
Ayatullah N. Hamedani: Amurka Da Sahyoniyawa da Salafawa Masu Kafirta Musulmi Ba Za Su Iya Dakatar Da Yaduwar Musulunci Na Hakika Ba
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Marajaai
- Hits: 3234

Ayatullah Noori Hamedani, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shia da ke zaune a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana cewar lamarin Ghadir ya shata tafarkin Wilaya ne don nesantar da bil’adama daga bata yana mai cewa Imam Ali (a.s) shi ne mutumin da ya fi cancantar halifanci bayan Ma’aikin Allah (s.a.w.a).
Ayatullah Noori Hamedani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ma’aikatan ma’aikatar tsaro na Iran inda ya ce Amurka da sahyoniyawa da salafawa da masu kafirta al’ummar musulmi ba za su taba iya hana yaduwar Musulunci na hakika ba.
A wani bangare na jawabin nasa, babban marja’in ya bayyana Idin Ghadir a matsayin babban idin al’ummar musulmi yana mai cewa: Ko shakka babu lamarin Ghadir ba wani lamari ne da za a wuce shih aka kawai ba, don kuwa wata hanya da kuma tafarki ne ga bil’adama a dukkanin zamunna. Saboda rana ce da Manzon Allah (s.a.w.a) ya nada halifansa a bayansa sannan kuma ya biya wa bil’adama daya daga cikin bukatun da yake da su.
Ayatullah Noori Hamedani ya ce dan’adam dai yana da zabi a rayuwarsa ta duniya kamar yadda kuma yake da bukatu da sha’auce-sha’auce daban-daban inda ya ce: Daga cikin mafiya muhimmancin bukatun dan’adam ita ce bukatar da yake da ita zuwa ga shugaba da kuma jagora. Saboda shi mutum a dukkanin rayuwarsa yana a mararraba ce tsakanin gaskiya da karya, don haka a koda yaushe mutum yana bukatar wanda zai ceto shi da kuma shiryar da shi zuwa ga madaidaicin tafarki.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da riwayoyin da suke nuni da wajibcin samuwar shugaba ga bil’adama, Ayatullah Hamedani ya bayyana cewar: Wasu riwayoyin sun jaddada cewa duniya ba za ta taba rabuwa da hujja ba, zai ci gaba da kasantuwa matukar dai akwai mutum a bayan kasa. Don haka ne ma mutumin karshe da za a dau ransa shi ne Hujjar Allah kuma Imami.
Ayatullah Noori Hamedani ya kara da cewa: Duk wanda ya saba wa tafarkin Ghadir hakika ya kauce wa hanya. Wajibi ne a yi riko da kuma biyayya ga jagororin Musulunci tun daga Manzon Allah (s.a.w.a) zuwa ga Imamai (a.s) har zuwa ga Waliyul fakih a wannan zamani na mu wanda kuma ake kirga hakan a matsayin ci gaban wannan tafarki.