A+ R A-
08 December 2023

Ayat. M. Shirazi: Akidar Takfiriyya Ta Shafa Wa Musulunci Kashin Kaji A Lokacin Da Duniyar Take Kishirwar Musuluncin

Ayatullah al-Uzma Sheikh Nasir Makarem Shirazi, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shi’a da ke birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar duniya tana kishirwar Musulunci, to sai dai akidar takfiriyya ta shafa wa Musulunci kashin kaji. Don haka bayanin matsaloli kawai bai wadatar ba, face dai wajibi ne a binciko hanyar tumbuke wannan akidar daga tushe.

Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wajen bude taron kasa da kasa na fada da kungiyoyin ‘yan Takfiriyya masu kafirta musulmi a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce wajibi ne a hada hannu waje guda da musayen ra’ayi dangane da hatsarin da ke cikin tsaurin ra’ayi da akidar kafirta musulmi.

Ayatullah Makarem Shirazi ya ci gaba da cewa: A shekarun baya-bayan nan Musulunci ya fuskanci gagarumin zagon kasa da makirce-makirce mara tamka, lamarin da ya haifar da yakin basasa da ruguza garuruwa da wajajen tarihi na Musulunci a wadannan kasashe.

Sheik Makarem ya kara da cewa: An keta hurumin masallatai da kaburburan waliyan Allah sannan kuma an mai da dubun dubatan musulmi sun zamanto ‘yan gudun hijira mafiya yawansu mata da kananan yara, kamar yadda kuma aka keta hurumin da dama daga cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Don haka sai Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana tsananin damuwarsa inda ya ce: Abin bakin cikin shi ne cewa an ba wa makiya Musulunci wata dama ta bayyana Musulunci a matsayin wani addini maras tausayi da zubar da jinin mutane.

Yayin da yake magana kan ‘yan kungiyar takfiriyya ta Da’esh (ISIS) da kuma yadda masu adawa da Musulunci suka matsa wajen jingina su da Musulunci da kuma kiransu da daular Musulunci, Ayatullah Makarem Shirazi ya ce: Ba haka kawai masu adawa da Musulunci suka tsaya kyam wajen ci gaba da kiran ‘yan wadannan kungiya da sunan Daular Musulunci ba, don kuwa sun san cewa ita wannan kungiyar, batacciyar kungiya ce wacce ba ta Musulunci ba, don su sami damar yada farfaganda a kan Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa ba za a iya kawar da ‘yan wannan kungiya da karfi na makami ba, Ayatullah Makarem Shirazi ya ce: Wajibi ne dukkaninmu mu yi kokari, malaman Musulunci su hada hannunsu waje guda da tattaunawa kan akidun ‘yan takfiriyya da kuma gabatar da su don matasa da sauran al’umma su san inda aka sa gaba.

Har ila yau kuma yayin da yake karin haske kan akidar ‘yan takfiriyya din, Ayatullah Makarem Shirazi cewa: Wadannan mutane suna ganin duk wani wanda ba su ba a matsayin kafirin da ya wajaba a yake shi, sannan kuma matansa da dukiyarsa da mutumcinsa sun halalta a gare su, sannan kuma ba sa kasa a gwiwa wajen aikata duk wani aiki na ta’addanci wanda tunanin mutum ma ba zai kai gare shi ba.

Shehin malamin ya ci gaba da cewa: ‘Yan takfiriyya sun sanya wa kansu sunan Musulunci don su bakanta sunan Musulunci. Don haka Ayatullah Makarem ya ce: wajibi ne a binciko tushen wannan akidar da kuma bayyanar da shi ga al’umma.

Ayatullah Makarem Shirazi ya kara da cewa wajibi ne a yi fada da wannan akida ta masu kafirta musulmi ta hanyar binciko tushen akidarsu don kuwa fada da makami bai wadatar ba.