A+ R A-
29 February 2020

Imam Khamenei Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Ayatullah Zanjan

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sakon ta'aziyyarsa dangane da rasuwar marigayi Ayatullah Hajj Izzuddeen Husaini Zanjani wanda ya rasu a ranar Talata 14, Mayun 2013.

Abin da ke biye fassarar sakon ta'aziyyar Jagoran ne:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina isar da sakon ta'aziyyar rasuwar babban malami marigayi Ayatullah Hajj Agha Izzuddeen Husaini Zanjani (yardar Allah ta tabbata a gare shi) ga dukkanin masoyansa a garuruwan Masshad da Zanjan haka nan kuma ga manyan malamai da makaranta Hauza sannan kuma musamman ga ‘ya'yansa da kuma iyalansa masu girma.

Tsawon lokaci marigayin wanda ya kasance daga cikin fitattun malamai masana ya kasance abin komawar masana kama daga garin Zanjan har zuwa tsawon lokacin da ya shafe a garin Masshad mai tsarki, sannan kuma ya kasance mai shiryar da al'umma daban-daban.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kara masa girman matsayi sannan kuma ya albarkaci abubuwan da ya bari.

Sayyid Ali Khamenei

24, ga watan Ordebehesht, 1392.

(14, ga watan Mayu, 2013)

(Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora)

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook