A+ R A-
26 May 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Fitar Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Ayatullah Khoshvaqt

A yau Laraba (20-2-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatullah Hajj Sheikh Azizullah Khoshwaqt daya daga cikin manyan malamai, masana Ubangiji na Iran.

Abin da ke biye fassarar sakon Jagoran ne:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Cikin tsananin bakin ciki da alhini, na samu labarin rasuwar malami masanin Allah da kuma neman kusaci ga Ubangiji Madaukakin Sarki, marigayi Ayatullah Agha Hajj Sheikh Azizullah Khoshwaqt (yardar Allah ta tabbata a gare shi). Rayuwa da ke cike da albarka, wacce kuma take cike da neman kusaci da Allah da tsarkake zuciya tare da kama hanyar isa ga Allah Madaukakin Sarki, bugu da kari kan kokari maras tamka wajen tarbiyyantar da kai, wani bangare ne na rayuwar wannan malami mai tsarkake zuciya sannan da kuma kyawawan halaye. Ko shakka babu rashin wannan babban bawan Allah, ga wadanda suka san matsayinsa, lalle abin bakin ciki ne, sannan kuma gagarumin rashi ne ga dalibansa da kuma masu amfana da dimbin ilimi da kyawawan halayensa.

A saboda haka ina isar da sakon ta'aziyyata ga iyalansa masu girma da ‘ya'yansa abin girmamawa da sauran ‘yan'uwansa da dukkanin masoyansa. Haka nan kuma ina roka masa gafara da rahama ta Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma tashi tare da Waliyan Allah.

Sayyid Ali Khamenei
2, Esfanda, 1391
(20/02/2013)

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook