A+ R A-
08 December 2023

Ayatullah Safi Golpaygani: Idin Ghadir Wata Hakika Ce Ta Addinin Musulunci Da Sauran Saukakkun Addinai

Ayatullah Lutfullah Safi Golpaygani, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shia dake zaune a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar idin Ghadir wata hakika ce ta addinin Musulunci da sauran saukakkun addinai yana mai cewa saukakkun addinai (na Ubangiji) ba za su cika ba in ba tare da wilayar Amirul Muminin (a.s) ba.

Ayatullah Golpaygani ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin yayin ganawarsa da manyan jami’an dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran a birnin Qum inda yayin da ya ke magana kan lamarin Ghadir Khum, muhimmancinsa da kuma wajibcin ci gaba da raya shi inda ya ce: Duk wani abin da muka yi wajen raya wannan rana mai girma da aka kira ta da babban idi, lalle kadan ne. Wajibvi ne mu kara kokari wajen sanar da duniya wannan idi mai girma wanda ya ke a matsayin hakikanin Musulunci da sauran saukakkun addinai.

Ayatullah Golpaygani ya kara da cewa: Idin Ghadir yana nuni ne da matsayin Shi’anci da kuma addinin Musulunci a yanayi na gaba. A saboda haka wajibi ne dukkanin ‘yan Shi’a da kuma masu kaunar Ahlulbaiti (a.s) su ba wa wannan idin muhimmanci na musamman da kuma raya shi ta hanyar gudanar da bukukuwa da tarurruka.