A+ R A-
25 May 2020

Imam Khamenei Ya Gana Da Malaman Makarantu Na Iran Don Tunawa Da Makon Malamai

A safiyar yau Laraba (9-5-2013) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban malaman makarantu da masu gudanar da ayyukansu a fagen tarbiyyar al’umma daga duk fadin kasar Iran, inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana ma’aikatar ilimi da tarbiyya a matsayin wata cibiya mai  tsananin muhimmanci sannan tushe na asali wajen kafa al’umma ma’abociyar ci gaba da kuma gudanar da rayuwa irin ta Musulunci yana mai cewa: Ci gaba da irin yunkuri na ciyar da kasar Iran gaba a dukkan bangarori da aka faro wani lamari ne da ke bukatar kokari ba kama hannun yaro bugu da kari kan kumaji na siyasa da  tattalin arziki, wanda ko shakka babu ma’aikatar ilimi da tarbiyya tana da rawar da za ta taka a wannan bangaren.

A yayin wannan ganawar, wacce aka gudanar da ita don tunawa da makon girmama matsayin malamai a Iran, Ayatullah Khamenei ya jinjinawa irin rawar da shahid Ayatullah Mutahari da sauran malaman makarantu na Iran da suka yi shahada suka taka a fagen ilimi da tarbiyyar daliban makarantu inda ya bayyana matsayin aikin malanta a mahangar Musulunci da cewa wani matsayi ne mai girman gaske da ya bambanta da matsayin da sauran ayyuka suke da shi. Jagoran ya ci gaba da cewa: A hakikanin gaskiya malamai su ne tushen gina yara manyan gobe na kasa. A saboda haka ne babu yadda za a iya kwatanta aikin malanta da sauran ayyuka.

Jagoran ya kara da cewa: Isar da kasa da kuma wata al’umma zuwa ga daukaka, jin dadi da walwala, ci gaba na ilimi, jaruntaka, hikima, ‘yanci da kuma amfani da hankali ya damfara ne ga samar da ingantacciyar tarbiyya ga yara da matasan wannan kasar, wanda mafi girman wannan nauyin yana wuyan malaman makarantu ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Dalilin da ya sanya nake nanata batun wajibcin samar da sauyi da kuma karfafa tushen ilimi da tarbiyya saboda wannan dalilin ne na cewa samar da duk wani nau’in ci gaba cikin al’umma ya ta’allaka ne da samar da tushe na asali wanda shi ne ilimi da kuma tarbiyya wadanda suka yi daidai da mahanga ta Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan umurnin da ya bayar na a samar da sauyi cikin tsarin ilimi da tarbiyya na kasar Iran, Ayatullah Imam Khamenei ya jaddada wajibcin aiwatar da wannan sauyi sai dai kuma ya ja kunnen jami’an da abin ya shafa da su guji gaggawa maras amfani wajen aiwatar da hakan yana mai jaddada wajibcin haifar da irin wannan sauyi a dukkanin bangarori na ilimi da tarbiyya.

Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan wajibcin da ke wuyan gwamnati da majalisa wajen taimakawa bangaren ilimi da tarbiyya, Jagoran ya yi ishara da jami’ar tarbiyyartar da malamai ta kasar Iran inda ya ce: wannan jami’a dai ta bambanta da sauran jami’oi na kasa, don kuwa a wannan jami’ar ana kokarin gina malamai ne. A saboda haka wajibi ne ma’aikatar ilimi ta ba wa wannan jami’a kula da kuma taimako na musamman.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi magana kan batun littafan da ake koyar da su a makarantu a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske da ya wajaba a ba shi kulawa ta musamman. Jagoran ya ce: Wajibi ne a koda yaushe a bude idanuwa da kuma sanya ido abubuwan da ke cikin littafan da ake karantar da su a makarantu don ganin sun yi daidai da bukatar da daliban makarantun suke da ita da suka hada da ilmummuka na addinin Musulunci da kuma gina dan’adam, sannan kuma a yi gyara da wadanda suke bukatar gyaran.

 

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Imam Khamenei ya jinjinawa malaman na Iran saboda irin sadaukarwa da wahalhalun da suke sha wajen tarbiyyantar da yara ‘yan makaranta yana mai ishara da irin tsayin dakan da malaman suka yi wajen kare manufofin juyin juya halin Musulunci na kasar Iran tsawon shekaru 34 da suka gabata bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar inda ya ce: A wannan shekarar dai da aka ba ta sunan ‘Shekarar Kumaji na Siyasa da Tattalin Arziki”, ko shakka babu ma’aikatar ilimi da tarbiyya za ta taka gagarumar rawa wajen tabbatar da wannan manufar da aka sanya a gaba.

Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin gagarumin ci gaban da kasar Iran ta samu cikin shekaru talatin din da suka gabata, Jagoran ya bayyana cewar: Irin gagarumin ci gaban da Iran ta samu sannan kuma cikin sauri wani lamari ne da hatta cibiyoyin kasa da kasa sun tabbatar da hakan, koda kuwa ba sa so.

To sai da kuma Jagoran ya ce: Duk da irin wannan gagarumin ci gaban da aka samu, Iran tana bukatar kara damara wajen isa ga manufofin da ta sa a gaba da kuma isa ga matsayin da ya dace da ita.

(Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei)

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook