A+ R A-
29 February 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Gana Da Shugaban Kasar Pakistan Asef Ali Zardari

A yammacin yau Laraba (27-2-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari da ‘yan tawagarsa da suka kawo masa ziyarar ban girma. A yayin wannan ganawar Jagoran ya bayyana cewar mafi yawa daga cikin matsalolin da al'ummar musulmi suke fuskanta matsaloli ne da makiyan Musulunci suka tsara musu su yana mai cewa: rayar da irin karfi da kwarewa na dan'adam da kuma albarkatun kasa da duniyar musulmi take da su, za su iya taka gagarumar rawa wajen magance wadannan matsalolin.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana karfafawa da kuma fadada alakar da ke tsakanin kasashen musulmi a matsayin lamari na biyu mai muhimmanci da zai iya magance matsalolin da al'ummar musulmi suke fuskanta inda ya ce: haifar da rarrabuwa da sabani a tsakanin al'ummar musulmi na daga cikin ayyuka da tsare-tsare sahyoniyawa da sauran ma'abota girman kai da ko shakka babu cikin hakan.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin al'ummomin kasashen Iran da Pakistan, Jagoran ya bayyana cewar: Lalle mu dai mun yi imanin cewa wajibi ne a karfafa alaka ta tattalin arziki, siyasa, zamantakewa da tsaro tsakanin kasashen biyu.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas tsakanin Iran da Pakistan a matsayin misali mai muhimmanci da ke nuni da irin alakar da ke tsakanin Iran da Pakistan. Sannan kuma yayin da ya ke ishara da irin adawar da makiya suke nunawa irin wannan kyautatuwar alaka da ake samu tsakanin kasashen biyu, Jagoran ya ce: wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen ketare wannan adawa da suke nunawa.

Jagoran ya bayyana samun hanyar lamunce samun makamashi a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske ga kowace kasa ciki kuwa har da kasar Pakistan yana mai cewa: A wannan yankin dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kasa daya tilo da take da irin wannan lamuni na makamashi, don haka a shirye mu ke mu lamunce wa kasar Pakistan makamashin da take bukata.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kokarin haifar da rarrabuwa da sabani na mazhaba a kasar Pakistan a matsayin wata cuta da ‘yan kasashen waje suka shigo da ita kasar yana mai cewa: A hakikanin gaskiya kashe-kashe na mazhaba da ke faruwa a Pakistan lamari ne mai sosa rai. A saboda haka wajibi ne a yi fada da hakan da dukkan karfi don kada ya haifar da matsala cikin hadin kai na kasa na kasar Pakistan.

Daga karshe Jagoran ya bayyana cewar: Muna fatan gwamnatinku za ta sami nasarar karfafa hadin kai na mazhaba da kabilu da kuma ci gaban kasar Pakistan.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Pakistan din Asef Ali Zardari ya bayyana farin cikinsa da wannan ganawar yana mai cewa: Na yi amanna da kyautata alaka tsakanin kasashen nan biyu.

Shugaban kasar Pakistan ya ci gaba da cewa: Kokarin da wasu kasashen duniya da kuma na yankin nan suke yi wajen hana karfafuwar alaka tsakanin Iran da Pakistan wani aikin baban giwa ne, don kuwa al'ummomi sun fahimci yadda za su yi fada da makiyan Musulunci.

Mr. Zardari ya bayyana kokarin haifar da yakin basasa a cikin kasar Pakistan a matsayin makircin makiyan kasar yana mai cewa: Albarkacin addu'oinku, lalle ba za mu taba bari su aiwatar da wannan makirci na su ba.

Daga Shafin Jagora