A+ R A-
25 May 2020

Amsoshin Ayat. Khamenei da Ayat. Sistani Dangane Da Batun Sanya Safa Ga Mace Da Sauransu

Abin da ke biye amsoshin da Ayatullah Sayyid Ali Khamenei (Jagoran juyin juya halin Musulunci) da kuma Ayatullah Sayyid Ali Sistani suka bayar ga tambayoyin da aka gabatar musu ne dangane da abin da ya shafi sanya safa ga mata da kuma batun rufe kafafunsu da dai sauransu.

 

Tambaya: Shin ya halalta mace ta bar kafafunta a waje?

 

Amsa:

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei: Hakan ba ya halalta. Wajibi ne ga mace ta rufe dukkanin jikinta in ban da fuska da tafukanta.

Ayatullah Sayyid Ali Sistani: Wajibi ne mace ta rufe dukkanin kafafunta daga idanuwan baki (wadanda ba muharramanta ba).

 

Tambaya: Shin wajibi ne mace ta rufe kafafunta ta hanyar sanya safa ko kuma idan ta rufe su da hijabin (abaya ko rigar) da take sanya da shi ya wadatar?

 

Amsa:

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei: Wajibinta dai shi ne rufe dukkanin kafafunta.

Ayatullah Sayyid Ali Sistani: Wajibi ne ta rufe dukkanin kafafunta daga idanuwan mutumin da ba muharraminta ba, shin da safa ne ko kuma ta hanyar sauke hijabi ko rigarta a kan kafar da yadda kafafun ba za su fito ba. Haka nan kuma wajibi ne ta rufe dukkanin jikinta da abin da ba a kirga shi a matsayin ado in ban da fuska da tafukanta.

 

Tambaya: Mene ne hukuncin rashin sanya safa?

 

Amsa:

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei: Ba ya halalta mace ta fitar da wani bangare na kafafunta waje.

Ayatullah Sayyid Ali Sistani: Abin da yake wajibi a kan mace shi ne rufe kafafunta daga idanuwan mutanen da ba muharramanta ba.

 

Tambaya: Akwai safunna masu launin fatar mutum wadanda suke zama ado ga kafa, shin ya halalta budurwa ta sanya su?

 

Amsa:

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei: Ita kanta wannan safar ba ta da matsala a kan kanta, idan har ba a kirga hakan a matsayin ado sannan kuma ba za ta janyo hankulan mutanen da ba muharramai ba gare ta.

Ayatullah Sayyid Ali Sistani: Hakan ya halalta a gare ta, to amma idan har ana kirga hakan a matsayin ado, wajibi ne ta rufe ta daga idanuwan wadanda ba muharramai ba.

 

Tambaya: Shin ya halalta ga mace ta sanya budadden takalmi (sandal da makamantansa) ba tare da sanya safa ba sannan kuma ta fita waje?

 

Amsa:

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei: Ba ya halalta ga mace ta fitar da wani bangare na kafafunta.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook