A+ R A-
25 May 2020

Ayatullah Makarem Shirazi Ya Bayyana Tsananin Damuwarsa Dangane Da Rikici Da Zubar Da Jinin Da Ke Faruwa Tsakanin Musulmi

Ayatullah Sheikh Nasir Makarem Shirazi, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shia da ke zaune a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da yadda musulmi suke zubar da jinin junansu a kasashe daban-daban na musulmi yana mai kiran musulmin da su yi taka tsantsan dangane da makircin makiya da suke son rarraba kansu don cimma manufofinsu.

Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da malaman kasar Azarbaijan da suka kai masa ziyara inda ya ce: Makiyan Musulunci suna tsoron ranar da musulmi za su hada kansu waje guda ne. A saboda haka ne suke kokarin wajen haifar da fitina da sabani da mummunan zato tsakanin musulmin.

Sheikh Makarem Shirazi ya kara da cewa: Matukar dai musulmi suka hada hannayensu waje guda, to kuwa za su iya zama wata al’umma madaukakiya sannan kuma ma’abociyar karfi.

Har ila yau yayin da ya ke ishara da cewa Musulunci dai wani addini ne mai karfi sannan kuma ma’abocin koyarwa mai girman gaske, Ayatullah Makarem Shirazi ya yi fatan al’ummar musulmi za su hada kansu waje guda don cimma manyan manufofinsu.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan irin yanayin da wasu kasashen musulmi suke ciki, Ayatullah Makarem Shirazi cewa ya yi: Abin bakin cikin shi ne cewa idan aka kalli kasashen musulmi za a ga yadda dan’uwa musulmi yake fadawa dan’uwansa musulmi, suna ci gaba da lalata kasashensu. Tushen hakan kuwa su ne makiyan musulmin.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan fagen aikin hajji babban marja’in ya bayyana cewar: Hikimar aikin hajji ita ce tabbatar da cewa al’ummar musulmi na duniya tamkar wata tsintsiya madaurinki guda ne. A saboda haka wajibi ne a karfafa wannan koyarwa da kuma tabbatar da cewa babu wani bambanci na kan iyaka tsakanin al’ummar musulmi.