A+ R A-
13 July 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Halarci Taron Juyayin Arba'in Na Imam Husain (a.s) A Husainiyar Imam Khumaini (r.a)

A safiyar yau Litinin (23-12-2013), wacce ta yi daidai da ranar Arba'in na shahadar Shugaban Shahidai Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) tare da mabiyansa, aka gudanar da taron juyayin arba'in din a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A yayin wannan taron wanda ya sami halartar Jagoran juyin juya halin Musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamenei tare da wasu manyan jami'an Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma gungun daliban jami'oin kasar, Hujjatul Islam wal muslimin Qasimiyan ne ya gabatar da jawabi inda ya tabo bangarori daban-daban na wannan yunkuri na Imam Husain (a.s) da kuma irin darussan da za a iya dauka cikin matakan da fursunonin yakin Karbala suka dauka wajen wayar wa mutane da kai kan hakikanin abin da ya faru a Karbalan.

Har ila yau kuma a wajen taron, mawakin juyayin Ahlulbaiti (a.s) Malam Muti'iy ne ya gabatar da wakokin juyayin abubuwan da suka faru a Karbalan ga Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a).

A karshen taron dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci mahalarta taron sallar azahar da la'asar inda bayan sallar ya gabatar da dan gajeren jawabi inda ya bayyana wannan taron a matsayin wani taro maras tamka da aka taba gudanarwa a wajen.

Daga karshe dai Ayatullah Khamenei ya yi adduoi da fatan alheri ga matasan da suka tarun da sauran matasa inda ya kiraye su da su shirya wa daukan gagarumin nauyin da ke wuyansu a matsayinsu na manyan gobe.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook