A+ R A-
08 December 2023

Sakon Ayatullah Makarem Shirazi Ga Paparoma Francis, Shugaban Mabiya Darikar Katalika Ta Duniya

Mai Girma Paparoma Francis – Shugaban ‘Yan Darikar Katolika Ta Duniya

Bayan sallama da gaisuwa:

A baya-bayan nan wasu jami’an fadar Vatican sun bukaci malaman duniyar musulmi da su dau mataki da bayyana matsayarsu dangane da hare-haren dabbanci da ‘yan kungiyar takfiriyya ta Da’esh (ISIS) suke kai wa kiristoci da sauran ‘yan tsiraru mabiya sauran addini a arewacin kasar Iraki.

Kai ma da kanka ka rubuta wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya sako inda ka bukace shi da ya yi amfani da dukkan dama da karfin da ya ke da shi wajen kawo karshen irin wannan kisan gillan da ake yi wa Kiristoci da ‘yan tsiraru mabiya sauran addinai.

A daidai lokacin da nake maraba da wannan shawara taka, ina ganin duk wata alaka da aiki tare tsakanin shugabannin addinai daban-daban na duniya da nufin tseratar da bil’adama a matsayin wani lamari da ya zama wajibi. Tabbas ina Allah wadai da wadannan hare-hare na dabbanci da rashin imani, sannan kuma ina kiran dukkanin musulmin duniya da su yi Allah wadai da wadannan ayyuka da suka saba wa ‘yan adamtaka. A saboda haka ina son sanar da kai wasu lamurra guda biyu:

1. A halin yanzu ‘yan Takfiriyya sun kasance mafi girmar barazana ga bala'i ga rayuwar bil’adama, ba tare da la’akari da addini da kasar da suka fito ba. Shekara da shekaru kenan muke magana kan wannan hatsarin. Shekaru ukun da suka gabata, a wata ganawa da na yi da mai girma shugaban majalisar malaman fadar Vatican na yi masa ishara da hatsarin kungiyoyin takfiriyya din inda na shaida masa cewa:

“Babu wani makon da ba zan yi Allah wadai da ayyukan wadannan ‘yan tsiraru masu tsaurin ra’ayi ba cikin jawaban da nake yi…bai kamata a dora alhakin ayyukan wadannan ‘yan tsirarru masu tsaurin ra’ayi a kan addinin Musulunci ba”.

Alkur’ani mai girma ya fadi cewa Manzon Musulunci rahama ce ga dukkanin bil’adama. To amma abin bakin cikin shi ne cewa da dama daga cikin shugabanni na siyasa da addinai na duniya, ba wai kawai sun yi tsit da bakunansu kan wannan danyen aiki ba ne, face ma wasu daga cikinsu suna goyon bayan hakan ne a aikace.

Idan ba don goyon baya da taimako na kudade da kayan aiki da makamai na wasu kasashen yammaci da gwamnatocin ‘yan amshin shatansu na yankin nan ba, da kuwa kungiyar Da’esh da makamantanta ba su sami damar ci gaba da wanzuwa da aikata wadannan danyen aiki da zubar da jinin da suke yi ba.

2. A bangare guda ina fatan ganin fadar Vatican a lokacin shugabancinka ta dau mataki da bayyanar da matsaya a fili kan irin zalunci da munanan ayyukan da ake yi da sunaye mabambanta, shin wannan zaluncin ana yinsa ne a kan kiristoci ‘yan tsiraru a kasashen musulmi ko kuma ga musulmi ‘yan tsiraru a kasashen yammaci da makamantan hakan.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba ka dacewa kai da abokan aikinka.

 

Nasir Makarem Shirazi