A+ R A-
23 October 2019

Ayatullah Subhani: Ahlulbaiti (a.s) Su Ne Mafi Kyawun Hanyar Da Za Ta Hada Kan Musulmi Waje Guda

Ayatullah Jaafar Subhani, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shia da ke zaune a birnin Qum ya bayyana cewar Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) su ne mafi kyawu da kuma muhimmancin hanyar da za ta hada kan musulmi waje guda saboda tarayyar da suka yi cikin girmama su da kuma matsayi na musamman da suke da shi a wajensu.

Ayatullah Ja’afar Subhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a yayin ganawa da masu shirya taron kara wa juna sani kan Imam Sajjad (a.s) da suka kai masa ziyara inda ya ce Alkur’ani mai girma ya kirayi al’ummar musulmi da su yi riko da igiyar Allah mai karfi inda ya ce: Al’ummar da kanta yake rarrabe tamkar mutumin da  ya fada cikin rijiya wanda kuma yake neman wata igiyar da zai rika wacce za ta fitar da shi daga mutuwa. A saboda haka ne Allah Madaukakin Sarki ya umurci musulmi da su yi riko da wannan igiyar.

Ayatullah Subhani ya ci gaba da cewa: Lalle Ahlulbaiti (a.s) suna daga cikin mafiya muhimmancin abubuwan da musulmi suka yi tarayya kansu sannan kuma hanyar da za ta hada su waje guda. Saboda kuwa Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kasance abin girmamawar dukkanin musulmi in ban da nasibai.

Babban marja’in ya kara da cewa: Hakika tsawon tarihi an jarrabci musulmi da rarrabuwa da rikici da sabani a tsakaninsu, to amma tarihi bai taba ganin irin bakar farfangadar da wahabiyawa suke yi a kan Shi’anci a wannan lokacin ba, tsawon tarihi.

Ayatullah Subhani ya ci gaba da cewa: Shekaru aru aru kenan ‘yan Shi’a suke zaune lafiya tare da ‘yan’uwansu ‘yan Sunna a mafi yawa daga cikin kasashen musulmi irin su Iraki da Labanon, to amma nasarar da juyin juya halin Musulunci ya samu a kasar Iran ya sanya masu tsaurin ra’ayi cikin ‘yan Sunnan da jin tsoron cewa hakan zai haifar da yaduwar da Shi’anci a duniya. Don haka ne wasu kasashen suka ware makudan kudade wajen fada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.