A+ R A-
08 December 2023

Na’ibin Shugaba Majalisar Koli Ta ‘Yan Shi’an Labanon Ya Bukaci A Sako Sheikh al-Nimr

Mataimakin shugaban majalisar koli ta ‘yan Shi’an kasar Labanon Sheikh Abdul’amir Qabalan ya kirayi malaman duniyar musulmi da su yunkura da kuma yin dukkanin abin da za su iya wajen ganin an sako Sheikh Nimr Bakir al-Nimr, fitaccen malamin Shi’a na kasar Saudiyya da kuma ganin ba a zartar da hukumcin kisan da aka yanke masa ba, don kuwa hakan zai iya maganin fitinar da za ta iya kunno kai tsakanin musulmi.

Sheikh Qabalan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a yau din nan asabar (18-10-2014) a wajen wani taron malamai a birnin Beirut babban birnin kasar Labanon inda ya kirayi sarkin Saudiyya Abdullah bn Abdul’aziz da ya soke wannan hukumci na kisa da aka yanke wa Sheikh al-Nimr da kuma ba da umurnin a sako shi.

Har ila yau mataimakin shugaban majalisar koli ta ‘yan Shi’an na Labanon ya kirayi shugabannin kasashen larabawa da su dinga mu’amala ta kwarai da ‘yan’uwantaka da al’ummominsu yana mai bayyana Sheik al-Nimr da cewa babban malami ne masani.