A+ R A-
05 December 2021

Ayat. Gorgani: Hukumcin Kisa A Kan Sheikh Al Nimr, Kokarin Kawar Da Malamai Ne

Ayatullah Sayyid Aliwi Gorgani, daya daga cikin maraja'an birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da bukatar yanke hukumcin kisa a kan fitaccen malamin nan na kasar Saudiyya Ayatullah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr da mai shigar da karar kasar Saudiyyan ya bukaci wata kotun kasar ta yi.

Ayatullah Gorganin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar don nuna damuwarsa dangane da wannan lamarin da kuma ci gaba da takurawa mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da gwamnatin Saudiyyan take ci gaba da yi.

Yayin da ya ke magana kan batun bukatar yankewa wa Sheikh Al Nimr hukumcin kisan da mai shigar da karar ya bukata, Ayatullah Sayyid Alawi Gorgani ya bayyana cewar: Na san cewa ma'abota girman kai ne suka yi wa sarakunan Saudiyya shiftar hakan a kokarin da suke yi na ganin bayan malaman Musulunci sannan kuma masu kare addinin Allah, wato Musulunci.

Daga nan sai Ayatullahin ya ce: A saboda haka ina Allah wadai da hakan da kuma kiran musulmi da sauran masu neman 'yanci na duniya musamman musulmin kasar Saudiyya da su nuna rashin amincewarsu ga gwamnatin Saudiyyan.

A makon da ya wuce ne dai bayan kimanin watanni takwas na tsare shi, mahukuntan kasar Saudiyyan suka gabatar da Sheikh Nimr Baqir Al Nimr a gaban wata kotun binciken ayyukan ta'addanci da ke birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya. A wannan lokacin ne mai shigar da kasar ya gabatar da zargi kimanin bakwai a kan Sheikh Nimr da suka hada da kokarin tada fitina a yankin Qatif, neman taimakon kasashen waje da kuma goyon bayan yunkurin al'ummar kasar Bahrain, don haka ya bukaci kotun da ta yanke wa shehin malamin dan shekaru 55 a duniya hukumcin kisa, lamarin da ya ke ci gaba da fuskantar Allah wadai daga ciki da kuma wajen kasar Saudiyyan.