A+ R A-
22 January 2020

Imam Khamenei Ya Rantsar Da Sheikh Hasan Ruhani A Matsayin Sabon Shugaban Iran

A wani gagarumin bikin da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) a yammacin yau asabar (3-8-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya rantsar da Hujjatul Islam wal muslimin Dakta Hasan Ruhani a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

A cikin takardar rantsarwar, wadda Hujjatul Islam wal muslimin Muhammadi Golpaygani, shugaban ofishin Jagoran ya karanta, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi lokacin zaben shugaban kasar da aka gudanar a matsayin wata alama da ke tabbatar da sanin ya kamata na siyasa da al'ummar suka da shi bugu da kari kan riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, yarda da tsarin Musulunci da suke da ita. Jagoran ya kara da cewa: A yayin wannan zaben al'ummar Iran sun mayar wa makiyansu, wadanda suka amfani da duk wani karfi na siyasa da farfaganda wajen kashe musu gwiwa, kakkausan martani.

A jawabin da ya yi a wajen wannan taron, Ayatullah Khamenei ya bayyana irin mika mulki tsakanin gwamnatoci cikin ruwan sanyi ba tare da tashin hankali da ke gudana a Iran a matsayin wani lamari mai muhimmanci wanda kuma ya samo asali ne daga tsarin demokradiyya na addini da ke gudana a kasar Iran.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da rashin iko da fadi a ji da mutane suke da shi a lokacin mulkin kama-karya na ‘ya'yan gidan sarautar Pahlawi da kuma kafin nan a kasar Iran, Jagoran cewa ya yi: Albarkacin nasarar juyin juya halin Musulunci ne al'ummar Iran suka dandani dadin tsarin demokradiyya na al'umma, sannan kuma albarkacin Musulunci aka mayar da al'amurra hannunsu.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da rawar da mutane suke takawa cikin dukkanin lamurra masu muhimmanci na gudanar da kasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Tsawon shekaru 34 da suka gabata (bayan nasarar juyin juya halin Musulunci) a kowace shekara akan gudanar da zabe guda a kasar Iran inda mutane suke ba da tasu gudummawar wajen gudanar da kasarsu.

Har ila yau kuma Jagoran ya yi nuni da irin kyakkyawar alaka da ke tsakanin mutane da jami'an gwamnati wanda ya ce ba shi da tamka a duk fadin duniya. Jagoran ya yi ishara da irin gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a lokacin jerin gwanon Ranar Kudus ta duniya da aka gudanar a duk fadin kasar Iran inda ya ce: A irin wannan tsananin zafin rana sannan kuma cikin azumi, amma haka al'umma suka fito kan tituna don nuna goyon bayansu ga koyarwar juyin juya halin Musulunci da kuma matsalar Palastinu. Kamar yadda kuma yayi ishara da irin fitowar da al'ummar Iran din suke yi a lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman don nuna farin cikinsu da ranar da juyin juya halin Musulunci ya sami nasara a matsayin wani lamari da ke tabbatar da kyakkyawar alakar da suke da ita da jami'an gwamnati da kuma tsarin Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Marigayi Imam Khumaini (r.a) shi ne ya share wa al'ummar Iran wannan tafarki da ke cike da albarkoki, sannan kuma ya zuwa yanzu al'ummar Iran suna ci gaba da riko da wannan tafarkin da dukkan karfinsu. A nan gaba ma, cikin yardar Allah za su ci gaba da riko da shi.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana shugabanci a tsarin Musulunci a matsayin riko da wani nauyi ne na kokari da kuma yin hidima ba kama hannun yaro wa al'umma. Don haka ne ya kirayi jami'ai da sauran al'ummar Iran da su nemi taimakon Ubangiji wajen gudanar da ayyukan ciyar da kasar Iran gaba da kuma magance matsalolin da ake fuskanta.

Ayatullah Khamenei ya kirayi sabon shugaban kasar da kuma ‘yan majalisar ministocinsa da su ba da himma da kuma dukkanin kokarinsu wajen magance wa al'umma matsalolin da suke da su, kamar yadda kuma ya kiraye su da su guzuri ayyukan gaggawa.

Har ila yau yayin da ya ke magana kan irin kiyayyar da makiya musamman Amurka suke nuna wa al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Kamar yadda mai girma shugaban kasa yayi ishara da takunkumi da kiyayyar da makiya suke nuna wa al'ummar Iran wadanda suka haifar da matsaloli ga al'ummar, to amma kuma akwai kwarewa da darussan da ake samu cikin hakan. Don haka sai ya kirayi jami'an gwamnati da su ba da himma wajen amfanuwa da irin karfin na cikin gida da ake da su da kuma karfafa su wanda yace hakan zai taimaka wajen rage matsin lambar ‘yan kasashen wajen.

Yayin da ya ke magana kan amfani da hikima cikin alaka ta kasa da kasa da kuma lamurra na siyasa da sabon shugaban kasar ya yi ishara da shi cikin jawabinsa, Jagoran ya bayyana goyon bayansa ga hakan sai dai kuma yace abin bakin cikin shi ne makiyan al'ummar Iran din mutane ne wadanda ba kasafai suke riko da tafarkin amfani da hankali ba. Jagoran ya kirayi jami'an sabuwar gwamnatin da su yi dukkanin abin da za su iya wajen samun yardar Ubangiji cikin ayyukansu.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wasu makiyan tun ranar farko ta nasarar wannan juyi a fili suka sanar da cewa manufarsu ita ce ganin bayan juyin da kuma kifar da tsarin Musulunci, to amma bayan gushewar shekaru 34, ba wai kawai ba sun gaza wajen girgiza wannan tsarin ba ne face ma dai sun gaza wajen hana shi ci gaba ma. Don haka sai ya kirayi dukkanin jami'an gwamnatin da su hada kansu waje guda don ciyar da kasar Iran gaba.

Har ila yai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin zaluncin da yahudawan sahyoniya suke yi wa al'ummar Palastinu bisa goyon bayan manyan ma'abota girman kan duniya inda ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da riko da tafarkin da take kai ba tare da la'akari da kiyayyar makiya ba.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da sabon shugaban kasar Sheikh Hasan Ruhani ya gabatar da nasa jawabin inda ya yi karin haske kan ayyukan da gwamnatin tasa za ta sa a gaba.

Har ila yau a wajen bikin dai, ministan cikin gida na Iran Mustafa Muhammad Najjar ya gabatar da rahoto kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar da kuma irin fitowar da al'ummar Iran suka yi a lokacin zaben.