
Maraja’ai Da Malaman Addini Na Iran Sun Ja Kunnen Saudiyya Kan Zartar Da Hukumcin Kan Sheikh Al-Nimr
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Marajaai
- Hits: 3924

Manyan maraja’ai da sauran malaman addini na kasar Iran na ci gaba da tofin Allah tsine ga kasar Saudiyya dangane da hukuncin zalunci da wata kotu ta yanke wa babban malamin ‘yan Shi’a na kasar Sheikh Nimr Bakir al-Nimr suna masu jan kunnen Saudiyya dangane da abin da ka iya biyo baya matukar aka zartar da wannan hukumcin.
A nasa bangaren Ayatullah Ja’afar Subhani, daya daga cikin manyan maraja’an Shi’an da ke zaune a birnin na Qum, yayi tofin Allah tsine ga wannan hukuncin yana mai cewa bai kamata sarakunan Saudiyya su yi zaton cewa lamarin zai tsaya kawai ga nuna rashin amincewa ba ne, face dai kowane digon jinin wannan malami zai zamanto wata guguwa ce da za ta girgiza turakan da tushen sarautar Saudiyyan.
Shi ma a nasa bangaren Ayatullah Sayyid Muhammad Alawi Gorgani cikin wata wasika da ya fitar ya bayyana cewar duk da cewa shahada a tafarkin fada da zalunci da dawagitai wani abin alfahari ne ga dukkanin malamai da kuma ‘yan Shi’a, to amma abin bakin cikin shi ne irin mu’amalar da mahukuntan Saudiyyan suke yi da ‘yan kasarsu ba tare da girmamawa ba.
Ayatullah Gorgani ya kara da cewa a daidai lokacin da na ke Allah wadai da wannan hukunci, har ila yau kuma na yi amanna da cewa babu abin da irin wannan hukuncin zai haifar in ban da raunana matsayin Al Sa’ud a yankin nan da kuma tsakanin al’ummar Saudiyyan. Yana mai cewa wannan hukuncin dai ko da wasa ba zai hana mutanen Saudiyya ci gaba da neman hakkokinsu ba.
Shi ma a nasa bangaren Ayatullah Noori Hamedani, daya daga cikin manyan maraja’n Shi’a na birnin Qum, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi Allah wadai da wannan hukumci na zalunci yana mai jan kunnen mahukuntan Saudiyyan da cewa irin wannan hukuncin ba abin da zai haifar in ban da sosa zukatan ‘yan Shi’a na duniya. Don haka ya ce babu wani abin da ya saura ga mahukuntan Saudiyyan face ta amince da bukatun al’ummar kasar.
Shi ma Ayatullah Safi Golpaygani, daya daga cikin manyan maraja’an birnin na Qum ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da wannan hukumcin da mahukuntan Saudiyyan suka yanke wa Sheikh Nimr Bakir al-Nimr din.
Ayatullah Safi Golpaygani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban ofishin shugaban kasar Iran wanda ya kai masa ziyara inda ya ce lalle wannan hukunci da aka yanke wa wannan babban malami dan gwagwarmaya babban abin bakin ciki ne, saboda babu wani abin da ya aikata da ya cancanci wannan hukumcin. Don haka sai ya bukaci ministan harkokin wajen Iran da ya dauki dukkanin matakan da suka dace kuma cikin gaggawa wajen isar wa mahukuntan Saudiyyan sakonnin malaman na Iran da kuma Allah wadai din su kan wannan hukunci na zalunci.
Shi ma a nasa bangaren, Ayatullah Ka’abi, daya daga cikin membobin majalisar kwararru ta Jagoranci ta Iran ya yi kakkausar suka ga wannan hukunci inda ya ce an yanke wa Sheikh al-Nimr hukunci ne ba tare da ya aikata wani ba face dai sai saboda fadin gaskiya da kuma neman hakki.