A+ R A-
28 February 2020

Sheikh Asad: Ayatullah Khamenei Bai Sauya Ra'ayi Da Fatawarsa Kan Haramcin "Tatbir" Ba

Shugaban bangaren larabci na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a birnin Qum, Sheikh Asad Muhammad Qasir, ya bayyana cewar koda wasa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei bai sauya fatawarsa kan haramcin ‘Tatbir’ (wato irin saran kai da wuka ko takobi da wasu ‘yan Shi’a suke yi a lokacin juyayin Ashura) ba, face ma dai ya kara tabbatar da haramcin hakan ne da kuma kiran mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da su nesanci hakan.

Sheikh Asad Qasir ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambaya kan wannan lamarin a shirin “Hukunce-Hukuncen Musulunci” da yake gabatarwa a tashar talabijin ta Alkauthar da ke watsa shirye-shiryen daga birnin Tehran na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce: “Na sami labarin wata magana da ake yadawa da kuma jingina ta ga wani malami na cewa ‘tatbir’ yana daga cikin alamu na addini da kuma cewa wai Ayatullah Khamenei ya sauka fatawarsa ta baya kan haramcin ‘tatbir’ din”. Don haka ina sake jaddada cewa Imam Khamenei (Allah ya kara masa tsawon rai) bai sauya ra’ayi da fatawarsa kan haramcin tadbir ba da kuma cewa hakan cin mutumcin addini ne da kuma raunana akidar Ashura.

Sheikh Asad Qasir ya kara da cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yana nan kan bakanta kan haramcin tadbir da ma kara tsanantawa kan haka sama da lokacin da ya fitar da wancan fatawar.

Shugaban bangaren larabci na ofishin Jagoran ya ci gaba da cewa: Ina kiran masu fasa kawukan na su da su fasa kan nasu wajen fada da makiyan al’ummar musulmi, makiyan addini, makiyan muminai, wadanda a halin yanzu suke barazana ga ababe masu tsarki na Musulunci.

Sheikh Asad Qasir ya cika da cewa: Kamata ya yi mu ba da dukkan jininmu, musamman a wannan lokaci, wajen kare ababe masu tsarki na Musulunci, Karbala, Najaf al-Ashraf da kaburburan Ahlulbaiti da sahabban Manzon Allah (s.a.w.a).

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook