A+ R A-
13 July 2020

Sayyid Nasrallah Wajen Taron Tasu’a: A Yau ‘Isra’ila Na Farin Ciki Saboda Kashe-Kashen Da Ke Faruwa A Duniyar Musulmi

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar a halin yanzu (haramtacciyar kasar) Israila tana cikin farin ciki dangane da abin da ke faruwa a kasashen musulmi da na larabawa na irin yake-yake da kashe-kashen da ke faruwa a tsakanin musulmi sannan kuma tana ci gaba da kwadaitar da hakan, kamar yadda ya ce ‘Isra’ila tana cikin bakin ciki saboda yiyuwar cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da manyan kasashen duniya (kasashen 5+1).

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen taron ranar Tasu’a (9 ga watan Muharram) a unguwar ‘Dhahiya’ na garin Beirut inda ya ce: Babbar manufar ‘Isra’ila’ a koda yaushe ita ce dukkanin kasashen da suke kewaye da ita su zamanto a rarrabe, rarrabuwa ta kabilanci da mazhaba don ta sami damar zama gwamnati mafi girma da karfi.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa bayan harin 11 ga watan Satumba haramtacciyar kasar Isra’ila ta shigo da dukkanin karfinta wajen sanya Amurka kai hare-hare kasashen yankin Gabas ta tsakiya. Ita ce ta sanya Amurka kai hari Iraki da mamaye kasar, yana mai cewa: ‘Isra’ila’ ita ce take tunkuda yankin Gabas ta tsakiya zuwa ga yaki, ba ta son ganin zaman lafiya ko kwanciyar hankalin yankin nan.

Har ila yau Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Haramtaciyar kasar Isra’ila tana cikin tsananin damuwa dangane da makomarta don kuwa babu tabbas cikinta saboda mai yiyuwa ne rikici ya balle a dukkanin yankin. Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana son ganin yankin Gabas ta tsakiya ya fada cikin yaki don ta zamanto cikin kwanciyar hankali da kuma kara irin karfin da take da shi. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Cikin ‘yan watannin baya-bayan nan haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da dukkanin karfinta wajen tunkuda Amurka wajen kai hari kasar Siriya.

 

Isra’ila Tana Cikin Fushi Saboda Yiyuwar Kulla Yarjejeniya Tsakanin Iran Da Kasashen 5+1

 

Haka nan kuma Sayyid Nasrallah ya ce: ‘Isra’ila’ tana cikin fushi dangane da yiyuwar cimma yarjejeniya tsakanin Iran da kasashen 5+1 (Rasha, China, Amurka, Birtaniya, Faransa da Jamus) kan shirin nukiliyanta tana mai cewa za ta yi amfani da dukkanin karfinta wajen hana faruwar hakan. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Amurka dai ba ta da karfin sake kirkiro wani sabon yaki. Irin kashin da Amurka take sha a duniya ya hana ta sake kaddamar da wani sabon yaki, to amma ‘Isra’ila’ tana son tunkuda ta zuwa ga hakan.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya ce aikin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya shi ne yaki da haifar da fitina sannan kuma wasu daga cikin kasashen larabawa suna tare da ita cikin hakan inda ya ce: ‘Isra’ila da kawayenta sun san cewa suna iya fara yaki, to sai dai suna da sanin cewa ba za su iya takaita shi a waje guda ba” don haka sai ya ce: wajibi ne al’ummomin kasashen larabawa musamman ma na Tekun Fasha su fahimci cewa yaki shi ne makwafin rashin cimma yarjejeniya tsakanin Iran da kasashen yammaci”.

Sayyid Nasrallah ya ce: Aikin Isra’ila a yankin nan shi ne yaki da lalata kasashe da haifar da rarrabuwa da fitina da yakin basasa da kuma kiran makiya ‘yan waje da su kaddamar da yaki a madadinta.

Shugaban kungiyar Hizbullah din ya ci gaba da cewa: Babban abin bakin ciki ne yadda wasu kasashen larabawa suka kasance sannan kuma har ya zuwa yanzu suna tare da Isra’ila cikin wannan manufa ta ta, su ma kamar Isra’ila ba sa son a magance rikicin Siriya ta hanyar siyasa wanda hakan ne zai kawo karshen zubar da jinni da lalata kasar. Kamar yadda kuma wasu daga cikin wadannan kasashen na larabawa suna tsananin adawa da cimma yarjejeniya tsakanin Iran da wadannan kasashen larabawan.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Har ila yau kuma babban abin bakin ciki ne yadda Netanyahu (firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila) ya zamanto kakakin wasu kasashen larabawan yana magana kan irin damuwar da suke ciki. Haka nan kuma babban abin bakin ciki ne mu ji Mrs Livni, tsohuwar ministar harkokin wajen ‘Isra’ila’ sannan a halin yanzu kuma minista a gwamnatin Netanyahu tana fadin cewa gwamnatin ‘Isra’ila’ ta sami wasiku da sakonni daga wajen wasu gwamnatocin larabawa da suke bukatar ‘Isra’ila’ da kada ta sassauto kan matsayartakan tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyan Iran. Shin wannan ba abin kunya ba ne? duk kuwa da cewa hakan ba wani sabon abu ba ne.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Mun ji irin wadannan kalaman a lokacin yakin shekara ta 2006, a tsakiyar yakin a lokacin da Isra’ilawa suna gaji sannan kuma shan kashinsu ya fara bayyana a fili, ita kanta wannan Livni ita ce take cewa, haka nan shi ma Olmert (firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila na lokacin) ya ce wasu daga cikin kasashen larabawa sun bugo mana suna kiranmu da cewa kada ku dakatar da wannan yaki na Labanon, saboda me? Saboda, abin kunya, nasarar kungiyar gwagwarmaya ta Labanon lamari ne mai bakanta ran wadannan shugabanni ‘yan amshin shata. Wannan ita ce hakikanin lamarin. Irin wadannan maganganu dai su ne muka ji su a lokacin yakin Gaza.

Jagoran kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa: Amurka dai ba ma’aikaciyar ‘Isra’ila’ ba ce ba kuma ta kawayenta na yankin nan ba ne ko kuma ‘yan amshin shatanta na yankin nan. Wa Amurka take wa aiki? Tana aiki ne wa kanta. ‘Isra’ila’ ce take aiki wa Amurka. Lalle wannan wani tunani ne da ke bukatar gagarumin kokari wajen gyara shi. ‘Isra’ila tana aiki ne wa Amurka. Amurka ita ce shugaba sannan kuma mai wuka da nama.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Mun dai ga abubuwan da suka faru cikin ‘yan makonnin da suka gabata, a lokacin da ‘Isra’ila’ da wasu kasashen larabawa suke kai gwauro su kai mari wajen ganin Amurka ta kai wa Siriya hari. Me ya hana Amurka kai wannan harin? Maslaharta, tsoron da take ciki da kuma irin abubuwan da suke dabaibaye ta. Don kuwa Amurka tana aiki ne saboda maslaharta.

 

Tsoma Bakin Amurka Cikin Lamurran Labanon:

 

A wani bangare na jawabin nasa, shugaban kungiyar Hizbullah din ya yi ishara da maganar sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a ziyarar da ya kai Saudiyya inda ya ce: (John) Kerry ya fadi wata magana wacce ma’anarta take nufin  cewa sun cimma yarjejeniya da jami’an kasar Saudiyya cewa ba za a taba barin Hizbullah ta ayyana makomar kasar Labanon ba. Na’am akwai wadansu a Labanon da suka yi farin ciki suna cewa lalle Amurkawa za su suna kan hanya. Wasu daga cikinsu idan har Amurkawa suka fadi magana, to ba za su iya barci ba, don haka suke zaton cewa hankalin Hizbullah zai tashi. To mu dai a wajen mu John Kerry ne ya fadi wannan maganar ko Obama kai ko ma waye a duniyar nan, hakan ba zai sauya komai ba, wato babu wani tasirin da zai yi. Magana ce wacce muka ji ta sannan ta wuce ta gefen kunnuwanmu.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Tun shekarar 1982 Amurka da ‘Isra’ila’ da ma wasu kasashen larabawa sun so su tsara makomar kasar Labanon da kuma yankin nan, amma ‘yan gwagwarmaya sun ruguza wannan tsari na su, Hizbullah kuwa wani bangare ne na wadannan ‘yan gwagwarmayar, sannan kuma suka tabbatar da tsarin da ‘yan gwagwarmaya suke so a Labanon da kuma yankin nan.

Sayyid Hasan Nasrallah ya ci gaba da cewa: Babu wani da ya isa ya kawar da wannan bangare na mu, haka nan mu ma ba ma son kawar da wani bangaren. Wannan shi ne yanayin kasar Labanon. Hakikanin lamarin dai shi ne cewa akwai bangarori biyu a Labanon, ba su da wani zabi face su binciko abubuwan da suka yi tarayya a kansu su yi aiki tare wajen ayyana makomar Labanon. Amurka ko John Kerry kai ko ma wani daga waje ne za su tsara makomar Labanon, ku din nan dai mutanen Labanon ku ne za ku tsara makomar kasarku.

Sayyid Nasrallah ya ce kasar Saudiyya ce ta hana a kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Labanon saboda tana zaton za a kawo karshen gwamnatin Siriya. Don haka ne ya ce duk wani da ya ke jiran a kifar da gwamnatin Siriya kafin a kafa gwamnati to kuwa ba za su sami nasarar kifar da gwamnatin Siriyan ba.

Har ila yau Sayyid Nasrallah ya ce a halin yanzu kuma wasu suna jiran tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da kasashen yammaci kan shirin nukiliyanta kafin a kafa gwamnatin don kuwa hakan zai sanya Iran ta yi watsi da Hizbullah din, don haka sai ya ce: Duk wanda ya san Iran sannan kuma ya san Hizbullah, ya san cewa Iran ba za ta taba bukatar Hizbullah da ta yi watsi da wajibi na kasa da ke kanta ba, koda kuwa tattaunawar ba ta ci nasara ba.

Sayyid Nasrallah ya ce: Koda kuwa tattaunawar ta kai ga yaki ne, to hakan lamari ne mai daga hankali ga kowa, to amma zai fi daga hankalin wasunmu. Idan kuma har an cimma wata yarjejeniya, to kuwa bangarenmu zai kara samun karfi ne. A saboda haka da me kuke jira?

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ce: Mu dai muna da manyan kawaye guda biyu su ne kuwa Iran da Siriya. Shin akwai wani lokacin da suka taba sayar da mu? Ko kuma akwai wani lokacin da suka taba yin watsi da mu? Shin akwai wani lokacin da Iran da Siriya suka yaudare mu ko suka kulla mana makirci? Ko da wasa. Don haka mun yarda da wadannan kawaye na mu.

Daga nan sai Sayyid Nasrallah ya ce: Amma ku din nan musakai, shin kuna son in kirga muka lokutan da kawayen naku suka yi watsi da ku? Sau nawa suka sayar da ku? Sau nawa suke kulla yarjejeniya su yi watsi da ku a tsakiyar hanya? Abin da ya faru cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan kan Siriya dai babban dalili ne da ke tabbatar da hakan.

Daga karshe dai Sayyid Nasrallah ya gode wa dukkanin wadanda suka halarci taron kamar yadda kuma ya kirayi al’ummar Labanon da su fito kwansu da kwarkwatarsu don raya ranar Ashura duk kuwa da barazanar da makiya suka yi na kawo hari inda ya ce babu wani abin da zai raba su da Imam Husain (a.s).

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook