A+ R A-
08 December 2023

Ayatullah Sistani Ya Ki Amincewa A Fita Waje Da Matarsa Don Shan Magani

Wasu majiyoyi na kusa da babban marja’in duniyar Shi’a a kasar Iraki, Ayatullah Sayyid Ali Sistani, sun bayyana cewar Ayatullahi Sistanin ya ki amincewa da bukatar da wasu asibitoci na gwamnati da na masu zaman kansu a ciki da wajen Irakin suka gabatar masa na yi wa matarsa magani sakamakon matsanancin rashin lafiyar da take fama da shi.

Tashar talabijin din Al-Alam dake watsa shirye-shiryenta daga birnin Tehran ta jiyo wadannan majiyoyin suna cewa Ayatullah Sistani ya ki amincewa da wadannan bukatu yana mai jaddada cewa ya fi so ta ci gaba da shan magani a asibitin Al-Sadr da ke birnin Najaf inda take kwance sannan kuma a bangaren da sauran jama’a suke ba wai a wani waje na musamman ba.

Har ila yau tashar ta Al-Alam ta jiyo wasu likitocin asibitin na Al-Sadr suna fadin cewa a wata ziyarar da dan Sayyid Sistanin, wato Sayyid Muhammad Ridha Sistani ya kai asibitin don duba lafiyar mahaifiyar tasa, ya bayyana musu cewa: Lalle su dai sun yarda da likitocin da kuma ayyukansu, kamar yadda kuma ya isar da gaisuwar Sayyid Sistani ga likitocin, kamar yadda kuma ya shaida musu cewa Sayyid din yana adawa da nuna duk wani bambanci da fifiko tsakanin iyalin nasa da take kwance da sauran marasa lafiya.

A kwanakin baya ne dai mai dakin Ayatullah Sistani ta fuskanci rashin lafiyar hawan jini mai tsananin gaske lamarin da ya sanya aka kwantar da ita a asibitin.

A daidai lokacin da Ayatullah Sistanin ya ki amincewa da a fita da matar tasa waje don yi mata magani, a daidai lokacin da a bangare guda kuma yake daukar nauyin wasu marasa lafiyan marasa abin hannu wajen kai su kasashen waje don neman magani.