A+ R A-
05 December 2021

Limamin Najaf: Saudiyya Ta Haka Kabarinta Da Kanta Bayan Hukumcin Kisan Sheikh al-Nimr

Limamin Juma’ar birnin Najaf mai tsarki na kasar iraki Sayyid Sadruddin al-Qabanchi ya bayyana cewar mahukuntan Saudiyya sun tafka gagarumin kuskure sakamakon hukumcin kisan da suka yanke wa Ayatullah Sheikh Nimr Bakir al-Nimr, fitaccen malamin Shi’a na kasar yana mai cewa Saudiyya ta ‘tona kabarinta ne da hannunta’ sakamakon wannan hukuncin.

Sayyid Qabanchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din a Husainiyar al-Fatimiyya da ke birnin na Najaf inda ya ce “ko shakka babu Saudiyya ta tafka babban kuskure sakamakon zaluncin da take yi wa malaman shi’a a kasar musamman ma bayan hukuncin kisan da aka yanke wa Sheikh al-Nimr.

Shehin malamin ya kara da cewa: Wannan hukunci na zalunci a kan Sheikh al-Nimr ya zo sakamakon neman ‘yanci da hakkokin ‘yan Shi’an kasar da yake yi , yana mai cewa Sheikh Nimr bait aba daukar makamai a kan gwamnatin Saudiyya ko kuma shirya mata juyin mulki na soji ba.

Sayyid Qabanchi ya ci gaba da cewa: Lalle ya kamata mahukuntan Saudiyya da malamansu wahabiyawa su san cewa ba za su tsira ba matukar suka tunzura ‘yan Shi’a, sannan kuwa su zauna cikin shirin fuskantar martanin da za a mayarsu wanda babu wani guda daga cikinsu da zai tsira. Sayyid Qabanci ya ci gaba da cewa; A halin yanzu an samu farkawa a kasar ta Saudiyya wacce ta samo asali daga wajen ‘yan Shi’an Ahlulbaiti, wanda hakan kuma zai haifar da gagarumin sauyin da zai tunmuke gidan sarautar Al Sa’ud.

A ranar Larabar da ta gabata (15-10-2014) ce wata kotun manyan laifuffuka a birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyyan, ta yanke hukumcin kisa a kan fitaccen malamin Shi’a na kasar Sheikh Nimr Bakir al-Nimr saboda abin da suka kira samunsa da laifin tunzura mutane su yi bore wa gwamnati da kuma kin bin umurnin sarki.