A+ R A-
23 October 2019

Ministan Wajen Iran Ga Muftin Saudiyya: Akidar Mafi Yawan Musulmin Duniya Ta Yi Hannun Riga Da Ta Wahabiyanci

Ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif yayi kakkausar suka ga kalaman babban muftin kasar Saudiyya na kafirta al'ummar Iran inda ya ce ko shakka babu akidar mafiya yawan al'ummar musulmin duniya ta yi hannun riga da akidar wannan mufti da makamantansa da suka ginu wajen goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na Twitter a matsayin mayar da martani ga muftin kasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al ash-Sheikh inda ya ce: "Tabbas Musuluncin al'ummar Iran da na mafiya yawan al'ummar musulmin duniya ya bambanta da akidar wuce gona da iri wacce wannan babban malamin wahabiyyawa da jagororin ta'addanci na Saudiyya suke yadawa".

Kafin hakan dai babban muftin kasar Saudiyyan Sheikh Abdul Aziz Al ash-Sheikh ya shaida wa wata jaridar larabci cewa al'ummar Iran dai ba musulmi ba ne a matsayin mayar da martani ga sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aikewa mahajjatan bana.

A cikin sakon nasa dai Ayatullah Ali Khamenei yayi kakkausar suka ga yadda mahukuntan Sa'udiyya suke gudanar da sha'anin aikin hajji, kamar yadda kuma ya zargi hukumomin Sa'udiyya da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa dubbban alhazan da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya yayin turmutsutsin da ya faru ranar sallar bara a Mina lamarin da da dama suke zargin Saudiyyan da hannu cikin hakan.

A yayin wannan turmutsutsi na Mina din dai mahukuntan Saudiyyan sun yi ikirarin cewa kimanin mutane 770 ne suka rasa rayukansu alhali jami'an Iran da wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa kimanin mutane 4700 cikinsu kuwa da Iraniyawa 460 suka rasa rayukansu.