A+ R A-
05 December 2021

Na’ibin Limamin Tehran Ya Ja Kunnen Saudiyya Dangane Da Zartar Da Hukumcin Kisa Kan Sheikh al-Nimr

Na’ibin limamin juma’ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana hukumcin kisan da wata kotun kasar Saudiyya ta yanke wa fitaccen malamin Shi’an nan na Sheik Nimr Bakir al-Nimr da cewa zalunci ne tsagoronsa yana mai jan kunnen mahukuntan Saudiyya dangane da abin da zai biyo bayan zartar da wannan hukumcin.

Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan a masallacin Juma’ar birnin na Tehran inda ya bayyana tuhumar da ake yi wa Sheikh Nimr din a matsayin tuhumar zalunci. Ayatullah Khatami ya ce daga cikin tuhumar da ake yi wa Sheikh Nimr har da cewa wai me ya sa yake goyon bayan zanga-zangar nuna rashin amincewar da al’ummar Bahrain suke yi, sannan kuma me ya sa yayi imani da fikirar Wilayatul fakih da kuma cewa me ya sa yake fadin cewa mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suna da hakki su rayu a Saudiyya kamar sauran ‘yan kasa. Don haka ya ce dukkanin wadannan tuhumce-tuhumce, tuhumce-tuhumce ne marasa kan gado sannan kuma na zalunci.

Daga nan sai na’ibin limamin Juma’ar na Tehran ya ja kunnen mahukuntan Saudiyyan da cewa: Ina sanar da gwamnatin Saudiyya da cewa wannan lamarin ba kanwan lasa ba ne, don kuwa sakamako da abin da zai biyo bayan zartar da hukumcin kisa a kan wannan malamin addinin ga Saudiyyan ba karamin abu ba ne.

Haka nan kuma yayin da ya koma ga maganganun da ministan harkokin wajen Saudiyya Sa’ud Faisal ya yi kan Iran da bayyana ta a matsayin wani bangare na matsalar da yankin Gabas ta tsakiya yake fuskanta, Ayatullah Khatami ya bayyana cewa kasar Saudiyya ita ce ma babbar matsalar kasashen yankin Gabas ta tsakiya da na musulmi gaba daya ba ma wai wani bangare na matsalar ba.

Na’ibin limamin na Tehran ya kara da cewa: Waye ban san cewa da kudaden man fetur din ku ne aka kirkiro kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh (ISIS) ba? Sannan kuma waye bai san cewa da kudadenku irin na dan karuna ne ake zubar da jinin musulmin duniya a halin yanzu ba?

Ayatullah Khatami ya ci gaba da cewa: “Idan har kuna son sanin gaskiya, to ya kamata ku san cewa ku din nan ba wai ma wani bangare ne na matsalar da ake fuskanta ba, face ma dai ku ne dukkanin matsalar.

Ayatullah Ahmad Khatami ya kara da cewa: Lalle muna iya fahimtar dalilin wannan fushi na ku, saboda kuwa kun kasha biliyoyin daloli don kifar da gwamnatin kasar Siriya amma ku sha kashi. Haka nan kuma kashe miliyoyin daloli don cimma bakaken manufofinku a Iraki, a nan ma kun sha kashi.

A ranar Larabar da ta gabata (15-10-2014) ce wata kotun manyan laifuffuka a birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyyan, ta yanke hukumcin kisa a kan fitaccen malamin Shi’a na kasar Sheikh Nimr Bakir al-Nimr saboda abin da suka kira samunsa da laifin tunzura mutane su yi bore wa gwamnati da kuma kin bin umurnin sarki.

Ashura

Takaitaccen Bayani K...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook