A+ R A-
28 February 2020

Jagora Ya Jagoranci Taron Tunawa Da Shekaru 24 Da Rasuwar Imam Khumaini (r.a)

A safiyar yau Talata (4-6-2013) ne miliyoyin al’ummar Iran da sauran masoya juyin juya halin Musulunci na kasar Iran da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya suka taru a hubbaren marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke birnin Tehran don sake jaddada mubaya’arsu a gare shi da kuma riko da tafarkinsa a matsayin hanyar tabbatar da hadin kai a tsakaninsu.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen wannan taron na tunawa da shekaru 24 da rasuwar marigayi Imam din, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana yarda da Ubangiji, mutane da kuma kan kansa a matsayin abubuwan da suka share fagen nasara da kuma ci gaba da wanzuwa da ci gaban juyin juya halin Musulunci na kasar Iran. Har ila yau kuma yayin da ya ya koma kan zaben shugaban kasar da za a gudanar a nan gaba, Jagoran ya bayyana wannan zaben a matsayin zabe mai muhimmanci, sannan kuma ya kirayi al’ummar Iran da sauran ‘yan takaran zaben da cewa: Da yardar Allah kwanaki goma masu zuwa za su haifar da wani gagarumin yunkuri sannan kuma za su nasara cikin jarrabawar da ke gabansu a wannan rana ta 24 ga watan Khordad (14 ga watan Yuni – ranar da za a gudanar da zaben kenan).

Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan yunkurin ranar 15 ga watan Khordad 1342 (Yunin 1963 wato mafarin juyin juya halin Musulunci na kasar Iran) karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan ranar a matsayin rana mai matukar muhimmanci cikin tarihin kasar Iran inda ya ce: Bayan kama marigayi Imam Khumaini (r.a) da aka yi sakamakon jawabin da ya yi a ranar 13 ga watan Khordad din 1342 (3 Yunin 1963), hakan ya zamanto gagarumar barazana ga gwamnatin dagutu (ta wancan lokacin) sakamakon gagarumar zanga-zangar da mutane suka yi a garuruwan Tehran, Qum da sauran garuruwa wanda ke nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin mutane da malamai da kuma marja’iyya.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin wannan alaka mai karfi da ke tsakanin mutane da malamai a matsayin lamarin da ya lamunce karin karfi da kuma daukakar wannan yunkuri da kuma nasarar da ya samu, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A lokacin da mutane suka shigo cikin fage sannan kuma tunani da kwakwalansu suka hadu da wannan yunkurin, hakan ne ya samar wa yunkurin da yanayin ci gaba da tafiya da kuma samun nasara daga karshe.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin rashin imani da tausayin da gwamnatin dagutu ta wancan lokacin ta nuna wa al’umma a lokacin wannan yunkuri na watan Yunin 1963, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Daya daga cikin lamurra mafiya daukan hankula a yayin wannan lamarin shi ne irin gum da bakin da cibiyoyin kasa da kasa masu ikirarin kare hakkokin bil’adama suka yi. Don kuwa ba su nuna komai kashin nuna rashin amincewarsu da irin wannan diran mikiya da aka yi wa al’umma ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk da irin wadannan abubuwan, haka marigayi Imam Khumaini (r.a) shi kadai, amma tare da goyon bayan al’umma, ya tsaya kyam da kuma tabbatar wa da al’ummomin duniya irin tsayin daka da riko da tafarkin da ya yi amanna da shi.

Yayin da kuma yake ishara da abubuwan da suka sanya marigayi Imam Khumaini (r.a) yin irin wannan tsayin daka duk kuwa da matsin lambar da mahukuntan lokacin suke masa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da wasu abubuwa guda uku a matsayin abubuwan da suka sanya shi yin wannan tsayin dakan inda ya ce: Ko shakka babu ana iya ganin yarda da Allah, yarda da karfin mutane da kuma yarda da kai cikin samuwar Imam wadanda kuma su ne suka taimaka masa wajen tsayin dakan da ya yi tsawon lokacin wannan yunkuri na sa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Imam Khumaini (r.a) ya kasance yana magana da mutane ne daga tsakar zuciyarsa sannan su kuma mutane da dukkanin karfinsu da kuma zuciya guda suka amsa masa da kuma shigowa cikin fage, ta haka ne a sannu a hankali wannan yunkurin ya kama hanyar nasara, sannan daga karshe kuma ba tare da taimakon kowace kasa ba ya kai ga nasara.

 

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Imam Khumaini (r.a) ya dogara da Allah da kuma imani na gaskiyar alkawarin taimakonsa. A saboda haka ne ya kasance ba ya yin komai sai saboda Allah.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Har ila yau kuma marigayi Imam ya yi amanna da kuma dogaro da karfin mutane. A saboda haka ne al’ummar Iran ma’abota imani da jaruntaka suka zamanto a duk lokacin da suka sami wani Jagora da ya dace, suke bayyanar da kansu tamkar hasken rana a dukkanin fagage.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mutane suna da girman matsayi a wajen Imam, su kuwa makiya su ne wadanda ya fi kyamarsu. Hakan kuwa daya ne daga cikin manyan dalilan tsayin dakan Imam a gaban azzaluman mahukuntan da suke adawa da al’ummar Iran.

Haka nan kuma yayin da ya ke karin haske kan siffa ta uku da Imam ya kebanta da ita wato dogaro da kai da yake da shi, Jagoran cewa ya yi: Imam ya rayar da akidar ‘lalle za mu iya’ cikin zukatan al’umma da kuma bayyanar da karfin da al’ummar suke da shi a fagage daban-daban.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin jaruntakar da marigayi Imam ya nuna wajen tinkarar gwamnatin kama karya ta Shah, lokacin juyin juya halin Musulunci da kuma lokacin kallafaffen yaki da tinkarar ma’abota girman kan duniya, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: a sannu a hankali irin wannan jaruntaka, tsayin daka da kuma dogaro da kai cikin maganganu da kuma aiki da Imam yake da su suka yi tasiri a tsakankanin al’ummar Iran ta yadda suka zamanto abin koyi a fagen tsayin daka da kuma basira.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Irin wannan dogaro da kai da kuma jaruntaka ne suka sanya Imam ya zamanto a karshe-karshen rayuwarsa bai taba samun kokwanto ko shakku cikin matsayar da yake dauka ba, ta yadda hatta maganganu da matsayar da ya dauka a shekarun karshe-karshe na rayuwarsa sun ma fi na farko-farkon wannan yunkurin karfi da kumaji.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Albarkacin irin wannan dogaro da kai da kuma dogaro da Allah ya sanya al’ummar Iran watsi da duk wani yanke kauna da suke da shi a lokacin gwamnatin zalunci ta Shah, sannan kuma bayyanar da kansu  a fagage daban-daban na daukaka da ci gaba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin nasarorin da al’ummar Iran suka samu a bangarori daban-daban na rayuwa wanda ya ce sun sami hakan ne sakamakon riko da tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a), sai dai kuma ya kiraye su da kada irin wadannan nasarorin da suka samu su sanya su ji-ji-da-kai da cewa sun sami komai don kuwa akwai gagarumin aiki a gabansu. Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan har muka kwatanta kanmu da lokacin dagutu, to lalle muna iya cewa mun sami gagarumin ci gaba. Amma idan har muka kwatanta kanmu da irin fata da kuma ci gaban da Musulunci yake so mu samu, to a nan kan ko shakka babu akwai tazara a tsakaninmu da wannan yanayin. Jagoran dai ya ce ana iya cimma hakan ta hanyar riko da kuma aiki da abubuwan nan guda uku da ya yi bayaninsu a baya, wato dogaro da Allah, dogaro da karfin mutane da kuma yarda da kai.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Koyarwar Imam, wadda take cikin jawabansa da kuma wasiyyar da ya bari, ita ce dai ta mayar da al’ummar Iran wacce ta ci gaba ainun zuwa ga wata al’umma ma’abociyar ci gaba da kuma ‘yancin kai.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mutanen da suke ambaton sunan Imam da kuma ikirarin riko da tafarkin Imam, wajibi ne su zamanto masu imani da ‘taswirar hanyar Imam’, don ta hanyar riko da wadannan koyarwar tasa ne za a iya fahimtarsa da kuma jingina kai gare shi.

Yayin da yake magana kan koyarwar Imam a bangaren siyasar cikin gida, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana dogaro da mutane, tabbatar da hadin kan al’umma, girmama mutane da kuma nesantar almubazzaranci a bangaren jami’an gwamnati, girmama maslahar kasa a kan maslaha da kashin kai da kuma aiki tukuru wajen ciyar da kasa gaba a matsayin koyarwar marigayi Imam din a fagen siyasa ta cikin gida.

Dangane da siyasar waje kuwa, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Tsayin daka wajen tinkarar siyasar tsoma baki da mulkin mallaka ta ‘yan kasashen waje, tabbatar da ‘yan’uwantaka a tsakanin al’ummar musulmi, kyautata alaka da dukkanin kasashen duniya in banda wadanda suka zare takubbansu a kan al’ummar Iran, fada da sahyoniyawa, gwagwarmaya wajen ‘yanto Palastinu da kuma taimakon raunana wajen fada da azzalumai, wadannan su ne tushen siyasar waje cikin koyarwar marigayi Imam Khumaini.

A bangaren al’adu kuwa Jagoran ya bayyana: nesantar al’adar lalata ta kasashen yammaci, nesantar daskarewar tunani, nesantar riya cikin riko da addini, goyon bayan kyawawan halaye da hukunce-hukuncen Musulunci da kuma fada da watsa alfasha da fasadi a cikin al’umma, a matsayin koyarwar Imam a bangaren al’adu.

Dangane da bangaren tattalin arziki kuwa, Jagoran ya bayyana: dogaro da tattalin arziki na kasa da dogaro da kai, yin adalci cikin abubuwan da ake samarwa da kuma raba su tsakanin al’umma, ba da kariya ga marasa galihu, fada da al’adar jari hujja, girmama hakkin mallaka da zuba jari da aiki da kuma tabbatar da ‘yanci na tattalin arziki, a matsayin tushen koyarwar Imam a fagen tattalin arziki.

Don haka sai Jagoran ya ce: Fatan da Imam yake da shi a koda yaushe a wajen jami’an gwamnati, shi ne tsayawa kyam wajen aiwatar da wadannan koyarwar ta hanyar amfani da hankali da kuma basira.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabo batun zaben shugaban kasar mai matukar muhimmanci da za a gudanar nan gaba ne inda ya yi ishara da wasu batutuwa da ya wajaba a kula da su.

Ayatullah Khamenei ya bayyana zaben a matsayin abubuwan da suke tabbatar da wadannan abubuwa guda uku da Imam ya yi amanna da su da ya yi bayaninsu a baya inda ya ce: Zabe alama ce ta yarda da Allah, don kuwa kamata ya yi a dauke shi a matsayin wani nauyi da ke wuyan mutum da ya shafi makomar kasa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Har ila yau zabe wata alama ce ta yarda da mutane, don kuwa ta hanyar zabe ne mutane za su zabi shugabanni da jami’ansu. Kamar yadda kuma Jagoran ya bayyana zaben a matsayin alama ta yarda da kai, don kuwa duk wata kuri’a da mutum zai kada tana a matsayin yin tarayya ne cikin ayyana makomar kasa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samar da gagarumin yunkuri na siyasa da kuma shigowar mutane a cikin fage a matsayin lamari mai matukar muhimmanci cikin zaben inda ya ce: Duk wata kuri’a da mutane za su kada wa daya daga cikin wadannan ‘yan takara takwas din, a matakin farko kuri’a ce ga Jamhuriyar Musulunci da kuma yarda da shi kansa zaben.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da kokarin makiya na lalata wannan zabe da kuma mai she shi a matsayin wata barazana ga wannan tsari na Musulunci na Iran, Jagoran cewa ya yi: Wadannan mutane dai suna fatan ganin ko dai a gudanar da zabe ba tare da wani armashi ba ko kuma idan ma an gudanar din to su haifar da fitina bayansa kamar yadda ya faru a shekara ta 2009. To sai dai makiyan sun yi kuskure, don kuwa ba su fahimci al’ummar Iran ba sannan kuma sun mance da ranar 9 ga watan Dey (ranar da al’ummar Iran suka fito kwansu da kwarkwatansu wajen tabbatar da goyon bayansu da tsarin Musulunci bayan fititar da ta faru a shekara ta 2009 bayan zaben shugaban kasar).

Jagoran ya ci gaba da cewa: Cikin yardar Allah sannan kuma sabanin abin da makiya suke so, insha Allahu wannan zaben zai zamanto wata dama ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Makiya dai suna zaton cewa mafi yawan al’ummar Iran suna adawa da tsarin Musulunci ne, alhali kuwa sun mance da irin gagarumar fitowar da al’umma suka yi a ranar 22 ga watan Bahman inda bayan gushewar shekaru 34 da nasarar juyin juya halin Musulunci amma haka mutane suka fito kan tituna don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da kuma rera taken ‘Allah Ya La’anci Amurka’.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da kokarin makiyan al’ummar Iran na kashe gwuiwar al’umma ta hanyar farfagandar karya da rashin adalci da nufin hana su fitowa zaben, Jagoran cewa ya yi: A ina ne a duniya ake ba wa ‘yan takara, sanannun cikinsu da ma wadanda ba a sansu ba, damar yakin neman zabe a kafafen watsa labarai na kasa daidai wa daida.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A Amurka da kasashen ‘yan jari hujja, idan har dan takara ba memba ba ne a manyan jam’iyyu biyu zuwa uku sannan kuma bai sami goyon bayan masu kudi da cibiyoyin sahyoniyawa ba, to kuwa babu yadda zai sami damar yakin neman zabe ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana doka a matsayin abar komawa a lokacin zabe a Iran inda ya ce: A Jamhuriyar Musulunci, abin da ke da iko a fagen zabe, ita ce doka. A bisa doka ce wasu za su shigo fagen zaben wasu kuma ba za su sami damar shigowa ba kamar yadda masu tantance ‘yan takaran ma suna gudanar da ayyukansu ne bisa doka.

Jagoran ya ci gaba da cewa makiya ‘yan kasashen waje sun rufe idanuwansu kan wannan hakikar, da kuma yada farfaganda ta karya, wanda abin bakin cikin shi ne cewa wasu ma a cikin gida suna ci gaba da nanata wadannan abubuwan da suke fadi. Don haka ne Jagoran ya ce da yardarm Allah al’ummar Iran za su bada wa makiya kasa a fuska ta hanyar fitowarsu lokacin zaben.

Har ila yau a bangaren zaben dai, Jagoran ya gabatar da wasu wasiyyoyi ga ‘yan takaran zaben shugaban kasar. Inda ya ce: yana da kyau ‘yan takara masu girma su yi adalci wajen sukan wasu tsare-tsaren da aka gudanar a baya, sannan sukan da za su yi su zamanto wani kokari ne na magance matsalolin da ake fuskanta. Kamar yadda kuma ya kiraye su da su guji fadin maganganu da alkawurran da suka san cewa ba za su cika su ba. Har ila yau kuma Jagoran ya sake yin watsi da kokarin da kafafen watsa labaran kasashen yammaci suke yi na nuna cewa shi ne wuka shi ne nama a zaben na Iran da kuma kokarin da wasu suke yi na nuna cewa yana goyon bayan wani dan takara guda inda ya ce babu wani dan takaran da yake goyon sai dai zai yi bayanin irin siffofin da ya kamata a ce dan takara yana da shi wanda hakan wani nauyi ne da ke wuyansa.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook