A+ R A-
25 May 2020

Jagora Ya Kada Kuri’arsa A Zaben Shugaban Kasa Da Na Kananan Hukumomi Na Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ‘yan mintoci bayan bude rumfunar zaben shugaban kasar Iran karo na 11 da kuma zaben ‘yan majalisun kananan hukumomi karo na 14, ya fito Husainiyar Imam Khumaini (r.a) don kada kuri’arsa a yayin wannan zaben a akwati mai lamba 110 da aka ajiye a Husainiyar.

Jim kadan bayan kada kuri’ar tasa, Jagoran ya gana da manema labarai da suka taru a wajen don amsa wasu daga cikin tambayoyin da suke da su. Jagoran ya bayyana fitowar al’ummar Iran a kan lokaci sannan kuma kwansu da kwarkwatansu don zaban shugaban kasar da kuma ‘yan majalisar a matsayin lamari mai matukar muhimmanci inda ya ce: Wajibi ne al’ummar Iran su fito cikin shauki don kada  kuri’arsu, don kuwa makomar wannan kasar da kuma sa’ada da farin cikin al’ummar Iran, yana hannun fitowarsu da kuma kada kuri’arsu ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin bakar farfagandar da makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma al’ummar kasar suke yi a matsayin dalilin da ya sanya fitowa wannan zaben yake da muhimmanci da kuma tasirin gaske inda ya ce: Makiya sun yi iyakacin kokarinsu ta hanyar amfani da masanansu da kuma kafafen watsa labarai wajen ganin sun kashe wa mutane gwiwan kada su fito zaben. A fili ‘yan siyasa da sauran ‘yan amshin shatan makiya suke fadin maganganu da kuma gudanar da ayyukansu wajen ganin sun dushe hasken wannan zaben.

Yayin da ya ke magana kan maganganun da wasu jami’an Amurka suke fadi na cewa su dai ba su yarda da zaben Iran ba, Jagoran cewa ya yi: Ra’ayi da mahangar makiya dai ba su da wani muhimmanci a idon al’ummar Iran. A koda yaushe al’ummar Iran su ne suke zaban abin da suka ga ya dace da su, sannan kuma a ina ne maslahar kasarsu take. Bisa wannan mahangar ce suke zabe kuma za su ci gaba da yi.

Yayin da yake amsa tambayar dangane da sakon da ke cikin fitowar da ya yi a farko farkon lokaci da kuma kiran da yake da shi ga al’ummar Iran kan hakan, Ayatullah Khamenei ya kirayi al’ummar ne da su fito don farko-farkon lokaci kada su bari sai lokaci ya kure musu. Har ila yau kuma Jagoran ya kiraye su da su yi iyakacin kokarinsu wajen zaban dan takaran da ya dace ta hanyar gudanar da binciken da suka yi inda ya ce: Babu wani hatta iyalaina da suka san ga wa zan kada kuri’a ta, don haka wajibi ne a kan al’umma su gudanar da bincike kan dan takaran da za su zaba musamman dangane da zaben shugaban kasa.

Yayin da ya koma kan masu gudanar da zaben kuwa, Jagoran ya kiraye su da su kiyaye amana wajen gudanar da ayyukansu inda ya ce: Kuri’un mutane dai amana ce sannan kuma hakki ne na al’umma a wuyan masu kula da akwatunan zaben. A saboda haka wajibi ne a rike wannan amanar da kyau.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook