A+ R A-
08 December 2023

Ayat. Makarem Shirazi Ya Ja Kunnen Saudiyya Kan Zartar Da Hukumci Kan Sheikh al-Nimr

Ayatullah Sheikh Nasir Makarem Shirazi, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shi’a da ke birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayi kakkausar suka kan hukumcin kisa da wata kotun kasar Saudiyya ta yanke wa fitaccen malamin Shi’a na kasar Ayatullah Allamah Sheikh Nimr Bakir al-Nimr yana mai jan kunnen mahukuntan Saudiyyan da cewa wajibi ne su san cewa zartar da irin wannan hukunci zai kara irin kyamar da ake yi mata da kuma fushin ‘yan Shi’a da Sunna ma’abota ‘yanci.

Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi yau din nan asabar (18-10-2014) inda ya bayyana wannan hukuncin da cewa hukunci ne na zalunci. Ayatullah Makarem Shirazi ya ci gaba da cewa: Sheikh al-Nimr bai aikata wani abin da ya cancanci wannan hukumcin ba.

Ayatullah Makarem Shirazi ya ci gaba da cewa: Abin bakin ciki ne yadda ‘yan Shi’an kasar Saudiyya suke fuskantar matsin lamba mai girman gaske da hana su gudanar da ayyukansu na ibada kamar yadda kuma aka hana su mafi karancin hakkokinsu da kuma hana su gudanar da wasu ayyukan na gwamnati.

Har ila yau kuma Shehin malamin ya soki siyasar nuna wariya da Amurka da sauran kungiyoyi na kasa da kasa masu ikirarin kare hakkokin bil’adama yana mai cewa: A duk lokacin da aka aka dauki wani mataki kan wata batacciyar kungiya a Iran, nan take za ta ka ‘yan majalisar Amurka suna kumfan baki, amma sai ga shi sun yi gum da bakinsu kan irin zaluncin da ake yi wa ‘yan Shi’a a kasar Saudiyya da hana su mafi kashin hakkokinsu. Sheikh Makarem Shirazi ya ci gaba da cewa: Wannan yana nuni da rashin gaskiya wannan ikirari da suke yi na kare hakkokin bil’adama.

Daga karshe Ayatullah Makarem Shirazi ya ja kunnen kasar Saudiyyan da cewa ba za ta ji ta dadi ba matukar ta zartar da hukuncin kisa a kan Sheikh al-Nimr.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Ashura

Takaitaccen Bayani K...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook