A+ R A-
22 January 2020

Jagora Imam Khamenei Yayi Karin Haske Kan Kokarin Makiya Na Dushe Hasken Zaben Shugaban Kasar Iran

A safiyar yau Laraba (15-5-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban al'ummomi daban-daban na Iran da suka kai masa ziyara. A yayin wannan ganawar Jagoran ya kirayi al'ummar Iran musamman matasa da su yi kokarin amfanuwa da dama ta kyautata ruhi da ake samun cikin watan Rajab, kamar yadda kuma ya bayyana zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuni mai kamawa a matsayin wata jarrabawa ta daban ga al'ummar Iran inda ya ce: Don cimma manufofin da suka sa a gaba da kuma hana makiya cimma bakaken manufofinsu, wajibi ne mutane su fito kwansu da kwarkwatansu yayin wannan zaben sannan su zabi mutumin da ya dace, mumini, mai riko da koyarwar juyi, ma'abocin azama da tsayin daka da kuma himma ta jihadi daga cikin ‘yan takaran da majalisar kundin tsarin mulki za ta tantance wanda kuma zai dauki wannan gagarumin nauyi na tabbatar da daukaka da ci gaban kasa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana zaben shugaban kasar da za a gudanar a wata mai kamawa a matsayin lamari mafi muhimmanci a halin yanzu a Iran, sannan kuma yayin da yake magana kan tasirin hakan a halin yanzu da kuma a nan gaba, Jagoran cewa ya yi: A yayin wannan zaben, mutane za su zabi mutum guda ne wanda zai dauki nauyin gudanar da kasar nan na tsawon shekaru hudu, to amma mai yiyuwa ne wasu daga cikin matsaya da ayyuka masu kyau ko marasa kyau da zai yi su zamanto masu tasiri a kasar nan har nan da shekaru 40 masu zuwa. Hakan lamari ne da ke nuni da irin muhimmancin da zaben shugaban kasa yake da shi ne.

Har ila yau a ci gaba da bayanin karin muhimmancin da zaben na bana yake da shi, Jagoran cewa ya yi: Duk da cewa akwai sauran wata guda da wani abu kafin zaben, to amma zaben ya zamanto daya daga cikin batutuwa na kasa da kasa, sannan kuma tuni cibiyoyin tunani na duniya da makiya al'ummar Iran suka share fagen sanya ido kan zaben.

Haka nan kuma yayin da ya ke bayanin cewa manufar da makiya suke son cimma a yayin wannan zaben ya yi hannun riga da manufofin da al'ummar Iran suke son cimmawa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Al'ummar Iran suna neman mutumin da ya fi dacewa ne wanda zai ciyar da kasar nan gaba cikin sauri, kamar yadda kuma zai yi kokari wajen magance matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu da kuma kyautata rayuwar mutane karkashin daukaka da ‘yancin kai na Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: To su kuwa makiya suna kokari ne wajen rage armashin zaben, suna neman mutumin da ba shi da wadannan siffofi wanda zai mayar da Iran ta zamanto mai dogaro da wasu, mai rauni sannan wacce ta ci baya a bangarori daban-daban da kuma sanya ta a hanya da siyasar baki ‘yan kasashen waje.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas makiyan suna fatan ganin ba a gudanar da zaben ba ne, to amma da ya ke sun ga ba za su iya cimma hakan ba, don haka sai suka koma ga kokarin kashe gwiwan mutane daga fitowa da yin tasiri cikin wannan zaben.

Jagoran ya bayyana kokarin kashe gwiwan mutane da sanya su yanke kauna cikin fitowa yayin zaben a matsayin daya daga cikin dabarun na asali na makiya inda ya ce: Suna son su sanya mutane jin cewa babu wata fa'ida cikin fitowarsu zaben, don haka da wani dalili ne za su fito?

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin abubuwan da manyan kafafen watsa labaran duniya da na sahyoniyawa suke yi cikin makonnin baya-bayan nan dangane da zaben na Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Kokarin nuna cewa Iran tana cikin rikici, kambama matsalolin da ake da su, sanya yanke kauna cikin zukatan mutane da cewa ba za a iya magance su ba da kuma bakanta makomar wannan kasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin da wadannan kafafen watsa labarai suke bi wajen dushe kaifin wannan zabe na Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas akwai matsaloli irin su tsadar kayayyaki da rashin aikin yi a kasar nan, to amma wace kasa ce ba ta da matsaloli? Shin irin zanga-zangogin da al'ummomin kasashen Turai suke yi a kowace rana, ba alama ce da ke tabbatar da cewa matsaloli sun dabaibaye kasashen Turan ba?

Haka nan kuma yayin da yake kwatanta yanayin da Iran take ciki da yanayin da wasu kasashen na daban suke ciki, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wace kasa ce take da irin ‘yanci na kasa da hadin kai na al'umma kamar irin wanda Iran take da shi? Wace kasa ce take da irin wadannan matasa da Iran take da su wadanda a koda yaushe suke ci gaba da samun nasarori a fagagen ilimi? Wace al'umma ce ta sami damar yin tasiri cikin abubuwan da ke faruwa a yankin nan da ma duniya kamar yadda al'ummar Iran ta samu? Sannan wace al'umma ce ta sami nasarar kawo karshen dukkanin makirce-makircen makiya sannan kuma ta ci gaba da bin tafarkin da ta sa a gaba kamar yadda al'ummar Iran masu girma suka samu?

Jagoran ya kammala wannan bayani nasa kan irin fito na fito na siyasa da al'ummar Iran suke yi da masu adawa da su dangane da wannan zaben da cewa: Wajibi ne mutane su san cewa fitowarsu kwansu da kwarkwatansu a yayin wannan zaben, lamari ne da zai ba wa kasar nan garkuwa da kuma rage irin kwadayi da fatan da ‘yan kasashen waje suke da shi na cimma bakaken manufofinsu.

Yayin da ya koma kan jami'an gwamnati, ‘yan siyasa da kuma masu fadi a ji a kasar ta Iran Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kiraye su da cewa: Ku karfafa wa mutane gwiwa, don kuwa hakikanin abin da ke gudana a kasar nan da kuma irin azama da tsayin daka na kasa lamari ne mai sanya fata cikin zukatan duk wani mutum ma'abocin adalci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda muka san al'ummar Iran sannan kuma cikin iko da yardar Allah, a wannan karon ma al'ummar Iran za su bada wa makiya kasa a ido.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi karin bayani kan alamu da siffofin dan takaran da ya fi dacewa da ya zama shugaban kasa ya kamata ya mallaka inda ya kirayi al'umma da su binciko wadannan siffofi don sauke wannan nauyi na shari'a da ke wuyansu.

Jagoran ya bayyana wajibcin zaben mutumin da dukkanin himmarsa ta ginu ne a kan kiyaye daukaka, mutumci da kuma ci gaban kasar Iran inda ya ce: Dukkanin abubuwan da muka samu cikin wadannan shekaru talatin da nasarar juyin juya halin Musulunci mun same su ne albarkacin riko da manufofin juyin nan. A saboda haka ya kamata mu zabi mutumin da zai ba da dukkanin himmarsa wajen tabbatar da wadannan manufofin ne.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wajibcin sanya ido sosai kan irin alkawurran da ‘yan takaran suke yi a lokacin yakin neman zabensu, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A wasu lokuta, don janyo hankulan mutane, wasu ‘yan takaran su kan yi alkawarin aiwatar da wasu abubuwa wadanda sun ketare kan iyakan ikon da shugaban kasa yake da shi da kuma irin karfin da kasar nan take da shi. To amma mutane dai za su kada wa mutumin da alkawarin da zai yi ya yi daidai da hakikar da take a kas ne sannan kuma wanda yake da hanyoyin da suka dace wajen magance matsalolin da ake da su.

Har ila yau Jagoran ya sake jaddada wajibcin girmama doka a yayin zaben da kuma bayansa inda ya ce: Aiki da doka wata alama ce sannan kuma hanya ce ta tabbatar da kwanciyar hankalin al'umma da kuma kiyaye hadin kai na kasa. A saboda bai kamata wani ya yi watsi da hakan ba.

Jagoran ya bayyana fitinar da ta faru a kasar Iran bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2009 a matsayin sakamako na kin bin doka inda ya ce mai yiyuwa ne doka ta zamanto ba daidai ba, to amma dai ta fi a ce babu dokar kwata-kwata. Har ila yau kuma Jagoran ya bayyana cewar mai yiyuwa ne a sami kuskure cikin aiwatar da dokan, to amma abin da ya fi dacewa shi ne a magance wannan matsalar ta hanyar da doka ta tanadar.

A wani bangare na jawabin nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan irin muhimmancin da watan Rajab yake da shi da kuma irin amfanin da za a iya samu a cikinsa wajen karfafa ruhi da kuma kyautata zuciya don haka ya kirayi al'ummar Iran da ma sauran al'ummomin musulmi da su yi dukkanin abin da za su iya wajen amfanuwa da wannan wata mai albarka.

(Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagoran)

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook