A+ R A-
22 January 2020

Imam Khamenei: Girmama Matsayin Mata, Zai Iya Magance Matsalolin Da Al'umma Take Fuskanta

A safiyar yau asabar (11-5-2013) ce, a daidai lokacin da ake shirin shiga watan Rajab mai albarka, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan mata masana masu gudanar da ayyuka a fagage daban-daban da suka hada da jami'oi da makarantun Hauza, da iyalai da mata, gudanarwa, kafafen watsa labarai da kungiyoyin fararen hula na Iran.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawa wacce ta dauki kimanin sa'oi biyu da rabi ana yinta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wajibcin gabatar da mahangar Musulunci dangane da mace a fagage na kasa da kasa da kuma karfafa cibiyar iyali da girmama mata a cikin gida a matsayin abubuwa guda biyu da ake bukatarsu cikin gaggawa. Jagoran ya ci gaba da cewa: wajibi ne masu gudanar da ayyukansu a fagagen da suke da alaka da juyin juya halin Musulunci su tabbatar da kasantuwarsu a fagen kare juyin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran sannan kuma albarkacin marigayi Imam Khumaini (r.a) an gudanar da ayyuka masu kyau da kuma girman gaske a fagen da shafi mace, to sai dai duk da haka akwai bukatar a kara himma.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da cewa bai kamata a yi sakaci da sako-sako da lamarin da ya shafi mace a wannan lokaci da ake samun farkawa ta Musulunci ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Da wani dalili ne za a dinga yin dari-dari da nuna rauni a gaban al'adun kasashen yammaci alhali kuwa muna da irin wannan mahanga ta Musulunci dangane da mace?

Jagoran ya bayyana cewa akidar kasashen yammaci dangane da mace wata akida ce tsararriya wacce take da alaka da siyasa inda ya ce: Duk da cewa a zahiri irin wadannan akida ta yammaci ita ce take yawo a halin yanzu, to amma ko shakka babu akidar kasashen yammaci dangane da mace ta kama hanyar faduwa kasa warwas.

Jagoran ya bayyana kokarin mai da mace tamkar namiji da kuma mayar da mace a matsayin wani kayan aiki na jin dadin namiji a matsayin tushen akidar kasashen yammaci dangane da mace inda ya ce: Kasashen yammaci suna kokari wajen tilasta wa mata wasu ayyuka wadanda sun dace ne kawai da yanayin namiji sannan da kuma bayyanar da hakan a matsayin wani abin alfahari ga mace.

Dangane da wannan lamarin, Jagoran ya bayyana cewar babu matsala mace ta yi aiki a bangaren gudanar, matsalar dai ita ce irin wannan mahanga ta kasashen yammaci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A mahangar Musulunci, kowane guda daga cikin mace da namiji suna da wasu siffofi da kowane guda ya kebanta da shi, to amma a bangaren hakkoki na dan'adam da zamantakewa da kima ta dan'adam da kamalarsa, babu wani bambanci a tsakaninsu.

Jagoran ya kara da cewa: Ingantacciyar mahanga dangane da mace, ita ce mahangar da take kallonta a matsayinta na mace da kuma abubuwan da suke tabbatar mata da daukaka.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kallon mace a matsayin kayan aiki na biyan sha'awar namiji a matsayin wani babban bala'i yana mai cewa: A halin yanzu dai wasu daga cikin masanan kasashen yammaci suna fara ganin hatsarin da ke cikin wannan mahangar, don kuwa irin wannan bala'i na auren jinsi guda da ke faruwa a can ya samo asali ne daga irin wannan mahangar. Hakan kuwa yana iya zama daya daga cikin abin da zai kawo faduwarsu kasa war was.

Har ila yau Jagoran ya kirayi al'umma da su yi taka tsantsan dangane da irin wadannan mahangar inda ya ce: Ko da yake a kasar mu muna da wata kariya saboda batun hijabi da ake da shi, to amma duk da haka wajibi ne a kara himma dangane da abin da ya shafi hijabi da kuma kan iyakoki na rayuwa tsakanin mace da namiji.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana karfafa yanayin iyali da kuma girmama mace a matsayin wasu batutuwa da ake da bukatarsu inda ya ce: Wajibi ne a samar da wasu dokoki da halaye da kuma yanayi da za su share fagen cewa ba a zalunci mace a fagage daban-daban na rayuwa da tunani da kuma iyali ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne dukkanin iyali su dinga kallo mace da kallo na girmamawa sannan kuma a samar da yanayin da ‘ya'ya za su zamanto masu girmama iyayensu mata da kuma rusuna musu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar aka samar da yanayi da al'adar girmama mace a cikin al'umma, to kuwa za a iya magance da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta da kuma irin zaluncin da ake yi wa mace.

Har ila yau daga cikin batutuwan da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabo da kuma yin karin haske kansu sun hada da batun aure, tufafin mace, taimakawa mace da kuma tabbatar da hakkokinta a cikin al'umma.

Kafin jawabin Jagoran sai da wasu daga cikin mata masanan suka gabatar da jawabansu da kuma bayyanar da mahangarsu kan batutuwa daban-daban da suka shafi mata da kuma hanyoyin da za a magance matsalolin da mata din suke fuskanta.

(Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei)

 

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook