A+ R A-
26 May 2020

Jagora Imam Khamenei: Bishiyoyi Da Shuke-Shuke Albarka Ce Ga Kowace Al'umma

A daidai lokacin da aka fara gudanar da bukukuwan makon dabi’a da kuma ranar shuka bishiyoyi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da hantsin yau Litinin (5-3-2013) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya shuka wasu bishiyoyi guda biyu.

A lokacin da ya ke gabatar da gajeren jawabi jim kadan bayan shuka bishiyoyin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana bishiyoyi da shuke-shuke a matsayin wata albarka ga kowace kasa da kuma gungun jama’a. Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da muhimmancin da Musulunci ya ke ba wa batun shuka bishiyoyi da kuma kula da su, bugu da kari kan kiyaye sare su, ya bayyana cewar: Korafin da muke da shi a kan jami’an da lamarin bishiyoyi da shuke-shuke yake hannunsu shi ne irin yadda ake sare daruruwan bishiyoyi a wajajen da bai kamata a ce an sare su ba.

Har ila yau Jagoran ya nuna damuwarsa kan yadda wasu masu hannu da shuni suke share wasu yankuna da gonaki da suke wajen gari don gina dogayen binaye don samun riba, yana mai cewa sare irin wadannan bishiyoyin yana barazana da kyawun yanayi da zamantakewa na wadannan garuruwa.

Jagoran dai ya kirayi dukkanin jami’an gwamnati da su yi kokari wajen hana faruwar irin wadannan ayyuka na kuskure da suke haifar da matsaloli ga jama’a.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook