A+ R A-
22 February 2024

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran: Kasar Siriya Ba Ta Bukatar Taimako Na Sojoji Daga Kasashen Waje

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewar kasar Siriya ba ta bukatar wani taimako na sojoji daga kasashen waje, yana mai cewa taimakon da dakarun kare juyin na Iran suke ba wa sojojin Siriyan bai wuce taimako na shawarwari da kuma kwarewa ta soji wanda kuma ya samar da sakamako mai kyau tsawon rikicin Siriyan.

Manjo Janar Ja’afari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a yau din nan Litinin (21-04-2014) don tunawa da zagayowar shekarar da aka kafa dakarun kare juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce bisa la’akari da kasantuwar al’ummar Siriya a fage da kuma irin karfi na mutane da take da shi, don haka ba ta bukatar wani taimako na sojoji daga waje. Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya kara da cewa irin taimakon da dakarun nasa suke ba wa kasar Siriya bai wuce taimako a bangaren shawarwari da musayen kwarewa da aka samu ba.

Manjo Janar Ja’afari ya kara da cewa matsalar da kasar Siriya ta ke fuskanta a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon fushin da Amurka take yi da kasa saboda irin goyon bayan da take ba wa kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci ne. Don haka ne Amurkan take ba wa ‘yan ta’adda taimakon da suke bukata don cutar da al’ummar Siriyan. Don haka babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya kirayi al’ummar musulmin duniya da su sauke nauyin da ke wuyansu na taimakon al’ummar Siriya wajen fada da ‘yan ta’addan da aka shigo da su kasar.

Babban kwamandan dakarun kare juyin na Iran ya ci gaba da cewa duk wata kasar da ta daga taken gwagwarmaya irin na juyin juya halin Musulunci na kasar Iran da kuma riko da wannan tafarkin to kuwa za ta fuskanci irin wannan adawa daga gwamnatoci ma’abota girman kai kamar yadda yake faruwa a Labanon da Siriya da Masar da wasu kasashe na Musulunci da aka sami bulluwar farkawa ta Musulunci a can.

Manjo Janar Muhammad Ali Ja’afari ya ci gaba da cewa: Manyan makiyan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sansanin gwagwarmaya a kasashen musulmi su ne Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila wadanda suke ci gaba da nuna kiyayyarsu ta kowane bangare.