
Sojoji Sun Bude Wuta Da Kashe Da Kuma Raunana Masu Jerin Gwanon Ranar Kudus Ta Duniya A Birnin Zaria
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Latest
- Hits: 54728

Shafin Harkar Musulunci a Nijeriya ya bayyana cewar: A yau jummu'a ne daidai da 28 ga watan Ramadan wanda kuma ya zo daidai da Ranar Qudus ta duinya harkar musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaquob El-Zakzaky ta gabatar da muzaharar Ranar Qudus da ta saba gabatarwa yau fiye da shekaru 30 da suka gabata. Amma bayan an kammala muzaharar sai sojoji suka budewa mahalartan wuta ta bayan su, wanda kuma kawo ya zuwa yanzun wannan yayi sanadin shahadar sama da yan uwa ashirin sannan sama da 50 suka ji munanan raunuka.
Cikin wadanda suka yi shahada akwai 'ya'yan jagoran harkar musulunci a Nigeria su uku, Shaheed Sayyid Ahmad, Shaheed Sayyid Hamid da kuma Shaheed Sayyid Mahmud.
A yau Asabar 29 ga watan Ramadan bayan kwana daya da bude wuta da sojoji suka yiwa muzaharar lumana na tunawa da Ranar Qudus na duniya da ake gabatarwa a Jummu'ar karshe na watan Ramadan na ko wacce shekara, jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaquob El-Zakzaky ya gana da manema labarai don musu karin haske kan hakikanin abin da ya faru.
An fara wannan ganawa ne da safe yau Asabar da misalign karfe 10:00 na safe.
Manema labarai daga bangaren Radiyo, Talbijin da jaridu a baki dayan kasar sun halarta.
Tun da farko dai kafin soma tambayoyi daga manema labaran Malam ya gabatar da dajeren jawabi kan abubuwan da suka faru a jiya Jummu'a, da kuma ci gaban ta'addancin na sojoji daya ci gaba har zuwa yau Asabar.
A wani bangare na jawabin nasa Malam ya bayyana yadda aka kasha mutane a cikin ruwan sanyi, babu komai a hannun su.
Malam ya yi bayani game yayan sa uku Shaheed Ahmad, da Shaheed Hameed, wadan da duka suke jami'a a kasar China kuma basu dade da zuwa hutu ba, shi Shaheed Hameed ma kwanakin sa shida kacal da zuwa hutu aka kasha shi.
Haka nan Shaheed Mahmud wanda shi kuma yake karatu a Jami'ar Al-Mustafa dake Beirut shima yazo hutun karshen shekara ne kwanan nan.
Haka nan kuma a wani bangare na jawabin nasa Malam ya jawo hankalin manema labarai da yadda wasu ke bada labarain cewa an kwama ne tsakanin shi'ah da sojoji, Malam yace wannan rashin adalci ne, da farko dai an auka mana ne ba kwamawa aka yi ba, fiye da shekaru 30 muna wannan muzaharar kuma ana karewa lafiya, sannan kuma hatta a bana ma anyi wannan muzajhara a akalla birane 22 ciki har da Lagos da Fatakwal.
Sannan kuma tun da farko su sojojin sun aukawa jama'a ne mahalarta muzaharar Ranar Qudus ba yan shi'ah ba, domin kuwa muzaharar Ranar Qudus ta kunshi kowa da kowa bata takaitu ga al'ummar musulmi su kadai ba, a'a ta hada da mabiya addinin kirista, hatta da yahudawa.
Bayan kammala jawabin sa an baiwa manema labaran dama sun gabatar da tambayoyin su.
Source: www.harkarmusulunci.org