekara ta 2009 inda ya ce: Mutanen da suka cutar da kasar nan da kuma al’ummar Iran (bayan zaben), sun yi hakan ne saboda rashin yarda da doka da kuma bin hanyar da doka ta tanadar ne, koda ya ke tsarin Musulunci yayi nasara sakamakon irin yadda ya fahimci yanayin al’ummar kasar nan. Don haka ne Jagoran ya yi kiran da a girmama dokokin kasa a yayin zaben.

Bayan magana kan zaben kuma, Ayatullah Khamenei ya yi karin haske kan batun keta hurumin kabarin sahabin Ma’aikin Allah (s.a.w.a), wato Hijr bn Adi da sauran manyan Musulunci da masu ‘yan ta’addan kasar Siriya suka yi inda ya ce: Abin da ya ke kara bakanta rai cikin wannan abin da ya farun shi ne samuwar wasu mutane masu mummunan tunani sannan kuma wadanda aka bar su a baya a tsakankanin al’ummar musulmi, wadanda suke ganin girmama fitattun mutanen da suka yi hidima wa Musulunci a farko-farkon bayyanarsa a matsayin shirka da kuma kafirci.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samuwar irin wannan mummunan tunani a matsayi wata musiba da ta fada wa Musulunci da kuma musulmi, inda ya ce: Wadannan mutanen dai su ne wadanda magabatansu suka rusa kaburburan Imamai tsarkaka a makabartar Baqi’a. Idan da ba don tinkararsu da al’ummar musulmi suka yi ba, da kabarin Annabi (s.a.w.a) ma sai sun rusa shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin wadannan mutane masu mummunan tunani ne wadanda suke ganin kasantuwa a kaburburan manyan bayin Allah da nema musu gafarar Ubangiji da kuma neman gafara wa kai a wajen a matsayin shirka, mutane ne da suka kauce wa hanya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Shirka ita ce a samu wasu mutane da za su zamanto kayan aikin cibiyoyin leken asirin Ingila da Amurka sannan kuma su dinga cutar da al’ummar musulmi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wani irin tunani ne wannan a ce biyayya da kaskantar da kai a gaban rayayyun dawagitai ba shirk aba ne, amma girmama magabata ya zamanto shirka?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: A halin yanzu wannan akida ta kafirta musulmi da ke samun goyon baya na kudi da makamancinsa (daga wasu bangarori), ta zamanto babban bala'i kuma na hakika ga Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan irin martani da ‘yan Shi’a suka mayar wa wannan danyen aikin, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: ‘Yan Shi’a dai sun gujewa fadawa wannan tarko na hura wutar rikicin Shi’a da Sunna da aka kunna, sannan kuma sun tabbatar da irin hangen nesan da suke da shi.

Haka nan kuma Jagoran ya bayyana irin matakan da bangaren ‘yan Ahlusunna suka dauka wajen Allah wadai da wannan danyen aikin a matsayin wani lamari da ke nuni da irin hangen nesan da su ma suke da shi yana mai cewa: Wajibi ne a ci gaba da yin Allah wadai da wannan danyen aiki. Don kuwa matukar malamai, masana da sauran ‘yan siyasar kasashen musulmi ba su sauke wannan nauyi da ke wuyansu ba, to kuwa wannan fitinar ba za ta tsaya haka nan kawai ba.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wajibi ne ta hanyar amfani da hanyoyi na siysa, fatawoyi na addini da kuma rubuce-rubuce a kawo karshen wutar wannan fitinar.

Jagoran ya bayyana cewar ko shakka babu akwai hannun makiya cikin wannan lamari inda ya ce: Cibiyoyi da jami’an kasa da kasa da sauran ‘yan siyasar da suke ta tada jijiyoyin wuya saboda an rusa wani waje na tarihi, amma sai ga shi sun yi gum da bakunansu kan wannan babban cin mutumcin.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ko shakka babu Allah dai yana nan a madakata, ko shakka babu tafarkin Allah zai yi nasara a kan makircin makiya, sannan kuma masu kokarin haifar da fitina da hana al’ummar musulmi ci gaba, ba za su yi nasara ba.

(Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei)

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook