A+ R A-
28 February 2020

Jagora: Idan Iran Tana Son Kera Makamin Nukiliya, Amurka Ba Za Ta Iya Hana Ta Ba

A safiyar yau Asabar (16-02-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun-dubatan mutanen garin Tabriz don tunawa da yunkurin 29 ga watan Bahman na mutanen Tabriz a shekarar 1356. A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin wannan ganawar, Jagoran ya yi karin haske kan maganganun jami'an gwamnatin Amurka dangane da batun tattaunawa da Iran da kuma shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, kamar yadda kuma ya sake jinjinawa al'ummar kasar Iran sakamakon fitowar da suka yi ranar 22 ga watan Bahman don tunawa da ranar da juyin juya halin Musulunci na kasar ya yi nasara da kuma batun rikicin da ya faru a majalisar shawarar Musulunci ta kasar.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da tsayin dakan al'ummar Iran da kuma rashin mika wuyansu ga matsin lambar ma'abota girman kan duniya ciki kuwa har da takunkumin da aka sanya musu yana mai cewa dalilin hakan shi ne imani da Allah da suke da shi. Daga nan kuma sai ya ce: Wadannan mutane tun wasu watannin da ya suka gabata suka fara aiki da takunkumin da suke kiransu da sunan masu gurguntarwa, kai hatta 'yan kwanaki kafin ranar 22 ga watan Bahman sun sake sanya wasu sabbin takunkumin don su kashe wa al'ummar Iran gwiwa. To amma amsar al'ummar Iran a gare su ita ce irin fitowar da suka yi a lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman sama da na shekarun da suka gabata.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekarar, mutane sun fito daga ko ina sannan kuma cikin karfin gwiwa da kuma fuskokin da suke cike da farin ciki da annashuwa. Hakan kuma lamari ne da ya sake bayyanar da hakikanin yanayin al'ummar Iran. Jagoran ya bayyana irin wannan fitowar da al'umma suke yi a matsayin wani gagarumin bugu ga makiya al'ummar Iran.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jinjinawa da kuma gode wa al'ummar Iran saboda wannan fitowar da suka yi a ranar 22 ga watan Bahman din.

Haka nan kuma yayin da ya ke karin haske kan yanayin da ake ciki a halin yanzu, Jagoran cewa ya yi: Makiya suna cikin fushi ne sakamakon wannan imani da azama da kuma jaruntaka da hakuri na al'ummar Iran, don haka ne suke yin abubuwan da suka saba wa hankali.

Ayatullah Khamenei ya bayyana jami'an gwamnatin Amurka a matsayin wadanda maganganu da ayyukansu suke cin karo da juna inda ya ce: Amurkawa dai suna fatan sauran al'ummomi za su mika kai ga irin wadannan maganganu na su da suka saba wa hankali da kuma son amfani da karfi ne, kamar yada wasu mutane suka mika musu kai. To amma al'ummar Iran da kuma Jamhuriyar Musulunci ba masu mika kai ba ne, don kuwa suna da karfi, hankali da kuma tsayin daka.

Yayin da ya ke karin haske kan irin wadannan ayyuka na Amurka da 'yan amshin shatansu na kasashen yammaci da suka saba wa hankali, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Suna cewa sun yi amanna da hakkokin bil'adama sannan kuma suna daga tutar kare hakkokin bil'adama a duniya. Amma a aikace su ne suka fi cutar da hakkokin bil'adama a duniya kamar yadda suka aikata a gidajen yarin Guantanamo da Abu Ghraib da kuma kisan gillan da suke yi wa al'ummomin kasashen Afghanistan da Pakistan wanda yake a matsayin gagarumin take hakkokin bil'adama.

Wani lamarin kuma da Ayatullah Khamenei ya kawo da ke nuni da karo juna da ke cikin maganganu da kuma ayyukan Amurkawan shi ne ikararin fada da makaman kare dangi da suke yi inda ya ce: Ta hanyar fakewa da wannan ikirari na su ne suka kai wa kasar Iraki hari shekaru 11 da suka gabata, to amma daga baya ya tabbata cewa babu gaskiya cikin wannan ikirari na su.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk da wannan ikirarin da suke yi, to amma sai ga shi suna ci gaba da goyon bayan haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa wacce take da makaman kare dangi sannan kuma take ci gaba da yi wa sauran kasashe barazana.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kawo ikirarin da Amurkan take yi na yada demokradiyya a duniya a matsayin daya daga cikin maganganun Amurkawan da suke karo da ayyukansu inda ya ce: A bangare guda suna wannan ikirarin, amma a daya bangaren kuma a koda yaushe suna ci gaba da fada da Iran wacce take gudanar da mafi bayyanar tsarin demokradiyya a wannan yankin nan.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A daidai lokacin da Amurkawa suke da'awar kare demokradiyya, amma sai ga shi suna goyon bayan wasu kasashen yankin nan da ko kamshin demokradiyya ma ba su shaka ba, sannan kuma al'ummominsu koda sau guda ba su taba tsayawa a gaban akwatunan zabe don kada kuri'arsu ba.

Batu na gaba da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya tabo da ke nuni da karo da juna cikin maganganu da ayyukan Amurkawan shi ne tayin zama teburin tattaunawa da Iran da suka gabatar da nufin magance matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu inda ya ce: Amurkawa suna gabatar da wannan batun ne a daidai lokacin da suke ci gaba jingina wasu maganganu marasa tushe ga Jamhuriyar Musulunci da kuma ci gaba da yi musu matsin lamba da kuma sanya takunkumi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da jawabin baya-bayan nan da shugaban Amurka ya yi na kokarin da yake kasarsa tana yi wajen hana Iran kera makaman kare dangi inda ya ce: Idan da a ce Iran tana da niyyar kera makaman kare dangi, to kuwa Amurka ba ta isa ta hana al'ummar Iran yin hakan ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ta da niyyar kera makaman nukiliya, hakan kuwa ba wai saboda rashin amincewar da Amurka take nunawa ba ne, face dai hakan ya ginu ne bisa imani da akidar da take da ita na cewa makaman nukiliya cutarwa ce ga bil'adama. A bisa wannan akidar ce take son ganin an kawar da makaman nukiliyan a duniya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Da'awar Amurkawa na cewa Iran tana shirin kera makaman nukiliya, wani magudi ne cikin magana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Dangane da batun nukiliyar kasar Iran, lamarin ba shi batun kera makamin nukiliya ba. Abin da suke so shi ne hana Iran hakkin da take da shi na tace sinadarin uranium da kuma amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya. Tabbas ba za su sami nasarar hana al'ummar Iran ba. Al'ummar Iran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta karkashin hakkin da take da shi.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Kokarin take hakkokin al'ummar Iran wata bayyananniyar alama ce da take tabbatar da rashin hikimar Amurkawa. A saboda haka ba za a taba dogaro da batun hikima wajen mu'amala da mutumin da babu ruwansa da hikima sai dai son amfani da karfi ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsawon shekaru 34 da suka gabata Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin lamurra daban-daban na duniya ta fahimci da wa take fada sannan da kuma yadda ya kamata a yi mu'amala da shi.

Yayin da ya koma kan batun tayin tattaunawar da Amurka ta gabatar wa Iran ta kuma yadda Amurka ta ke amfani da kafafen watsa labaran da suke karkashin ikonta da kuma yahudawan sahyoniya wajen wasa da hankalin al'ummomin duniya da kuma na Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Kafafen watsa labaran duniya ba sa gaya wa duniya mahangarmu ko kuma idan ma har za su fadi to wani bangaren suke fadi ko kuma ma su juya abin da muka fadi din.

Har ila yau a ci gaba da karin haske kan wannan batu na tattaunawa, Jagoran ya yi ishara da wasu abubuwa guda biyar masu muhimmanci da suka hada da:

Rashin hikima da kuma karo da juna da ke cikin maganganu da kuma ayyukan jami'an Amurkan, kokarin Amurkawa wajen sanya al'ummar Iran su mika musu wuya a matsayin asalin manufar wannan tattaunawar, hakikanin ma'anar tattaunawa a mahangar masu tinkaho da karfi ‘yan mulkin mallaka, yaudara da kuma karyar da ke cikin maganganun Amurkawa na cewa za su dage wa Iran takunkumi idan aka fara tattaunawar da kuma hikimar da cikin mahangar al'ummar Iran da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan wannan tayin tattaunawa da Amurka ta gabatar.

Ayatullah Khamenei ya bayyana asalin manufar Amurka na gabatar da tayin tattaunawar a matsayin wata farfaganda da kuma bayyana wa duniya cewa al'umma da kuma gwamnatin Iran sun mika wuya ga bukutunsu inda ya ce: Suna so ne su nuna wa al'ummar musulmi na yankin nan cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk kuwa da tsauri da kuma tsayin dakan da ta yi daga karshe dai ta zo teburin sulhu da tattaunawa. A saboda haka ku ma ba ku da wata mafita face dai ku mika kai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Koda yake wadannan ‘yan mulkin mallakan tun da jimawa suke ta kokarin janyo Iran zuwa ga teburin tattaunawa, a halin yanzu ma dai wannan manufar suke son cimmawa ta hanyar gabatar da batun ‘tattaunawar da ba ta shafi manyan batutuwa ba'. To amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ido a bude tana iya fahimtar manufarsu, sannan kuma za ta mayar musu da martani daidai da wannan manufar.

Jagoran ya bayyana cewar ma'anar hakikanin tattaunawa a wajen Amurka da sauran kasashen yammaci ita ce yarda da maganganunsu a lokacin da ake tattaunawar. Daga nan sai ya ci gaba da cewa: Da irin wannan mahanga da ta saba wa hankali suke fadin cewa za mu tattaunawa kai tsaye don Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya da tace uranium. To amma idan da da gaske tattaunawar suke so, abin da ya kamata su ce shi ne za mu tattaunawa don Iran ta gabatar da hujjoji da dalilan da take da su, don a magance matsalar da ta kunno kai cikin adalci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da tambayar cewa da irin wannan mahanga ta Amurka da fatan da take da shi na cewa al'ummar Iran za ta mika kai, idan har gwamnatin Iran ta amince da tattaunawar, shin wannan tattaunawar za ta amfane ta sannan kuma shin za a cimma wani abu?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Shekaru 15 din da suka gabata, sau biyu zuwa uku Amurkawa suka gabatar da batun tattaunawa suna masu cewa wajibi ne a tattauna din kan wasu batutuwa da suka gabatar. Wasu jami'an gwamnati sun tafi sun tattauna da su. Amma daga lokacin da suka rasa abin da za su fadi da kuma tinkarar maganganun da Iran ta gabatar, nan take suka dakatar da wannan tattaunawar, amma suka tafi suna cewa Iran ce da dakatar da tattaunawar.

Jagoran ya ce shin bayan irin wannan abin da muka gani din, akwai wata bukatar kuma mu sake tusa kanmu wajen da za mu sake ganin wannan rashin hankali na Amurkawan?

Ayatullah Khamenei ya bayyana farfagandar da Amurkawan suke yadawa dangane da dauke takunkumin da suka sanya wa Iran a lokacin da aka fara tattaunawar a matsayin alkawarin karya yana mai cewa: Suna zaton cewa al'ummar Iran suna tsoron wadannan takunkumin ne a saboda daga sun ji wannan alkawarin, nan take za su mika kai ga tattaunawa da Amurka sannan kuma za su ji gaba da matsa wa jami'an gwamnati lamba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A hakikanin gaskiya wannan alkawarin yana daga cikin maganganunsu na yaudara ne sannan kuma lamari ne da ke nuni da cewa ba suna son tattaunawa ta hakika ba ne, face dai abin da suke so shi ne al'ummar Iran su mika musu wuya. Alhali kuwa idan da al'umar Iran suna son mika musu wuya, to da tun farko ma ba su juyin juya hali ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Manufar wadannan takunkumi, kamar yadda suka sha fadi, shi ne gajiyar da al'ummar Iran da kuma raba su da wannan tsari na Musulunci. A saboda haka, koda a ce za a tattaunar amma sai ya zamana al'ummar Iran ba su mika wuyan ba da kuma ci gaba da neman hakkokinsu, to takunkumin za su ci gaba da wanzuwa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai ya bayyana cewar al'ummar Iran mutane ne da suke son rayuwa cikin jin dadi da nishadi, to amma ba a shirye suke su yi watsi da hakkinsu da manufofinsu saboda samun wannan jin dadin ba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an kasar da su yi kokarin kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu da kuma nesantar duk wani abin da zai haifar da rikici a tsakaninsu wanda ba abin da zai haifar in ban da faranta wa makiya rai da kuma cutar da kasa da al'ummar Iran.

Daga Shafin Jagora

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook