A+ R A-
05 December 2021

Hauzar Imam Jawad (a.s) A Karbala Ta Ja Kunnen Saudiyya Dangane Da Kokarin Cutar Da Malaman Shi'a Na Kasar

Makarantar hauzar Imam Jawad (a.s) da ke birnin Karbala mai tsarki na kasar Iraki, ta bayyana siyasar kokarin kawar da makaman addinin na yankin Gabashin kasar Saudiyya da gwamnatin kasar ta ke gudanarwa da kuma bukatar da mai shigar da kara na kasar ya yi na a yanke wa daya daga cikin malaman yankin Ayatullah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr hukumcin kisa a matsayin lamari mai hatsarin gaske, don haka suka ja kunnen mahukuntan Saudiyyan dangane da hatsarin da ke cikin hakan.

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Irakin, sun bayyana cewa makarantar Hauzar ta Imam Jawad (a.s) ta yi wannan kiran ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan inda ta yi Allah wadai da wannan siyasa ta kiyayya da gaba da nuna bambanci da mahukuntan Saudiyya suke gudanarwa a kan mabiyar tafarkin Shi'a na yankunan Gabashin kasar, suna masu jan kunnen gwamnatin dangane da abin da zai biyo bayan taba rayuwar fitattun malamai da fitattun masu fadi a ji na mabiya tafarkin Ahlulbaiti na yankin.

Har ila yau a cikin sanarwar, makarantar Hauzar ta Imam Jawad (a.s) ta bukaci al'ummar musulmi a kasashen musulmi sannan kuma musamman na yankunan gabashin kasar Saudiyya da su tsaya kyam cikin jaruntaka wajen kare wadannan malamai da fitattun mutane sannan kuma kada su sake yin shiru kan hakan.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan gurfanar da daya daga cikin fitattun malaman Shi'a a kasar Saudiyyan Ayatullah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr, a gaban wata kotu ne da kuma bukatar da mai shigar da kara na Saudiyyan ya gabatar wa kotun na a yanke masa hukumcin kisa, lamarin da ake ci gaba da yin Allah wadai da shi. Kamar yadda kuma a kwanakin baya ne gwamnatin kasar Saudiyyan ta sanar da kama wasu mutane 16 daga cikin fitattun 'yan Shi'an gabashin kasar da kuma wasu mutane biyu 'yan kasashen Iran da Labanon da ikirarin cewa wai suna gudanar da ayyukan leken asiri wa Iran a kasar, lamarin da malaman Shi'a na yankin da kuma iyalan mutanen da aka Kaman suka yi Allah wadai da shi da nuna rashin ingancin wannan ikirarin muhukuntan.

Masana dai suna ganin wadannan matakai da gwamnatin Saudiyya ta ke dauka cikin kwanakin nan daya ne daga cikin hanyoyin da suke bi wajen cutar da 'yan Shi'an kasar sakamakon yunkurin da suka yi na neman sauyi da kuma neman hakkokinsu a kasar bugu da kari kan kokarin da Al-Sa'ud suke yi wajen bakantawa da kuma shafa kashin kaji wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Ashura

Takaitaccen Bayani K...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook